Sashe 14
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yake asbitin na kuɗi ne ba wani ɓata lokaci, suna waiting area suna jira Habib ya kasa zaune ya kasa tsaye, tana shirin ta ce masa ko zai bar ta ne ya tafi wajen aiki in ta karɓi result ɗin sai ta nemi Napep ɗin da zai kaita gida kafin ma ta yi mgana ta ji yana waya yana cewa ba zai shigo office da wuri ba shi ya sa sai ta yi shuru da bakinta.
 Ita dai tana zaune saboda ba za ta iya tsayuwa ba, Habib kuma ko ya zauna sai ya tashi ya kasa zama a waje ɗaya tuni farar fuskan shi ta bayyana halin damuwar da yake ciki. Ummu na zaune tana bin shi da kallo tausayin shi take ji ta cikin hijabin ta, tana ta shafa cikinta a cikin zuciyarta take faɗin.
"Allah ya tabbatar da cikin nan."
Da ace Ummu-Salma ta san gaibu, da ace ta san fargan jajin da ke jiranta da ba ta yi ma kanta wannan addu'ar ba, da ta yi addu'an in ma cikin ne Allah ya sa ya bi rariya.
Zaman jiran mintina arba'in suka karɓi sakamakon gwajin. Bakin Ummu ya ƙi rufuwa tun bayan da likita ya ce tana da ciki na wata ɗaya da kwanaki, an rubuta mata magungunar karin jini da cin abinci, sai vitamin e, amma murnanta sai ya koma ciki na ganin fuskar Habib ta yi baƙiƙirin kamar an faɗa masa saƙon mutuwa, ita da ta yi tunanin yana jin tabbacin tana da ciki sai ya ɗaga ta sama ya yi juyi da ita, amma sai ta ga saɓanin tunanin ta, amma sai ta ƙarfafi kanta da cewa haka ya yi a cikin ta na farko lokacin da ya ji labari bai nuna murnansa ba amma lokacin da ya tabbatar da ta yi ɓarin shi ya fi kowa damuwa, ya yi jinyar ta har sai da ta warke da jikinsa da aljihunsa tunda ta kwanta asibiti wajen kwana uku aka ƙara mata jini, tun a lokacin likitan ya ce ta rasa jini da yawa. A lokacin ma jinin Hamma Kabiru aka saka mata tunda sun gwada na su Hamma Abdullahi bai yi mata ba, ita jininta O Negative. Na sauran kuma duk AB Negative ne.
Suna cikin mota a hanyar komawar su gida, kamar Habib zai ta shi sama. Ummu ta kasa yi masa mganar siyan mgani ganin fuskar shi tumu tumu ba annuri daga gani ba ya cikin natsuwarsa. A ƙofar get ɗin su ya sauke ta bai shiga ba tana kuma sauka bai ce mata komai ba ya fizgi mota a guje ya wuce ba domin ta yi saurin matsawa ba da ya take mata ƙafa.
Har ya ɓace ma ganinta bakin ta bai rufu ba saboda mamaki.
"Me ya samu Noori kuma?
Ta faɗa a fili saboda tunda suka yi aure bata taɓaa ganin shi cikin firgici da zafi haka ba.
Jiki a sanyaye ta shiga compound ɗin su har ta buɗe ɗakin ta shiga jikinta bai dawo daidai ba, mamakin yanayin yadda Habib ya yi mata yafi ba ta mamaki ta ɗauka cikin tattali da murna zai dawo da ita gida amma sai ta ga akasin abin da ta yi tunani, sai dai ta yi masa uziri da cewa watakila wani abu ne ke damun shi.
Takardan cikin ta É—auko duk da ba gane yaren na likitoci take yi ba amma kallo kawai na saka ta farinciki, tana shafa cikinta tana jin murna da farinciki nan da watanni takwas za ta zama uwa.
****
Habib tun da ya fizgi motar nan a guje bai ci burki a ko'ina ba sai da ya isa haraban bankin su, a parking space ya faka motar shi amma bai fito ba kansa ya dafe da hannu biyu yana jujjuyawa.
Kafin lokaci É—aya ya zaro wayarsa cikin aljihun wandon sa ya lalubo wata lamba da ya yi ma saving da M.S.
wajen saƙo ya shiga ya fara rubuta mai lambar saƙo.
"An sake samun matsala Ummu-Salma ma da ciki a karo na biyu."
Ya tura da mintina huɗu yana zaman jira riƙe da waya a hannun shi sannan mai lambar ya dawo masa da amsa.
"Again kuma? Habib wasa da hankalina kake yi? Da man ai ka san za ta iya samun ciki tun da mahaifarta lafiya lau. Sai da na ce ka yi mata planning ko a ɓoye ne amma ka ƙi amincewa. To na rantse da Allah ba zan amince ba, in farko ya zama kuskure wannan ganganci ne."
Jikinsa na rawa ya sake rubutawa ya tura.
"Ki yi haƙuri ki bar wannan mganar yanzu dai mene ne mafita?
Yana turawa da mintina biyu aka dawo masa da amsa.
"Ka fi ni sanin mafita. Ni dai ina so ka sani bayan ni babu wata macen da ta isa ta haihu da kai Habib. Ni ce uwar ƴa'yan ka nan duniya. Ka tuna da hakan"
Sai da ya share zufa duk da A.C É—in dake cikin motar, daga ganin shi yana cikin tashin hankali.
Yana shirin sake rubuta wani sakon ne wani ya sake shigowa.
"Ka tuna da alƙawarin mu shekara ɗaya ka ce na baka za ka cire Ummu Salma daga rayuwarka na har abada. Yanzu kuna da wattani takwas da aure. Wattani huɗu suka rage maka Habib."
Sai ya dakata yana mai kallon saƙon zuciyarsa na bugawa da gudu fat! fat.
Ajiyar zuciya ya sauke a jere kafin ya ba da amsa.
"Ina sane da komai. Zan kuma É—au matakin da ya dace."
Yana gama turawa, ya rufe wayar ya mai da ta cikin aljihun wandon shi, sai da ya É—an natsa sannan ya É—auki brief case É—in sa ya fito daga motar bayan ya kulleta cikin Sassarfa ya nufi katafaren ginin ma'aikatan su na First bank.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
https://chat.whatsapp.com/BxcTrVcz7GoIDzbqZTpIxF?mode=gi_t
*04*
*9:43pm*
Har zuwa lokacin Habib bai dawo ba, Ummu ta kira shi sau uku bai É—aga wayarta ba daga karshe ma sai ta ji ta daina samun shi kwata-kwata.
Zaune take a falo saman ɗaya daga cikin kujerun da suka yi ma falon ƙwanya, tun ɗazu ta gama girki ta yi wanka tana jiran dawowar Habib amma har zuwa wannan lokacin bai shigo ba, kuma bai saba yin dare a waje ba sai da dalili mai karfi.
Tunaninta da hasashenta bai taɓa kawo mata matsalan daga ita ba ne, tagumi ta yi ta ƙura ma talabijin ido a tashar tauraruwa an saka wakar Salin smart na Labarina. Amma hankalinta da nazarin ta ba ya wajen, idanuwanta na juyawa akan allon talabijin ɗin amma tunanin ta da dukkan zuciyarta yana kan Habib.
"Me aka yi masa?
Ta tambayi kanta sau shurun masaki a cikin zuciyarta ko daga ɗazu bayan dawowarsu daga asibiti ta yi ma Habib wani laifi ne? Ya iya hangen ta da tunanin ba ta hango wani laifin da ta yi masa ba, fuskar sa da ayyukansa sun sauya ne daga lokacin da ya samu tabbacin tana da shigar ciki, daga lokacin Habib ya sauya sauyawar da ta kasa gano dalilin shi, kuma zuciyarta ta aminta da shi, shi ya sa ba ta yarda ta kintsa mata wani mugun tunani a game da shi. Ƙarfafa kanta take yi da cewa watakila wani ne ya ɓata masa rai, amma Habib sai ya fi kowa murna da samun cikinta anan duniya.
Tun da ya sauketa a bakin get ta shigo gida take nazarin abin da ya faru amma ta kasa gano bakin zaren. Ko da daddaren nan sai da ta yi Amai bayan ta yini kwanciya saboda kasalan da ta rufe ta amma ba ta biye ma yanayin jikinta ba yamma na yi ta miƙe ta yi ma Habib girki, soyayyan taliya da Nama mai kayan lambu da ya ke ana gobe su Amma za su dawo ya ɗauke ta sun je kasuwa sun yo cefane mai yawa tana da komai na buƙata kayan miya ta ñika shi ta tafasa shi yana cikin Frezer ɗiɓa kawai take yi in ta tashi amfani da shi.
Wayarta ta sake jawowa yanzu kam har goma ta wuce amma babu alamun Habib, tunanin ta ya sake karkata kan ko dai yana fushi da ita ne ya ɗauka ta san tana da ciki ba ta faɗa masa ba? Tuna haka ya sa ta yi mirmishi ita kaɗai ta san ma saboda haka ne ya ke fushi yaƙi dawowa gida da wuri, in ya dawo za ta bashi haƙuri in dai Habib ne ba ya iya dogon fushi a kanta saboda yadda yake tsananin sonta da gudun duk wani abu da zai ɓata mata rai.
Gajiya ta yi ta zaman shuru sai ta yi tunanin bari ta kira Bestie sai dai wayar na ta ringing ba ta ɗaga ba, sai ta ma yar da akalan kiran ga Baɗɗo ita dai ta ɗauka sun yi mgana ga shi tana so ta sanar da ita tana da ciki amma kamar an matse bakinta ta kasa faɗa mata, ba su daɗe suna waya ba saboda ta ce mata tana karatu sun fara jarabawa a satin nan da ya shiga. Ta tambayi Habib sai Ummu ta yi mata ƙaryan ya biya ta gidan su bai riga ya ƙariso ba.
"Allah ya ba ki sa'a da nasara SisNa."
Ummu ta faÉ—a cikin mirmishi lokaci É—aya tana shafa cikinta. Domin in ta tuna nan da wattani takwas ita É—in uwa ce kuma mai uba irin Habib sai ta ji kamar ba macen da ta kai ta farinciki anan duniya.
Daga can bangaren Baɗɗo ta amsa ma ta da Amin, sannan suka yi sallama bayan Ummu ta ce a gaishe mata da Ummin ikki.