← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 92

Sashe 83

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sai fa mun faÉ—a mata Mami, mu dai kar ta yi sanadiyar mutuwar Ammah, in hakan ya faru wallahi ba za mu yafe mata ba."
Hamma Kabiru ya faÉ—a yana balla ma Ummu Harara kukan banza take yi, shi da za a bar shi da ya lallasa ta, in aka tsaya ana jin tausayinta gaba ma za ta sake aikata irin haka. Dukkansu suna wajen aikinsu ta É—aga musu hankali ta sanya sun baro komai sun taho saboda ita.

"Hamma."

Ummu ta faÉ—a cikin matsanancin kuka.

"Ina Ammah?
Ta faÉ—a tana ware idanuwanta akan dukkansu.

"Tana gida tare da Ummi."

Iklima ta faÉ—a cikin sanyin jiki.
Halin da ta ga Ummu ya sake tsoratar da ita ga lamarin maza.

"Kar ki damu ba abin da ya same ta, suma ne ta yi tana farfaÉ—owa suka koma gida."

"Baffa fa?

Ta sake tambaya cikin muryan kuka.

"Yana gida amma Baba ya kira shi a waya ya sanar da shi farkawanki na san yana tafe."
Mami ta fada tana mai sake share ma Ummu hawaye.
"Ki daina wannan kukan, likita ya ce kar mu saka ki kuka, su na son ki samu hutu saboda jinin ki ya É—an yi sama.".
Kanta ta É—an gyaÉ—a, a tunanin ba su san abin da ya saka ta yanka kanta ba, ta É—auka kawai suna tunanin saboda sakin da Habib ya yi mata ne.

GabaÉ—aya suka yi ta masa sannu tana amsawa. Ba su wani daÉ—e ba mazan suka fita tunda ta farfaÉ—o zaman asibiti kuma ya kare, BaÉ—do kawai aka bari da Mami, su Adda Suwaiba ma sun bi mazajensu zuwa gida tunda tun safe suna asibitin.
Ummu ta tambayi BaÉ—É—o karfe nawa ta ce mata biyar da rabi na yamma.
Sai ta É—an runtse idanuwanta sannan ta sake buÉ—ewa tana kallon BaÉ—É—o, an samu sa'a Umma Balki ta bi su Hamma Abdullahi zuwa gida.

Mami kuma mijinta ya kirata a waya sai ta fita daga É—akin bayan fitan su ne Ummu ta kalli BaÉ—É—o lokaci É—aya tana fadin" Yanzu kwana biyu na yi a asibiti ban san in da kaina yake ba?
Ta faÉ—a cikin sanyin muryan da ta disashe da kuka.

"E, tunda aka kawo ki kina emargency sai yau ne ma da safe suka kawo ki wannan É—akin."
Ummu ta dukar da kanta saboda hawayenta da suka kawo

"Allah na tuba."

Ta faÉ—a tana kecewa da kuka wannan karon BaÉ—do aka bari da lallashi.

"Why Ummu Salma?
Akan Habib ko akan Shamsiya?
Da sauri Ummu ta kalleta cikin mamaki.
"Da man kin sani?
Ta tambayeta cikin raunin murya.

"Na sani, ai dalilin kiran da na yi ta miki a daran shekaranjiya kenan ba ki É—aga kirana ba. Nima a status É—in wata course mate dina na gani, ban taba tunanin Shamsiya za ta iya cin amanarki ba. Amma ban yi mamakinta ba, daga baya ta sauya dake sai da haka ta faru na fahimci dalilinta na kare ma Habibu ashe maciya amana ne."
Ta gama faÉ—a cikin bakinciki da takaici.
Kuka kawai Ummu ke yi kamar ranta zai fita.

"Na tsani Habib, na tsani Shamsiya. Ba zan taɓa yafe musu ba.'

Ummu ta faÉ—a majina na zilalo mata.

"Ki tsane su, amma ki fara cire su daga tunanin ki da rayuwarki gabaÉ—aya. Ba su da amfani kuma in dai amanace da suka ci taki su je ga su ga duniyanan nan da ikon Allah sai Allah ya saka miki."
BaÉ—do ta sake faÉ—a itama tana hawaye

"Shamsiya fa? Ashe duk abin da Habib yake yi mini da sanin ta.".
Nan Ummu ta fara ba ta labarin yadda suka yi da Shamsiya a gidan su.
"Ni dai na san na dawo gida cikin baƙinciki, ina so na ji zuciyata ta daina kuka, baɗdo ban san me ya sa na yi tunanin kashe kaina ba ni dai kawai ina so na samu salama ne a cikin zuciya ta."
Ta faÉ—a tana mai gunjin kuka.
BaÉ—É—o ta rumgumeta ta gefe tana É—an bubbuga bayanta alamun lallashi.

"Ni ce na fara iskoki kwance jini na tsiyaya a hannun ki. Daman da na yi ta kiran ki baki É—aga a daran na ce ma Ummi zan zo wajen ki, ina zuwa na samu Ammah da Baffa tare da Hamma LamiÉ—o a dakin Baffa bayan mun gaisa sai na shigo É—akin ki na iske ki kwance ba numfashi a tare dake nan fa na fasa ihu su Baffa suka rugo zuwa É—akin ki."
Ummu na cigaba da tsiyayan hawaye tana sauraran BaÉ—É—o

Baffa da Ammah sun shiga tashin hankalin da suka kasa iya baki wani taimako. Ba domin Hamma LamiÉ—o na nan ba da watakila jininki ya tsiyaye mu ba mu samu mafita ba."
Cak kukan Ummu ta tsaya ta da kukanta ta yi kasaƙe tana kallon Baɗɗo cikin mamakin jin sunan wanda ta ambata.
Tabbas a ranar ya zo, amma ita tama manta da shi kwatakwata.

"Shi ya yanki zanin ki ya É—aure hannun ki zubar jinin ya tsaya. Sannan shi ya ya É—auke ki cak zuwa mota da ni da shi da Ammah da Baffa muka kawo ki wannan asibitin cikin tashin hankali."
Ummu ta sake ƙura mata ido cikin mamakin wai Hamma Lamiɗo ne ya yi mata haka? Da man yana da tausayi.? Ita kallon mara tausayi take yi masa wanda bai damu da kowa ba.

"Dakyar suka karɓe ki, sun ce case ne na hatsari suna bukatar yan sanda Hamma Lamido ne ya yi cuku cukun da suka karbe ki. An yi nasaran ceto numfashin ki amma suka ce sai an sanya miki oxygen kuma kina bukatar jini, ga shi Hamma Kabiru ba ya kusa ana maganar a je a duba a lab a ko za a samu wanda zai dace dake, kawai Hamma Lamiɗo ya ce jininsa O ne, nan take kuma aka je aka gwada shi ba wata matsala aka ɗibi leda biyu aka sanya miki a daran nan."
Ummu sai da ta yi yar shaƙuwa.

"Daman ba Hamma Kabiru ba ne ya ba ni jininsa ba?

"A daran ta ina Hamma Kabiru zai taho? Yau ne ma ya samu zuwa ba daÉ—ewa. Hamma LamiÉ—o ne ya ba ki jininsa Sisna, ni kaina lamarin ya ba ni mamaki ban taba tunanin yana da tausayi haka ba"

Ummu Salma ta haɗiye wani miyau a maƙwagaronta.
Jikinta take kallo tana jinjina kai wai akwai jinin Hamma LamiÉ—o a jikinta yanzu haka.

"Kin ga farar shaddar jikinsa duk ta ɓaci da jinin ki, Baffa ya yi ta cewa ya je gida ya sauya bai tafi ba saboda faɗuwar da Ammah ta yi shi ya zauna da ita har asuba aka sallameta sai ya ɗauketa zuwa gida ni da Baffa kuma muka kwana dake sai da safe ne Ummi ta zo sannan ya koma gida."
Ummu ta share hawayenta da gefen hannunta na hagu, hannunta na dama take kallo dake dauke da bandage ya kumbura

"ÆŠinki aka yi miki. Likitan ya ce Allah yasa yankar bai yi zurfi ba."
Ummu dai sai sharan kwalla ba magana.

"Kin faÉ—a musu abin da ya faru ne?
Ta tambaya tana kallon BaÉ—É—o

"Na faÉ—a musu, kawarki Shamsiya ce ta za ta auri Habib shi ne kika yi yinkurin kashe kanki."
Ummu ta runtse idanuwanta tana jin kalmar kashe kanta ita ta aikata amma nadamar take yi, tsanar kalmar take yi.

"Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrahaman sun yi ta faÉ—a, Baffa na fama da kansa bai ma yi musu magana ba zuwan Mami ne ma da ta yi musu mgana suka É—an yi sauki da faÉ—an na su, amma kaf din su sun shiga damuwa ana kiransu a safiyar jiya suka cika asibitin nan tare da matan su, Mami ma ajiyan ta iso da rana. Hamma Jibo ne kaÉ—ai bai zo ba saboda aiki Hamma Sadam na makaranta bana ma tunanin ya san abin da ya faru."

Ummu ta yi shuru kafin ta ce" BaÉ—do na yi nadamar sanin Habib na yi nadamar sanin Shamsiya a rayuwata."
"Ki bar su da Allah, yau ne daurin auran an ma É—aura tun dazu ta je ga ta ga Habib É—in shima ga shi ga Shamsiyan in dai don sun tozarta ki ne suka samu damar auran juna. To da ikon Allah suma sai Allah ya tozarta su."

"Allah ya isa, ba zan taɓa yafe musu ba, sun lalata mini rayuwata. Me na yi musu?
Ummu ta sake fada tana kuka.
"Ba ki yi musu komai ba, ki dauka a haka a matsayin kaddaran ki. Ki bar masa faÉ—an shi zai saka miki "
Ummu ta cije lebenta na kasa tana jin wani irin turiri a zuciyanta. Ta tsani Habib ta tsani maza ma gabaÉ—aya dalilin shi yau take kwance akan gadon asibiti ta gode ma Allah da ya sake ba ta wata damar da yanzu ta mutu shikenan ta mutu a kafira ta yi asaran rayuwanta saboda Habib da Shamsiya da man burinsu kenan. In dai haka ne ba za ta sake ba su wannan damar ba, za ta cire su daga duniyarta har abada amma ba lalle ne abin da suka yi mata ya bace daga zuciyarta ba, har abada sun riga sun dasa masa ciwo mai wuyar warkewa a zuciyanta.

"Ki yi hakuri, ki yi hakuri amma don Allsh kar ki sake tunanin kashe kanki Ummu Salma."
BaÉ—do ta faÉ—a cikin karaya.
"Ba zan kara ba, in sha Allahu ba zan kara ba."
Ta faɗa cikin kuka da hawaye shaɓe-shaɓe.
Suka rumgume juna Ummu na kuka da shessheƙa Baɗɗo na hawayen tausayin Ummu.
A haka Mami ta dawo ta same su, sai ta fara faÉ—an ya haka kuma? Ita BaÉ—É—o da za ta yi lallashi sai ta bige da kuka nan take tace su bari ba ta so.

Dole suka share hawayen su, sai dai ajiyar zuciya.
Sai mangariba likita ya dawo suka sake É—aura ma Ummu karin ruwa sannan suka yi mata allura.
Mami ta koma gida da Hamma Abdullahi ya kawo Baffa ya duba Ummu ya sameta idanuwanta biyu tana kuka ta rirriƙe hannayen Baffa tana cewa ya yi hakuri.
"Bakomai Auta, na yi ma Allah godiya da kika kuɓuta ina sake masa godiya."
Da yakee an yi mata allura ashe akwai na barci ba daÉ—ewa sai barci ya kwashe ta.
Chapter 83 · 0% Book details