Sashe 73
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi ba ya son hayaniya, ba ya son magana ya fi daraja ya ji duniyar ma ta yi tsit gabaÉ—aya.
Amma in dai yana amsa sunan Muhammad Nasiru(Yariman Daura) ba zai iya guje ma abubuwan da suka shafi sarauta ba a baya ya yi haka amma jini da sarauta suna cikin jinin jikinsa ne ko ba a Daura ba shi É—in kasaitattace ne.
Har suka iso garin Daura magana ba ta sake haÉ—a shi da É—an'uwansa ba shima kuma kanin na shi ya san waye shi bai takura masa ba shima a cikin motan lamo ya yi kamar baya ciki.
Motocin da su Bilkisu ke ciki kofar shashen cikin gida ta nufa, su kuma direct motar su fada ta nufa, tuni bushe-bushe da kaÉ—e-kaÉ—e suka cika fada na zuwan Yariman Daura.
Motarsu ko gama fakin ba ta yi ba dogarai suka yi caa,tuni yar natsuwanr da ya fara samu ta yi ta kanta ga hayaniyar mutane ga busa wanda ya ke sake bashi tabbacin ya shigo garin Daura rayuwarsa ta sauya ya tashi daga Muhammad matuƙin jirgin ruwa ya koma Muhammad Nasiru(Lamiɗo) mai sarautan Yarima mai jiran gado duk da dai shi kam ya san ba wani gadon da ya je jira ba zai iya yin wata sarauta ba domin ba zai iya ba.
A guje dogarai suka buɗe musu ƙofofin motar shi da Saleem, da yake a tawagan da suke je ɗauko shi har da masu kakin masarauta.
Tun kafin ya fito daga motar dogarai suka zube a kasa suna faman kawo gaisuwa..
Daga lokacin ya ji kamar ana sauya shi komai na shi ya sauyawa kamar ba shi ba.
Shi ya sa aka ce in dai kai jinin sarauta ne, duk in da ka shiga ba zaka ɓuya ba.
Tuni Lamido ya rikiÉ—e ya fito a Yariman Daura sak.
Kafafunsa farare masu cike da gargasa ya fara sawowa waje masu ɗauke da takalma rufaffu bakake na fatar damisa masu kyau, sannan gangar jikinsa ta fito. Dogon Yarima mai ƙwarjini da Haiba. Haka wani dogari ke faɗi kamar zai saka kansa a kasa saboda girmamawa.
Sanye yake da wani baƙin yadi mai ɗan santsi ɗinkin riga da wando amma tazarce, sai ya ɗauki jaket baƙa na saƙin sarauta a jiki ya ɗora a sama. Kansa da hula baƙa ta dara shigar bakake ya yi daga samansa har ƙasa, ya rage gashin fuskarsa sai haibansa ta sake fitowa amma suman kansa na nan domin hulan ma a saman sumar ta zauna sannan gefe da gefen wajen kunnuwan shi kana ganin suman da ya tara da ɗan yawa.
"Barka da zuwa Yariman Daura. Sauka lafiya Namijin fama. Sauka lafiya Yariman matasa. Farin Yarima kake dogo É—an Nasiru jikan Shitu, barka da zuwa shalelen Masarautan Daura. Barka da zuwa kasaitattacen Yariman Daura. Jama'ar Daura na yi ma dogon Yarima barka da zuwa."
Hannu kawai yake ɗaga musu ba ya magana fuskar nan ta sa ta sake ginshiƙewa saboda jinin mulki ne ya motsa a cikin jininsa.
"Takawarka lafiya ɗan sarki jikan sarki. Angon Balkisu Baban Muhammadu, takawarka lafiya Amintattace, takawarka lafiya mai alheri takawarka lafiya Yarima Allah ya ƙara tsawon kwana Allah ya tsare gaban ka da bayan ka."
"Barka da isowa Hakimin Daura takawar ka lafiya Sardaunan Daura."
Suke ta faɗa kamar za su shiɗe suna mai ƙanƙantar da kan su. Hannu kawai ya ɗaga musu ya wuce tawagan suka bi bayan shi zuwa fadar Sarki Mai martaba Alhaji Dr Nasiru Daura in da yake gudanar da zaman fada a daidai lokacin.
"An gaishe ku. Yariman Daura ya amsa muku."
"An gaishe ku. Hakimin Daura ya gaishe ku."
Haka shugaban dogarai yake ta faɗa. Da irin takunsa na jaruman maza gif! Gif suka shiga fada, suna shigowa suka duƙa gaban Mai martaba da ke zaune kan wata kyakyawan karaga cikin naɗi idanuwansa ne kawai a ake gani su kuma su Wambai suka jeru cikin masu zaman fadan da suka sha rawani.
"Allah ya ja zamanin ka na kawo Yarima gida kamar yadda ka bukaci na jagoran ci haka."
Saleem ya faÉ—a cikin É—an rusunawa.
Jinjina kai Mai martaba ya yi alamun gamsuwa, ko da ba a ganinsa fuskar sa amma kowa ya shaida yau yana cikin farinciki.
"Sarki ya gode ma Hakimin Daura. Allah ya ja zamanin Sardaunan Daura."
Lamido ne ya É—an rankwafa cikin yanayin maganarsa ya ce.
"Allah ya tamaimaki Mai martaba fata duk mun same ku lafiya?
Maimartaba ya sake jinjina kai.
Dogarai suka É—auka.
"Sarki ya gaisheka Yarima, sannan yana yi maka maraba da sauka a masarautar Daura."
"Na gode. Allah ya kara yawan rai da lafiya mai É—orewa."
LamiÉ—o ya faÉ—a yana É—an jinjina kansa.
"Amin Yarima. Allah ya ja zamanin ka, Mai martaba ya amsa."
ÆŠaya bayan É—aya Lamido ya juya yana kai gaisuwa ga walikan fada suna amsawa da an gaishe da Yariman Daura barka da sauka,
Duk da haka fuskar nan ta shi ta nan a ginshiƙe cikin irin yanayin sa.
Yarima ya amsa, Yarima na godiya.
Wani dogari ke ta amsawa.
Ba su daÉ—e a fadan ba Mai Martaba ya ba da Umarnin Hakimin Daura ya raka Yarima zuwa bangarensa domin ya huta.
Bangaren Yarima in da yake sauka in ya zo Daura. Shashe ne mai girma a cikin masarautan.
Har kofar shashin Saleem ya raka shi.
"A fito lafiya Ranka ya daÉ—e."
Kai ya jinjina masa kafin su rabu shi ya juya shi kuma ya shige ciki tuni falon ya cika da hadimai mata wasu na jera abinci wasu na shigowa da shi.
"Barka da sauka Yarima. Barka da isowa ranka ya daÉ—e."
Magajiyar hadiman Fada ta faÉ—a cikin ladabi bayan ta zube kasa, haka ma sauran hadimai mata suka yi suna mai zubewa a gaban shi.
"Yauwa na same ku lafiya?
Ya faÉ—a a iya fatar bakinsa sannan ya shige wani korido.
Ba wacce ta sake motsi sai da ya nisa da in da suke sannan Magajiyar hadimai ta miƙe tana ba su umarnin su yi sauri su jera komai Yarima ya shigo.
Dattijuwa ce ita ce shugaban hadimai mata na gidan Sarki gabaÉ—aya, sannan amintataciya ce a wajen Uwargidan Maimartaba Gimbiya Shahida da umarninta ne ta ce ta yi jagoranci a tanadar ma Yarima da iyalansa duk abin da za su nema.
Cikin lokaci suka gama shirya komai suka bar shashen gabaÉ—aya.
Shi ko LamiÉ—o É—akin shi na musamman ya shige ya yi wanka ya É—an kwanta. Shashen na da girma ga dakunan barci ne ba adadi shi ya sa har ya yi barcinsa ya samu natsuwa ya tashi kafin La'asar bai ji ko motsin Balkisu da yara ba suna wani shashe a cikin bangaren na dabam ita da su Sabuwa.
Alwala ya yi ya fita sanye da jallabiya fara wannan karon sai ya dora rigar sarauta mai ruwan zuma haka ma hulan kansa ta sakin gidan sarauta ne haka ma takalmin kafarsa na irin takalman da yayan sarakunan kan saka ne, ga kaya nan birjit a cikin clothset dinsa na bangaren gidan Sarki sai wanda ya zaba sai saka.
Yana fita suka haÉ—e da Saleem shima da shirin zuwa masallacin.
"Barka da fitowa Ranka ya daÉ—e."
Lamido bai yi magana ba amma ya jinjina kai.
Yana daga cikin shaidar da ya samu, Lamido mutum ne mai daraja lokacin salla bai taba zuwa garin Daura ya yi fashin salla cikin jam'i ba.
Tare suka yi salla da Mai martaba a sahun gaba sai karamin kanin su Mujahid(Amir) ɗan shekara goma sha shidda , Mai martaba ransa fes ga shi zagaye da yaran shi maza yamma da kudu.
Bayan an idar da salla limamin masallacin ya yi É—an tunsarwa akan zumunci da falalar nasu sada shi, daga nan Lamido da Saleem suka koma bangaren shi duk da jama'a na son ganin shi amma Hakimin Daura ya ce Yarima na hutawa ne sai zuwa gobe.
Tare suka ci abinci a bangaren Lamiɗo kamar yadda suke yi in ya zo garin tare da Mujaheed da suka taho tare da shi, ita Balkisu sun riga sun ci na su abincin tuni har an raka ta shashen ɗakunan matan gidan daga ƙarshe ta ci burgi a bangaren Fulanin Daura.
Bayan sun gama cin abincin sun É—an natsa Lamido ya sauya kaya farar shadda har da babban riga, kayan da in ba a Daura ba, ba ya mu'alama da su.
Da rakiyar Salem da Muhajeed ya fara isa bangaren Uwar gidan Mai martaba yar kuma tsohon wazirin Daura.
Gimbiya Shahida, ita ce mahaifiyar Saleem kuma ita ce Fulani ta aura ma Mai martaba lokacin yana tare da Fatima.
Gimbiya Shahida ya'yanta huÉ—u ne uku mata namiji É—aya. Sakeena ce babba tana auran jakadan nageria a England.
Tana can tare da iyalanta(ita ce kuma ke da sarautan Magiyar Gah mata na garin Daura)
Sai Munnira(Magajiyar Hah matan garin Daura) auren zumunci aka yi mata tana auren yaron Hajiya kilishi yayar Mai matarba Sarki Nasiru. Sai Saleem Hakimin Daura, sai auta Badi'atu wacce ba ta daÉ—e da yin aure ba.
Ba su wani jima a shaahenta ba bayan gaisuwa da yi masa maraba ya yi mata sallama sai kuma bangaren Gimbiya Hadiza wacce ke bin ta.
Ita kuma ya'yanta uku. Ita É—in jikar sarkin Kano ce.
Hajiya Sadiya(Bata tuman Daura) tana auren yaron Wambai ne, suna kasar portugal da zama.
Sai Hajiya Zainab(magajiyar Jah mata)
Tana aure anan cikin garin Daura, sai Hajiya Safiyya(Yakumon Daura) tana aure a masarautar Gusau. Itama bayan gaisuwa suka bar nan zuwa shashen mai bi mata.
Gimbiya Maimuna É—iyar marigayi sarkin katsina da ya rasu.
Ya'yanta uku
Yazeed(É—an ruwatan Daura hakimin Babban mutum) yana can kasar waje yana karatu. Sai Sagir(É—an burum É—in Daura) shima yana can kasar wajen yana karatun lauya. Sai Auta Hafsat tana sakandiri.
Sai shashen ta karshe Gimbiya Amratu.
Ita kuma kakanta ƙani yake wajen marigayi Mai martaba Sarki Muhammad shitu kenan kakkani suka haɗa da Mai martaba sarki na yanzu, ita ɗin yar Daura ce kuma yar masarauta.
Yaranta biyu ƙanana ne Mujaheed(Amir) da Mujadala(Amira)
Nan ma gaishe ta suka yi suka fice, lamarin mulki da saurata sai wanda aka haifa a cikin shi ko gaisuwan ma ba wani mai yawa ba ne, shike nan an yi an gama.