← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 92

Sashe 56

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai zai samu hutu da lokaci ishasshe sosai Ammah. A yadda na yi binciken sabon kamfanin da zai fara aiki da su, suna sauyin matukan jiragen in wannan yaje ya yi kamar wata É—aya to za a bashi kamar break na sati É—aya yaje gida ya gana da iyalai da yan'uwa sannan ya dawo kuma kin ga su babu daÉ—ewa sosai kamar na wannan aikin."
"Gaskiya wannan ɗin yafi Kabiru to shima duk tuƙin jirgin ne?
Hamma Kabiru ya sake gyara zama yana faÉ—in" E mana shi ma kamfani ne kamar wanda yake aiki da shi a yanzu amma suna da É—an bambamci.
Shi wannan kamfanin na Chevron Nigerian Limited.
Kamfanin dake da alhakin fitar da Mai kasashen waje domin a cire su kalanzir, fetur, dessel, LLG. Suna da jirage da matuƙa jiragen dake da alhakin fita da man zuwa waje da dawowa dashi bayan an tantance shi. Su kawai aikin su fita da man zuwa ƙasar waje domin a tantance a cire abubuwan da na lissafa miki, kamfanin na haƙo Mai ne kuma suna da jirage da matuƙan da ke jigilan Mai zuwa in da za a tace shi a fidda abubuwa masu amfani a jikinsa yadda za a dawo mana da shi mu samu damar amfani da shi kin gane Ammah.?

"Na fahimta Kabiru. Ubangiji ya tsare mana ku. Shi kuma LamiÉ—o Allah ya sa ya fara a sa'a Allah ya taimake shi ya tsare shi."
Ammah take faÉ—a Hamma Kabiru na amsawa da Amin Amin.
" Ya ce ƙarshen watan nan ko ba su saka masa hannu ba zai dawo gida ya yi hutu sosai kafin ya fara aiki da sabon Kamfanin."
"Allah ya amince. Allah ya ba shi nasara."

Sun É—an jima suna ta hira rabin hiran ta su duk akan LamiÉ—o ne sai wajen biyar saura Hamma Kabiru ya yi sallama da Ammah da Baffa ya kama hanyar Jalingo tunda motarsa ce tafiyar awa uku ce zuwa da rabi.

Ummu kuma sai da ta yi kwana huɗu a asibiti sannan aka sallame ta tare da dokokin likita, ta riƙa samun hutu da barci sannan sun ba ta bedrest ga maganguna har da na barci tunda an faɗa musu ba ta samun barci cikin ta kuma ya na gabda shiga wattani huɗu likita ya ce tana buƙatar kulawa da an ga wata matsala a dawo da ita asibiti sannan ta riƙa cin abinci mai gina jiki saboda inganta lafiyan abin da ke cikin ta.

Bayan sun dawo gida Hamma Abdulrrahman ya sake zaunar da ita daga shi sai ita a ɗaki ya sake yi mata faɗa daga karshe ya koma lallashi ya faɗa mata ga dokokin likita sai ta kiyaye ma kanta da shiga damuwa in tana son ta tsira da abin da ke cikin ta, bai barta ba sai da ta yi masa alƙawarin za ta daina damuwa sannan za ta kula da kanta ko domin abin dake cikinta da take jin wani son shi na ƙaruwa a tsakiyar kirjinta ba kukan sakin da Habib ya yi mata take yi ba har yanzu  kukan bakin ciki da faɗa da zuciyarta da har lokacin ba ta daina son Habib da tunaninsa ba. Tana yi iya yin ta domin ta manta da shi amma ta kasa da ta keɓe shikenan za ta yi ta tunanin shi da irin good momories ɗin su tare da juna ba ta ma sanin lokacin da ta ke fara kuka.

Ba za ta taɓa mantawa da Baɗɗo ba sai da ta kwana goma da ita tana kula da ita sannan ta koma gida tunda sun koma makaranta. Sannan Ummin ikki ma kullum sai ta leƙo kowa dai burinsa ta samu ta sake ta fara walwala. Ga Baffa da duk ya sakar ma Hamma Abdullahi harkokinsa yana zaune a gida saboda ita. Shi dai nasihan shi ta daina damuwa ta yadda da kaddaranta. Ammah ma tana nuna nata kulawan amma in ta yi lallashin ta gaji za ta fara masifa ne da faɗa, ga Hamma Saddam ma yana iya bakin ƙoƙarin shi wajen zama da ita yana yin duk wani abu da zai sanya ta farinciki, haka ma Hamma Abdulllahi, da matan su in ba su zo ba yau ba za su zo gobe su Hamma Jibo duk da ba sa kusa duk ranar duniya sai ta yi magana da su ta wayar Amma tunda ita wayarta tana cikin kaya ta kashe kanta ma ba chaji, ganin yadda kowa ya damu da ita ya sa ta rage damuwa amma Allah kaɗai ya san halin da zuciyarta ke ciki tare da Ammah suke kwana Baffa ne ya ce ta riƙa kwana da ita amma in ba magungunanta ta sha ba tana daɗewa tana juye-juye ba ta samu barci ba gani take yi kamar a mafarki wai yau ita ce a gida a matsayin bazawara. Ba ta sare ba tunani take da yaƙinin cewa Habib zai dawo ya neme ta, tana ma mantawa da cewa har abada yanzu ta haramta ga Habibu ita soyayyar shi ta gama rufe mata ido da duk abin da ya yi mata ta kasa jin tsanar shi ta kasa daina son shi, duk da tana son ta tsane shi ɗin amma ta kasa tunda ba ita ke da alhakin sarrafa zuciyar ta ba.

Hamma Abdulrah. yana can kasar turai ya ji labarin abin da ke faruwa shi auren ma baya nan aka yi sai ga shi yana can komai ya ƙare. Ya shiga damuwa sosai barin ma da Saddam ke ba shi labarin yanayin da Ummun ke ciki Vedeo call ya kira aka bata ya yi magana da ita kuka kawai take yi tana ma kasa mgana shima daga ƙarshe kashewa ya yi ya fashe da kuka, yana da saurin kuka da tausayi shi ya sa bai sake kira ba sai dai duk lokacin da ya yi magana da wani na gida zai ce a gaishe masa da Ummu, ba ya son su sake magana ta saka shi kuka ga shi yana shekaran ƙarshe ne karatu yake yi kamar injin ya yi ya gama shima ya dawo gida cikin ahalinsa.

Mami ma suna Paris Hamma Saddam ya faÉ—a mata halin da ake ciki ai a daran ta matsa ma Abban islam cikin kwana biyu suka dawo gida Nigeria. Washe gari kuma suka sake biyo jirgi zuwa Jimeta. Tun da Mami ta zo ta ke kuka kowa ya san kukan da take yi kuka ne na fami daga tsohon gyambon dake zuciyanta. In ta kalli Ummu sai ta ji kukanta ya kasa tsayawa ta yi kuka kamar ranta zai fita sai da Baffa ya zauna yana ta ba ta baki Abban islam na gefe domin ko ya ba ta baki ba ta yin shuru sai ta ce wai ba zai gane yanayin ba ne.

Ummu Salma kukanta ya dawo sabo da zuwan Mami da kukan da take yi, tausayin Ummu Salma take ji duk da ta É—an fi ta shekaru ita lokacin ko ashirin ba ta cika ba ta faÉ—a wannan kaddaran amma duk yadda za a fassara lamarin ba wanda zai gane yanayin sai wanda abin ya faru da shi.

"Baffa yaron nan ya cutar da Ummu Salma. Muma ya cutar damu kuma wallahi sai Allah ya saka mata."

Mami take faÉ—a tana kuka kamar ranta zai fita.

"Ummu ki yi kuka ki yi ta kuka ko za ki sami salama. Amma kar ki yi dogon damuwa cuta za ta kama ki, in kuma hakan ta faru za ki samu cikin damuwa."

Haka take ta faÉ—a ma Ummu lokacin da ta rungumeta a jikin ta dole Alhaji Isa ÆŠanmarke ya nemi hotel ya kwana washegari ya juya Kaduna tunda yara na gida tare da su Baraka, ya bar Mami a Jimeta ita ta ce ya tafi kawai za ta zo daga baya.

Zuwan Mami ya tado ma Ummu taɓon ta amma kuma ta samu sauƙi saboda Mami ta zaunar da ita, ta ba ta labarin rayuwarta da yadda ta yi gwagwarmaya da kaddaranta daga ƙarshe ta yi nasara da yadda Ammah da Baffa suka yi ta ƙoƙari a kanta.

"Ummu Salma akwai zafi na sani amma sai kin daure. Yanzu ki sani ke uwa ce a gobe. Ki kula da kanki saboda abin da ke cikin ki, ki yi haƙuri ki yi haƙuri ki cire damuwa a ran ki, in kin ji kuka ki yi kuka domin shi kaɗai ne zai samar miki da salama."

Haka take ta faɗa mata cikin ƙarfafa mata gwiwa.

"Za ki ci wannan jarabawar Ummu. Za ki yi nasara kamar yadda na yi. Muna nan dake Allah zai kawo miki wanda zai share miki hawaye. Shi kuma Habib sai ya yi Fargar jaji da ikon Allah."

Ummu Salma tana kuka ta nuna ma Mami jikinta tana kuka take faɗin" Mamina wa zai aure ni a haka? Me na ke da shi? Ba ni da budurci ba ni da jiki mai kyau, nonuwana sun kwanta, ciki gare ni Mami nan da wata biyar zan haihu na buɗe na zama uwa na shayar da jariri, Mami ki faɗa mini wa zai kwashe ni a haka? Me ya sa shi da ya fara bai ƙarisa ba Mami na?
Haka Ummu ke faÉ—a tana ta gunjin kuka.

"Allah zai kawo shi, wanda ba jikin shi yake so ba ke yake so Ummu in kina tunanin ba zai yuyu ba ki riƙa duba rayuwata. In kika kalle ni za ki samun ƙwarin gwiwan cewa ke ma komai zai wuce zai zama sai labari, sai dai ki tuna ki yi mirmishi ko kin yi kuka sai dai ki yi kukan farinciki da tuna rayuwar baya."
Chapter 56 · 0% Book details