← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 92

Sashe 64

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gadon ta ɗan kakkabe tana ninke farin bargon. Gabaɗaya ɗakin kalan baki da fari ne Lamiɗo na son abu fari kuma yana son baki ko kayan shi rabi farare ne rabin su kuma baƙaƙe ne, bayan ta gyara gadon ta ninke bargon ta ɗan saka shi a gefen gadon ya ɗan ba da styel, itama sai ta koma ta zauna tana ɗan mirmishi.
Tana son mjinta tana son Lamiɗo, lokacin da mahaifinta ya kirata akan Lamiɗo ta ji wani iri, da jin labarin Baban shi ne ya yi gadon Sarauta, mahaifiyar shi ba yar kowa ba ce. Bata taɓa tunanin haka za ta ga Lamiɗo ba, sai da ya zo haɗuwar su ta farko anan ta fahimci ko a cikin maza shi na dabam ne, ko ita da take jinin sarauta gaba da baya tunda kakanta na bangaren uwa ya yi sarautan Kano, to ba za ta nuna ma Lamido iko da sarauta ba, tafiyar shi, maganar shi, yanayin tsarin rayuwarsa kaf kamar wanda aka haifa a gidan sarauta ya kuma girma acan, sai ga shi ta ji labarin shi bai ma zauna a Daura ba sai da ya girma ya zo. Kenan duk wani abu na hallayar shi ko yanayinsa halitar shi ce haka Allah ya yi shi.

Ba auren soyayya suka yi ba kakar sa Fulanin Daura ce ta zo ta nema masa auran ta, saboda kyayawan alaqan da ke tsakanin masarautun ba jayayya aka amince, kuma daman a zamanin da muke ciki ƴa'ƴan sarakuna sai ƴaƴan sarakuna ƴan'uwansu ko kuma ƴaƴan masu riƙe da madakan ikon a kasar gabaɗaya. Shi ya sa sai haɗin ya yi daidai duk da ana ta cewa mahaifiyar Lamiɗo ba ƴar sarauta ba ce wataƙika ba zai yi gadon Sarauta ba amma kwarjinsa da tasirinsa bai gushe ba. Balkisu ma tun a ganin farko da ta yi masa ta ce ya yi mata tana son shi. Duk a tunanin ta wannan shuru shurun na shi, da wannan ji da kan duk zai sauke su bayan aure. Itama jinin sarauta ne tana ji da takama da girman kai amna haɗuwarta da Lamiɗo sai ta sara ta kuma jinjina masa ta san ita ba ta yi komai ba. Bayan auren su babu abin da ya sauya Balkisu ta yi tunanin za su yi soyayya ta kwatance a yanayin yadda take, yar gayu wayayyiya mai ilimi. Amma sai ta ga sabanin haka, shi fa ba ka iya gane yanayin da yake ciki yana son abu ko ba ya so duk ba ka isa ka gane ba. Ta sha wahala sosai kafin ta fahimci Mijin data aura, komai in za ta yi masa ko ya yi masa ko bai yi masa ba, ba zai taɓa magana ba in ya yi masa ba zai nuna alamu ba, in ma bai yi masa ba, ba zai nuna ba.

SSai da ta yi ta karatun nazarin hallayan Lamiɗo sannan ta fahimce shi, shekaran su shidda da aure ba ta taɓa jin ya ce yana son ta ba, sunan ta ma bai wuce sau goma ya taɓa kira ba, in ma magana ta kama sa dole sai dai ya yi maganarsa kawai kai tsaye, da yawan lukata baya gida in ya kirata a waya suna gaisawa ya tambayi yara bai kara cewa komai sai dai in ita ce ta dauko masa hira. In ya dawo za su zauna a gida ɗaya amma bayan gaisuwan safe in dai ba itace ta yi masa magana ba za su iya yini su kwana ba su sake yi ma juna magana ba. Zai iya yini a bangarensa bai fito ba, wani lokacin sai dare in ya fito cin abinci tare da yara. Tunda duk da yanayin shi yana son yara yana wasa da su Sultan, suma ɗin akwai lokacin haka in yana son kaɗaici ma ba zai fito daga bangarensa ba yana son shuru fiye da komai a rayuwansa.

Bangaren abinci kuma sai da Ammah ta taimaka mata ta ɗan ba ta satar amsa, duk da ba ita ke yin abincin ba sai dai ta ba da umarnin a dafa masa. Lamiɗo na cin tuwo amma ba ya shan duk wata miya mai yauƙi, ba ya son yaji ba ya son mai ya yi yawa. Ba ya cin naman jan akuya sai kaza ko kifi, kuma ba ya cin shinkafa tsura ko wani abu sai da miya, miyar ko wata iri amma ban da miyar yauƙi, yana son ganye sosai. Da Balkisu ba ta sani ba ta yi ba shi miyar yauƙi sannan ita tana son cin yaji. Gashi dai ba ya so amma ba zai taɓa magana ba, sai dai ta ga baya ci da yawa sai dai ma wani lokacin ya yi ta cin abun gaya ba miya, in ta yi masa mgana sai dai kawai ya yi mata shuru, Ammah ce ta taimaketa anan ne ta san ba ya shan miyan yauki. Shi fa in dai shi zai fada maka abin da yake so da bakinsa to ba za ka taɓa sani ba. Tuni Balkisu ta sauke jin kai da sarauta ta fara karantan mijinta domin ta san cewa ba irin mijin kowa ba ne, Lamiɗo mijin Balkisu na dabam ne a cikin maza.

Da haka ta samu ta karance shi tsab har suke zaune lafiya cikin mutumtawa. Ko bai furta da bakin shi yana son ta ba, tana ganin haka a aikace. Ba ta damu ba ta amince da na shi salon nuna son ne a haka bai taɓa danne mata hakkinta na aure ba, tana daga cikin sahun gaba a matan da suka yi sa'an aure, ta samu miji na nunawa sa'a ga shi gwarZo kuma jarumin namiji mai iyawa da duka bukatunta, farkon auren su sai ta zauna jiran sai ya zo gareta ta yi ta cutuwa shi kuma ko yana son abu ba ya nema. Ba ma ka gane yana so ko ba ya so. Shi ya sa da ta fahimce shi ta riƙa ba da kai bori ya hau abin mamaki kuma sai ya fi ta ma rawan jiki da son nuna jin daɗinsa, tun daga lokacin ba ruwanta in tana bukatarsa za ta je gare sa shi kuma a kowani hali yake ciki bai taɓa tankwafar da bukatarta ba sai ya tabbatar da ta samu gamsuwa ɗari bisa ɗari.

Ta yi nisa cikin tunaninta ba ta ji karan buɗe kofar toilet ba sai dai kawai ta gan shi ya fito sanye da rigan wanka baka, gaban rigan ta ɗan buɗe, ganin ta a zaune kuma sun haɗa ido.  Da sauri ya juya baya lokaci ɗaya yana jan rigar wankan ya rufe ƙirjinsa.

"Me za ka ci na sa Debora ta dafa maka."
Ta faÉ—a cikin harshen turanci lokaci É—aya tana mikewa tsaye.

"Anything is ok. Buh zan fara da Coffea mai zafi."
Shima ya mayar mata da martanin maganarta cikin harshen turancu muryansa mai kama da ta jaruman maza.

"Okay"

Ta faÉ—a, bai ma jira ta fice ba shi ya fara shigewa cikin clothset É—in sa, domin ya sauya kaya. Ita kuma sai ta fice tana zuwa main falo su Sultan na shigowa falon James na bin bayansu É—auke da jakunkunansu da basket É—in su na makaranta
Suna ganinta Beena yarinya yar shekara uku
Yar ajin Baby class dabar dabar da lukutun jikinta na yara Æ´an hutu ta nufe ta da gudu da karamar muryanta tana kiran sunanta

"Momi."

Da sauri ta tarbeta ta É—aga ta sama tana nishi, tunda Beena akwai jiki kamar kazar turawa.
"My Beena."
Ta faÉ—a tana jan kumatun ta, ita kuma ta tsinke da magana tana fada mata ta ci egg a makaranta da plantain, da muryansu ta yara da turanci tana jinta tana dariya, Sultan kam a natse shi ya kariso falon yana faÉ—in.

" Good Afternoon Momi."

"Afternoon My Sultan. How was school?.

Ta faÉ—aa tana É—an shafa kan shi. Shi nursery 1, yake shi ne sak LamiÉ—o Beena ce ke kama da ita.
Ya amsa mata da lafiya lau da turanci yaro ne É—an shekara biyar amma yana da tsawo da É—an kiba shi ya sa sai ka yi zaton shekaransa takwas in ba ka san shekarunsa ba.

Anitha ta fito daga wani korido daga yamma da sauri domin ta na sane da lokacin dawowar yaran tunda alhakin kula da su yana wuyanta ne suna ko ganinta Beena ta ƙwace a hannun uwar ta nufeta ita kuma ta tarbeta tana mata oyoyo.
James cikin ladabi ya gaisar da Balkisu sannan ya  sauke kayan hannunsa ya fice daga falon.
Har Anitha ta ja Beena zuwa cikin É—akin su Sultan yana bin bayan ta Balkisu ta kira shi yana juyowa ta ce

"Ku sauya kaya ku ci abinci Papa is at home."
Jin ta ce Papa ya sa ya fara tsalle yana murnan Papa ya dawo ya bi bayan Anitha har suka ɓace ma ganin ta, tana tsaye tana kallonsu tana mirmishi,. Ba su san ya dawo ba tunda a jiyan ma cikin dare ya iso gidan kuma ya kwanta yau yana ta barcin gajiya ba su haɗu ba.

Kitchen ta shiga ta iske Debora na ta aikin Dinner tana ganin ta ta rankwafa tana gaisheta ba ta amsa ba ta ce ta haɗa ma Baban su Sultan coffea mai zafi nan da nan ta amsa falo ta fita ta zauna ba daɗewa sai ga shi ta haɗo ta kawo mata a cikin wani karamin fulas fari da karamin mug fari da faranti, Balkisu ta karɓa ta wuce da shi ɗakin Lamiɗo ta iske shi ya sauya kaya zuwa wani wando blue da farar riga mara hannu yana gefen gado yana kunna wayarsa da tafi sati a kashe.
Karamin teburin tangaran É—in da ke cikin bedroom É—in ta jawo ta sauke farantin hannunsa.

"Thanks"

Ta ji ya ambata a saman leben shi, halin shi ne duk abin da za ta ba shi ko za ta yi masa zai yi mata godiya wannan daɓi'an shi ne..
Zuba masa ta yi ɗan daidai a mug ɗin sannan ta miƙa masa ya karɓa yana sake yi mata godiya wannan karon da harshen fillanci, duk da ba ta ji amma tana tsinta a bakin shi da bakin yaran tunda yana yi musu magana da fillancin.
Chapter 64 · 0% Book details