Sashe 67
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammah ta kwashe da dariya Baffa na kallonta yana jin sanyi a ran shi, gabaɗaya ta faɗa damuwar halin da Ummu ke ciki na ta sukanta a ciki, shi ya sa ta yi ta rama a tsaye amma yau saboda zuwan Lamiɗo ta saki har yana ganin dariyanta kuma farincikinta ya kasa ɓoyuwa shi kan shi ya tabbata Ammah renon ɗa na cikinta ta yi ma Lamiɗo shi ya sa take jin sa fiye da ƴaƴan cikinta.
Shi dai har ya gama cin abincin Ammah na yi masa hira kan zuwan LamiÉ—o yana jinta kawai yana mirmishi.
Suna cikin É—akin ne ma BaÉ—É—o ta zo gidan, har É—akin Baffa ta shiga suka gaisa ta ce daga makaranta take ta biyo.
"Sannu BaÉ—do, Ammah ba ta abinci ta ci.".
Baffa ya faÉ—a yana kallon Ammah.
"Ta je Kitchen ta É—iba mana"
BaÉ—É—o ta amsa da bari ta yi salla tunda tana makaranta aka yi la'asar kuma tana sauri ba ta tsaya ta yi acan ba.
ÆŠakin Ammah ta shiga Ummu na kurya cikin É—akinta kwance tana tunani ba ta ma ji shigowar BaÉ—É—o ba sai da ta ji ta faÉ—o saman gadon sannan hankalinta ya dawo kanta.
"Kina kwance kullum kullum dai Sisna?
Ta faÉ—a tana mai kallon Ummu Salma da ta É—an tashi zaune tana kallon ta.
"Daga makaranta kike?
Ta tambaya, daidai BaÉ—É—o na sauke jakar hannunta lokaci daya da yaye mayafin jikinta.
"E na ce bari na É—an leko ki kwana biyu? Ya jikin! Ina fatan dai ba wata matsala,?
"Babu."
Ta faÉ—a a sanyaye.
"Kin tabbata?
"Allah bana jin komai, sai yar kasala ne da É—an ciwon kai."
"To magungunanki sun ƙare ne?
Sai ta É—an jinjina kai kafin ta ce" Bai wuce in na sha yau da gobe ba."
"Yakamata mu koma asibiti "
BaÉ—É—o ta faÉ—a tana kallon cikin jikin Ummu.
"Cikin fa har ya É—an turo"
Ummu ta bi cikinta da kallo saboda riga da sikat ta saka shi ya sa sai cikin ya É—an turo
Shuru kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba
"Kila fa in muka koma su ce ki fara zuwa awo".
Ummu ta kalli BaÉ—É—o na wani lokaci nan ma ba ta yi magana ba.
"Me ya faru?
"Sai na haihu har abin da na haifa ya girma bai san uban shi ko ba ta san uban ta ba?
Ta tambaya idanuwanta na cikowa da ƙwallah.
BaÉ—É—o ta ce" To wa ya ce ba zai san uban shi ba? Za a faÉ—a masa komai har labarin tun yana ciki uban ya ce ba ya bukatarsa."
Baɗɗo ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa.
"Bari na yo alwala'
Tana gama faÉ—in haka ta shige tiolet domin ba ta san ma ta tsaya Ummu Salma na damunta da mganganu kan Habib wallahi ta tsane shi ta tsani ma jin sunan shi
Fatan ta yadda ta tsane shi itama Ummu ta tsank Habib amma ina, ita har gobe tana begensa tana ganin zai iya neman ta, ta manta da cewa ya ce ya riga ya gama amfana da ita.
Alwala ta ɗauro ta zo ta yi salla bayan ta idar ta fita ta je ta ɗibo abinci ta zo ta hau gadon tana ci suna ɗan taɓa hira da Ummu, ko da ta kawo mata maganar Habib Baɗdo za ta ɓata rai ta kauce da hirar.
"Har yanzu Habib bai kira ki ba?
Ummu ta tambayeta tana kallon ta.
"Ni bai kirani ba, tunda ya sake ki na goge lambar shi a cikin wayata."
Ta ba ta amsa tana mai cigaba da cin abincinta.
"Me ya sa kika yi saurin gogewa? Da kin kira shi, kin tambaye shi me ya sa ya yi mini haka?
BaÉ—É—o ta kasa haÉ—iye abincin da ta saka a bakinta tana kallon Ummu da mamaki.
Ganin har ta fara hawaye.
"BaÉ—É—o na kasa mantawa da Habib. Wallahi a mafarkina da farke na duk tunaninsa ne."
Ta karishe faÉ—a cikin kuka.
"Kowa laifina yake gani, ba laifina ba ne, zuciyata ne har yau tana son Habib na kasa jin na tsane shi. Nima ina so na tsane shi, amma na kasa ya zan yi? Na rasa yadda zan yi da rayuwata."
Ta ƙarishe faɗa tana mai fashewa da kuka
Baɗɗo ta yi shuru ta ma kasa mgana, maganganunta sun ƙare duk wani kalami na lallashi ta gama zayyana ma Ummu amma har yau ba ta gane annabi ya faƙu ba.
"Ni ba ni da abin da zan kira Habib na faɗa masa. Domin duk wani abun da za mu sani ya sanar damu. Ummu ki saka a ranki ko da ganganci Habib ya kira ni sai ya yi nadama wallahi, domin ba zan raga mishi ba. Tunda shi batulu ne kuma mayaudari, sannan maganar kina son shi, ko kin kasa tsanar shi duk bai ta so ba, ki yi ma kanki faɗa Ummu cewa fa ya yi bai taɓa son ki ba, don jikin ki ya aure ki. Kuma ya gama amfana da ke shi ya sa ya sake ki, da cikin shi amma bai damu ba, to ke ki yi tunani da hankalinki wanna mutumin da ya gama yi miki haka ne zai dawo gare ki? To ko ma ya dawo da sunan mene? Bayan abin da ya haɗa ku ya riga ya kawo karshensa duka. Ko kin manta saki uku Habib ya yi miki ne Ummu Salma?
Ta gama faÉ—a tana kallonta.
Ummu tana hawaye ta ce" Ban manta ba"
"To gwara ki tuna cewa har abada aure ya haramta tsakaninki da Habib a yanzu. Kuma koma bai haramta ba shi baya sonki ba kuma zai dawo gare ki ba, in ma za ki yi daina tunanin ki cire sa a cikin zuciyarki ki cire shi, in kuma ba za ki iya ba har yanzu kina son shi to ki ba da himma. Amma ina so ki sani ko mutuwa kika yi wallahi tallahi Habib ba zai damu ba domin ba shi da asara."
BaÉ—É—o ta faÉ—a tana zare ma Ummu Salma idanuwanta domin yau itama ta kai ta bango.
Ummu ba magana sai kuka, tana faÉ—in kowa haka yake ce mata ko jiya ma Ammah ta yi mata faÉ—a yau ma Baffa ya yi mata nasiha.
"To ai duk muna son ki ne, gaskiya ce mai É—aci muke faÉ—a miki. Bayan mu masoyan ki, ba wanda ya san zafin ki Ummu Salma."
Ta faÉ—a tana É—an sassauta fushinta.
Ummu na kuka take faÉ—in" Ina so na manta nima ina so manta. Amma na kasa."
Sai gunjin kuka, tausayinta ya kama BaÉ—É—o dole ta sauke filet É—in abincin hannunta a saman dirowan gado ta karisa wajen Ummu ta rumgumeta tana lallashinta.
"Ki yi hakuri, ke ce za ki yi ma kanki wannan yaƙin. Ki koma ga Allah ki roƙesa ya cire miki, in sha Allahu zai cire miki."
Ummu ta amsa da cewa wallahi tana yi tana addu'a amma kamar sai kara gaba tunaninta akan Habib yake, ita kuma BaÉ—É—o na sake ba ta tabbacin kar ta gaji ta cigaba da kai kukanta wajen Allah zai kawo mata É—auki.
Da lallashi da ban baki Ummu ta yi shuru.
Sannan BaÉ—É—o ta karishe cin abincin ta ta fita da filet É—in zuwa kitchen ta haÉ—a wanke-wanken ta wanke sannan ta share tsarkar gidan Ammah na ta saka mata albarka.
Sai da ta yi mangariba sannan ta yi shirin tafiya.
"Ke wai na ji Ummi na faÉ—in gobe Hamma LamiÉ—o zai zo tare da iyalansa."
BaÉ—É—o ta faÉ—a lokaci É—aya tana gyara zaman jakarta a saman kafadanta.
Suna tsaye a tsakar É—akin Ummu ta zumbuÉ—a hijabin da ta yi salla da shi za ta É—an rakata haraban gida..
"Uhm haka na ji Ammah na faÉ—a."
Ummu ta faÉ—a cikin basarwa.
Bata son ya zo, haka kurum ba ta son su samu baki anan kusa, ita dai da Baffa ya sani ya barta ta bi Mami Kaduna da ta fi samun kwanciyar hankali.
Dazu ma da BaÉ—É—o ta yi mata maganar waya ta ce sun yi waya da Mami ta ce za ta aiko mata da sabuwar waya da layi, wayarta ba za ta iya amfani da ita a yanzu ba.
"Ai Ummi ta ce tun safe tana nan gidan Ammah ta ce ta zo ta taya ta abincin tarban shalelen Ammah.."
Ta faÉ—a tana yar dariya
Ummu ta kalleta kafin ta ce" Uhm kin san halin Ammah, in ban da ma ɗaukan ma kai, girki ko su Adda Suwaiba ba za su yi musu ba? In su Hamma Jibo ne za su zo ban taɓa ganin ta yi musu girki na musamman ba amma Hamma Lamiɗo duk abin da yake so ita ce za ta yi masa."
Ummu ta karishe faÉ—a da jin haushin Ammah haka kurum mutum kato da iyalansa amma har yau ba ta daina wahala a kan shi ba
"Ke ko É—an gaban goshin Ammah ne, naji ma Ummi na faÉ—in za su kwana biyu."
Ummu ta yi shuru ba ta sake magana ba tunani take yi in da hali ta guje ma gidanan har sai sun tafi, duk da ba dariya za su yi ma kaddaranta ba, ita kawai tana kunyar ya zo ya ganta a gida kawai a ce mijinta ne ya sake ta sai abin ya yi mata wani iri.
Bayan BaÉ—É—o ta yi ma su Baffa sallama Ummu ta tafi rakata har haraban gidan, suna tafe BaÉ—É—o na tambayan ko Shamsiya ta zo? Ummu ta ce ta zo kwanaki ta ma ce za ta dawo amma ba ta dawo ba.
"To watakila ta koma makaranta ne"
BaÉ—É—o ta faÉ—a Ummu ta yi shuru kafin ta ce" An ya! Ko dai ta ji haushin mganganun da Ammah ta faÉ—a mata ne"
"Me kuma ya faru?
BaÉ—É—o ta faÉ—a tana zare idanuwaanta.
Nan Ummu ta kwashe komai ta faÉ—a mata.
"Kin san halin Amman taki, ba ta da haƙuri ta yi ta masifa."
Ta karishe faÉ—a tana kallonta.