Sashe 22
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To in ba ka sona ba ka son ka haihu da ni me ya sa ka aure ni.? Sannan me ya sa ka yi mini ciki? Ai ka san ba ni na ba ma kaina cikin ba."
Ummu ta sake tambayan shi cikin kuka hawaye na kece mata
Kallon ta ya yi, tabbas ya yarda ita daƙiƙiiya ce sai ya yi mata bayani? Sai ya furta mata dalilin da ya sa ya aureta sannan za ta gane lalle ya yarda dakikiya ce Ummu ba ta da lissafi.
Tsaki ya ja kafin ya ce" Lalle na yarda rashin ilimin boko mai zurfi ya cuce ki, tunda har yanzu tunanin ki bai faÉ—a miki dalilin da ya sa na aure ki ba."
Yana gama faÉ—in haka ya juya ya koma cikin É—aki, ya bar Ummu na tsiyayan hawaye.
Hamma Kabiru da Hamma Abdulrrahaman sun sha nuna mata akwai ranar da za a iya goran ta mata rashin karatun ta mai zurfi a bangaren boko, ɗauka ta ke yi suna faɗa ne saboda ta yi zuciya ta ce za ta yi, sai yau da Habib ya goran ta mata ta sake aminta da maganar su, sai dai har a lokacin ba ta yi nadamar haka ba, ba ta son karatu har kuma gobe ba ta so iya sakandirin da ta gama ya ishe ta zaman duniya tunda tana da na muhammadiyan fiye da yadda ta samu na bokon, Hamma Saddam ya taɓa faɗa mata wata rana tana ji tana gani za a yi mata gorin ilimi sai ga shi yau Habib ya yi mata, hawaye ke kwaranyo mata ga jikinta ya sake ɗaukan zafi saboda sanyin da ta sha, tana son komawa ciki amma tana tsoron ka da Habib ya shirya mata wani gadan zaren, ba ta koma ciki ba sai da ta tabbatar da ba shi a falon sannan ta lallaɓa ta shige ɗakin ta ta rufe ta kwanta a saman gado ta fashe da kuka.
"Wayyo ni Ummu-Salma Ubangiji ka kawo mini agaji"
Ta faɗa a fili tana mai dafe kanta da ta ji yana sara mata, me ya kamata ta yi? Zama tare da Habib yana neman yi mata illa da karfin cin tuwo ba nata ba ne, ya kamata ta sanar da wani abin da ke faruwa. Ta daɗe kwance tana kuka amma ta rasa mafita, kunya ta ke ji da nauyi yadda kowa a dangi da ƙawaye suke yi mata kallon wacce ta yi dacen miji yanzu kuma ta je da wannan mganar? Amma in ba ta faɗa ba akwai yuyuwar ko ta ƙarfin tsiya sai Habib ya cimma burin sa na raba ta da cikin nan ita kuma ba za ta bar shi ya cika wannan burin ba, har ta rarrafa ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ba ta samu mafita ba tana salla tana kuka bayan ta idar ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah ya tsare ta daga sharrin Habib ya kuma tsare cikin jikin ta.
Haushin kanta take ji da har a lokacin ba ta ji ko da son Habib ya ragu daga cikin zuciyarta ba, sai ma ta ji kamar ana ƙara hura wutar ƙaunar sa ne a cikin zuciyanta. A saman darduman da ta yi sallan ta kwana cikin matsanan cin ciwon jiki da kai, sanna ga zazzaɓi mai zafi sallar asuba ma sai da safe lokacin akwai hasken rana sannan ta samu damar yi, shima a zaune saboda jiri take gani in da ta idar nan ta sake sulalewa ta kwanta numfashinta na sarƙewa ga zafin zazzaɓi kamar za ta mutu, ganin ta yi in ta cigaba da zama a cikin ɗaki za ta iya mutuwa Habib ba shi da asara ya sa ta rarrafa zuwa saman drowers ɗin gefen gadon ta lalubo wayarta Ummin ikki take da niyar kira amma dishi dishi ta ke gani tsabar zafin zazzaɓi.
Wayar na hannunta kira ya shigo ba ta iya gane sunan saboda yanayin da ta ke ciki ta samu dai ta yi ƙarfin halin ɗaga kiran sai ta ji muryan Baɗɗo.
"Sisna gani a ƙofar bangaren ki, ina ta knooking shuru ko bakwa nan ne?
Jin muryan BaÉ—É—o da abin da ta ce ne ya sa ta ji kamar an buÉ—e mata idanuwanta wani karfi ta ji ya zo mata da ya sa muryatan a dishe ta ce.
"Ga ni nan zuwa."
Sai ta sauke wayar a saman gado da taimakon gadon ta iya miƙewa tsaye tana dafa bango har ta buɗe kofar Bedroom ɗin ta fita falo tana dafe da bango, ƙofar ma a buɗe take Habib ya fita ita kuma ba ta san ma fitan shi ba, ballatana ta taso ta rufe.
Ita kuma Baɗɗo ba ta murɗa handel ɗin ba a tunanin ta ƙofar na rufe ne kamar yadda Ummu ta saba rufewa sai an yi knooking take zuwa ta buɗe ma wanda ya zo.
Tana buɗe ƙofar suka yi arba da Baɗɗo wacce sai da ta tsorata da ganin yadda Ummu Salma ta koma.
"Ummu lafiya.?
Ta faɗa cikin fizgo mganar, ita kuma Ummu jiri ya kwashe ta sai kawai ta faɗa ma Baɗɗo a jiki, da sai da ta saka ƙarfi ta iya riƙe ta suka shiga cikin falon da kafa ta rufe ƙofar lokaci ɗaya tana sake faɗin.
"Innalillahi Ummu lafiya?
Ba ta amsa mata saboda shaƙan turaran Baɗɗo da ta yi ya ta yar mata da zuciya Amai ta ji yana taso mata shi ya sa ta sake ta, da dafe bango ta isa tiolet ɗin falon nan ta fara kwara Amai, a su kwane Baɗɗo ta bita har ciki ta riƙe ta, tana yi mata sannu aman ba komai sai ruwa ruwa sai naman da ta ci jiya da daddare, a galabai ce ta gama aman Baɗɗo ce ma ta taimaka mata ta wanke bakin sannan ta kama ta suka dawo falo.
Ummu a kan kujera ta zube ta na mayar da numfashi BaÉ—É—o ta zauna gefen ta tana faÉ—in.
"Subhanalla jikin ki ya yi zafi ne haka ne Ummu? Habib ya fita ne?
Shuru ta yi ba ta yi mgana ba tana ma yar da numfashi kawai sai BaÉ—É—o ta jawo jakarta ta fiddo wayarta lokaci É—aya tana faÉ—in.
"Bari na kira shi ko asibiti sai mu je amma barin ki a gida ke kaÉ—ai a yanayin ki ai akwai matsala Sisna."
Da sauri Ummu ta riƙe hannun Baɗɗo cikin mamaki ta kalle ta sai ta hau girgiza mata kai.
"Wai kar na kira Habib É—in?
BaÉ—É—o ta tambaya cikin mamaki.
Sai Ummu ta gyaÉ—a mata kai tana mai lumshe idanuwanta sai ga hawaye ta gefe da gefen kumatun ta.
"Sabo da mene ne! Ko ba ya garin ne?
BaÉ—É—o ta sake tambaya cikin mamaki.
"BaÉ—É—o."
Ummu ta kira ta a raunane ta amsa da sauri.
" Naam."
"Ina da ciki."
Ta faÉ—a tana numfashi da sauri da sauri.
Sai BaÉ—É—o ta washe baki kafin ta ce" Da man a yadda na gan ki na yi tunanin cikin ne. Congratulations Sisna"
Ta faɗa da duka haƙoran ta a waje.
"Amma Habib."
Sai ta kasa ƙarisawa Baɗɗo ta kalle ta kafin ta ce.
"Amma Habib me ne? Me ya faru da shi?
Ummu ta miƙa ma Baɗdo hannu ita ta taimaka mata ta tashi zaune ta jingina da jikin kujera jin yadda jikinta ya yi zafi ne ya sa Baɗɗo ta ce.
"Sannu Zazzaɓi ne ma a jikin ki Ummu."
Shuru ta yi mata ba ta yi mgana ba.
"Kun je asibiti?
Sai Ummu ta girgiza mata kai cikin mamaki BaÉ—É—o ta ce.
"To saboda mene ne, Habib bai san ba ki da lafiya ba ne?
Ummu ta runtse idanuwanta sai hawaye suka kece mata.
Ganin haka ya sa sai jikin BaÉ—É—o ya yi sanyi.
"Sisna wani abu ne ya faru da Habib É—in ne?
Ta sake faɗa tana riƙe hannayenta ganin yadda take hawaye wasu na ganganrowa wasu na sake kwaranya.
"Me ke faruwa ne Ummu Salma?
Ta sake tambayan ta cikin damuwa da ya bayyana har a muryan ta.
"BaÉ—É—o."
Ummu ta sake kiran sunan ta wannan karon bata ba ta damar amsawa bq ta cigaba da faÉ—in.
"Habib ya ce ba ya sona sannan kuma ba ya son haɗa zuru'a da ni."
BaÉ—É—o ta zaro ido, tana kallon Ummu da ta fashe da kuka har yana fidda sauti.
"Me ne kika ce?
BaÉ—É—o ta faÉ—a da sauri lokaci É—aya tana zaro idanuwanta waje.
"Haka ya ce Baɗɗo. Yanzu ma ƙoƙarinsa na zubar da cikin dake jikina."
Ummu ta sake faÉ—a cikin kuka, lokaci É—aya tana ma yar da kanta saman cinyar BaÉ—É—o.
"Baɗɗo Habib ya canza ya tsane ni bai da mu da ni ba. burin shi kawai cikin dake jikina ya fita. Burin shi kawai na rasa cikin da ke jikina, ya faɗa mini bai aure ni domin ya haihu da ni ba."
Ta ƙarishe faɗa cikin kuka,har da shessheƙa.
BaÉ—É—o da itama har ta fara hawaayen tausayin yar'uwanta nata ta ce.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un"
"Me na ke ji haka Ummu? Shi Habib É—in?
Ummu ta kasa mgana ban da kuka ba abin da take yi, kukan baƙinciki da takaici kanta kukan ciwo da zafin zazzaɓin jikinta kukan samun salama tunda ta samu ta iya faɗa ma Baɗɗo damuwarta.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t
*06*
Cikin kuka mai tsanani da shessheƙa Ummu ta sanar ma da Baɗɗo abin da ke faruwa. Lamarin da ya girgiza duniyar Baɗɗo kafin Ummu ta gama ba ta labarin halin da ta ke ciki hawaye sun gama jiƙa ma Baɗɗo gaban doguwar rigar atamfar dake jikinta.
Tana kuka Ummu na kuka suka haɗu suka rumgume juna suna ta kuka a tare, ita Ummu kukan halin da ta tsinci kanta a ciki take yi da tausayin kanta sannan tana kukan takaici na har a yanzu tana yi ma Habib uziri, har yanzu tana tunanin cewa zai dawo gare ta, har a lokacin tana tunanin wasa yake yi yana son ta sannan kuma yana son haɗa zuru'a da ita. Ga gaskiya ƙiri-ƙiri amma soyayyar Habib ta rufe mata ido daga ganin wannan gaskiyn.