← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 92

Sashe 45

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta haifi Mustapha ko shekara bai yi ba suka sake samun wani rashin na rasuwar Audu Baba shima lafiya lau ya kwanta da asuba rai ya yi halin shi tsakanin shi da Gwaggo kwana arba'in, da man tun rasuwar Baba ba ta da lafiya ashe itama ajali ne Baffa da Ammah sun fi kowa shiga cikin tashin hankali gaba da baya maraici ya sarƙe rayuwarsu yanzu ba su da mai kula da su, Ammah ta rasa mai duba ta, mai kula da ya'yanta da duka rayuwarta sun yi kuka kamar ba za su daina ba. Ga Fatima da take ƙarama a lokacin abin tausayi da Baffa ya so ya karɓi riƙon tilon ƙanwarsa amma sai dangin Gwaggo da suka taho daga Daura suka ce za su tafi da ita saboda ita mace ce sannan Baffa kuma ba kai girman da zai iya rike wani ba shima yana da iyalansa tunda Baba baya raye yana ji yana gani suka tafi da Fatima Daura ko gadon su na Baba da Gwaggo da aka raba su suka tafi da shi, shi kuma ganin ba Gwaggo ba Baba sai ya fara tunanin barin Mubi duk da akwai Umma(Asma'u) da sauran ƴan'uwansa maza amma duk da haka sai garin ya yi masa ƙunci Ammah ma duk ba ta cikin walwalarta tun ballantana da Fatima ta bar Mubi zuwa Daura rashin ta dameta sosai tana kuka tana cewa za ta iya riƙe Fatima me ya sa Baffa ya bari aka tafi da ita? Lallashinta ya yi ta yi saboda shima bashi da tacewa a lokacin a matsayin sa na ƙarami sannan su Hamma Hamza a lokacin ba su hana ba to shi ma bai isa ya ce komai ba.

Da kuɗin da aka raba musu gado Baffa ya fara bin matasa garin da sukan shiga cikin birnin Yola kasuwanci yana ɗan taba harkoki a can farko ya ɗan faɗa harkan siyar da siyarwa ne daga baya kuma ya fara haɗawa har da cinikiyar dabobbi irin su shanaye da raguna, duk abubuwan dai ba su tafi daidai ba sai ya faɗa harkan siyan tsoffin ƙarafan motoci ya fara daga ƙananun karafa ne sanadiyar wani abokin kasuwancin sa da suka haɗu a garin Yola shi ya ba shi tabbacin harkan ana samu sosai kawai sai ya faɗa kuma bai rufe shekara ba ya ga haske a cikin lamarin, yana daɗewa baya gida tunda ba iya Yola yake harkokinsa ba ko'ina har Lagos da ibadan suna haurawa neman ƙarafa sai dai in ya ga mai zuwa gida ya tura ma Ammah da su Umma saƙo wani lokacin sai ya yi wattani biyar ba ya gida amma duk da haka bai manta da tilon ƙanwarsa ba yana tura kuɗi can gida Mubi ya ce in an samu mai zuwa Daura akai ma Fatima sannan duk salla yana yi mata sutura tunda suna kawo ta salla ƙarama in kuma sallar layya ce Baffa da Amma ke zuwa can Dauran saboda dai kar Fatima ta yi maraicin rashin iyaye da ƴan'uwa.

Kuma Alhamdulillah Fatima ta samu iyayen riƙo na gari. Wanda ke riƙon ta ƴaya maza suke da Gwaggo Madibbo shi Allah bai ba shi haihuwa ba ne har sun fara tsufa shi da mai ɗakin sa, sannan yana aiki a gidan Sarkin Daura shi ke kula da bargan dawakai na cikin masarautan gabaɗaya. Fatima ba ta yi karatun boko ba amma tana yin karatun addini. Shekaran su Gwaggo uku da rasuwa Baffa da Ammah da yaran su biyu suka yi ƙaura daga mubi zuwa garin Yola acan Baffa ya kama musu haya suka fara zama saboda harkokinsa suna daɗewa a can shi ya sa ya ga gwara ya ɗauko ta, ta dawo kusa da shi amma in salla ne ko aka yi wani abu ba su manta da mafarin su ba suna zuwa Mubi tunda can ne gabaɗayan yan'uwan suke Ammah ma duka yan'uwanta suna Mubi ga Aminiyarta dake aure a Girai sai dai har lokacin ba ta haihu ba amma in dai Amma ta je Mubi ta kan karisa can Girai su zumunci da amincewar Baffa kamar yadda ya saba bata dukkan wata dama ba ya tauye mata haƙƙin ta na aure ta kowani bangare godiya take yi ma Allah da ba ta auri Baffa ba da ta zama mai asara a cikin mata.

Baffa da kansa ya je Daura ya taho da Fatima ya kawo ta Yola ta ga in da suke da zama ta yi kwanaki da su kafin ta koma kuma lokaci bayan lokaci tana zuwa duba su musamman Baffa zai tura mata kuɗin mota domin ta zo, yana ƙaunar ƙanwar shi, itama tana son yayan ta guda ɗaya da suka haɗa uwa saboda yana kula da ita sosai. Tana da shekaru sha bakwai kwatsam mariƙinta Madibbo ya aiko masa da cewa ya zo Daura yana son ganin shi akan Fatima ne ba ɓata lokaci ya shirya ya tafi yana zuwa sai ya ji labarin da ya girgiza shi wai Fatima ta samu miji, amma mijin ba kowa ba ne sai yaron Sarkin Daura. Sarkin Daura a lokacin Alhaji Muhammad Shitu Daura ne sarki na 49 a lokacin.

Kuma ɗa ne ga sarki Alhaji Bashar Daura sarki na 39 a wancan zamanin, Sarki Alhaji Muhammad Shitu  yana da tarin ƴa'ƴa amma duka duka yaran shi maza guda biyu ne Babban ba shi da lafiya ana ta raɗen raɗen an haife shi da ɗan matsalan ƙwaƙwalwa, sai kuma na biyun Muhammad Nasiru(Hakimin Daura kuma Yarima mai jiran gado) domin tun a lokacin ana tunanin shi ne zai gaji sarauta daga mahaifinsa saboda zamowarsa tushen masauratan Daura. Mahaifiyarsa Hajiya Ruƙayya(Fulanin Daura) duk da fa a wancan lokacin ba ita ce uwargidan Maimartaba Alhaji Muhammad Shitu ba, Hajiya Rakiya Muhammad Shitu ce(Magiyar Yamman Daura) amma ita ce mafi soyuwa a gare shi tunda ita ce mahaifiyar Hakimin Daura sannan Yarima mai jiran gado.

Labarin ga shi dai mai daɗi ne amma kuma ba shi da daɗi a mahanga da yanayin tsarin rayuwarsu na talakawa, ina Fatima ina Yarima mai jiran gado! Ai haɗin ma bai yi ba akwai tazara mai yawa su da ba kowa ba, sai talakawan gari ina su ina haɗa kafaɗa da masu garin gabaɗaya nan da nan Baffa ya nuna bai amince ba shi bai ma yarda son Fatima yake yi ba domin bai ga ta in da suka haɗu ba, ballanta har rayuwarsu ta haɗu waje ɗaya. Amma mariƙinta ya dage da cewa Yariman Daura mutumi ne na gari mai taimakon talakawa, mai alheri ga matasa mai son talakawaa kuma mutanen garin Daura suna son shi kamar yadda ake son mahaifin shi.

Sai dai duk da haka Baffa bai amince ba duk sun faɗa masa a gidan Sarkin Yariman Daura ya ga Fatima lokacin da ta je kai ma Madobbi abinci kuma ya ji nan duniya ita yake so ya kuma je ya yi magana da mahaifinsa. Shi kuma Sarkin Daura a lokacin Marigayi Alhaji Muhammad shitu ya sa aka kira Maddibo mariƙin Fatima ya yi magana da shi a cewarsa da talaka da mai kuɗi da mai sarauta duk Allah ne ya yi su, sannan tunda dai Muhammad Nasiru ya ce yana son ta shi kuma ya yi alƙawarin samar masa da duk abin da yake so amma duk da haka Baffa bai amince ba haka ya dawo Yola cikin damuwa da Amma ta tambaye shi sai ya sanar da ita abin da ke faruwa itama ta ce gaskiya abin ma bai haɗu ba ta ina Fatima za ta kai kanta a matsayin auran ɗan sarkin? Sarkin gobe itama ta goya masa baya kan hukuncinsa saboda haka ma ya ce zai ɗauko Fatima ta dawo hannun shi ya saka ta a makaranta ta yi karatu nan gaba Allah zai kawo mata mijinta ta yi aurenta amma ba ya jin zai yi kasadan wasa da rayuwarta wajen kai ta in da ya fi karfin zuwan ire-iren su.

Ba ƙwace Fatima ya yi daga hannun mariƙanta Modibbo ba amma dai ya nuna zai karɓe ta riƙon ta ya dawo hannun shi tunda Allah ya rufa masa asiri shi kuma Madibbo sai ran shi ya ɓaci da ganin kamar Baffa ya raina masa ne sai ya tara yan'uwansu dangin Gwaggo ya faɗa musu halin da ake ciki nan aka ba ma Baffa rashin gaskiya suka kuma hana shi ɗaukan Fatima daga ƙarshe suka yanke shawaran tura wakilan Sarki can Mubi wajen su Baffa Hamza domin su yi mgana tunda suma suna da haƙƙi, Baffa ba da yawun shi aka aminta da auran Fatima da Yarinman Daura ba lamarin bai yi mishi ba tun ballanta da yaji auren a matsayin auren sirri ba wanda zai ji labarin auran daga Daura a cewar Maimartaba saboda mahaifiyar Muhammad Nasiru in ta ji labari ba za ta bari hakan ya faru ba, hankalin Baffa dai bai kwanta ba sai da ya je har garin Daura ya yi kyakyawan bincike akan Masarautar Daura ya samu kyakyawan shaida akan Maimartaba da Hakimin Daura amma sam bai samu shaida mai kyau kan Fulanin Daura ba, mace ce mai ji da kanta da sarauta, ita ɗin babanta ya yi sarki kakanta ma Sarki ne sannan mijinta ma Sarki ne kuma ɗan ta ma zai yi sarauta, shi ya sa ba ta ƙaumar talaka ko mara arziƙi tana harkokinta da masu asali ne da sarauta a labarin da ya ji ma tana nema ma ɗan ta auren ɗiyar wazirin Daura ne a lokacin.
Chapter 45 · 0% Book details