← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 92

Sashe 41

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Take faɗa cikin fitan hayyaci, domin ba ta ji ba ta gani, tunanin ta hangenta shi ne in Habib ya sake ta ya gama lalata mata goben ta, ya cuceta ya mai da ita ƙaramar bazawara, sannan tana son shi tana son aurenta za ta yi komai domin ta ga ta tsira da aurenta.

"Kika ce me?

Ya tambaya yana mata wani kallo

"Na ce, e zan zubar da cikin wallahi na yarda."

Ta faɗa hawaye na kwaranyo mata yadda ya ga ta ruɗe ne tana roƙon shi har tana cewa ta yarda za ta zubar da ciki ya sanya shi nishaɗi ya kwashe da wata dariyan jin daɗi.

"Na yarda ko yanzu ne ma mu je a zubar amma don Allah kar ka sake ni "

Ta sake faɗa tana haɗe hannayenta waje ɗaya alamun roƙo.

"Yarinya kin makara."

Ya faÉ—a yana dariya sannan ya cigaba da rubutun sa.

"Wataƙila da wata ɗaya kafin yanzu ne kika ce mini haka da zan iya sauraran ki, amma yanzu lokaci ya kure miki, da man ai na sha faɗa miki sai kin yi nadama, a ranar da nadamar ba za ta yi miki amfani ba lokacin da na ke bin ki, kina mini yadda kike so ai ba ki yi tunanin rana irin ta yau za ta zo ba, duk ɗaukan maganganuna kike yi a wasa?

Ummu ta kasa magana ban da kuka ba ta komai.
Ɗagowa ya yi yana kallon ta kafin ya cigaba da faɗin" Ni yanzu ban damu da ki zubar da cikin jikin ki , ko ki zubar ba ko ki haife shi duk wannan ya rage na ki, dake da cikin duka bana so, ba na kuma buƙatar ku a cikin rayuwata "

Ya ƙarishe faɗa yana nuna ta da yatsa daga sama har ƙasa cikin ƙyama.

Ummu ta gigice ta sake fashewa da kuka tana faÉ—in" To ba ka ce jikina kake so ba? To ai ga jikin nawa ai ba na hana ko?
Ta faÉ—a tana yi kamar za ta haura a saman kujeran da yake zaune.

"Ke kar ki hauro mini nan"

Ya faÉ—a yana zare mata ido.

"To to na zauna "

Ta faÉ—a lokaci É—aya tana zaman dirshan a gaban shi yanayinta kawai za ka gani ka fahimci ta rasa natsuwarta ba ta ma san abin da take yi ba, ballantana abin da take furtawa.

Ganin ta cikin wannan yanayin yafi masa komai daÉ—i, nishaÉ—i da farinciki yake ji da man ya ce sai ta yi nadama to kaÉ—an ta gani.

"Ai ni gama moran duk wani albarkatun jikin ki, babu wani sauran maiƙon da ya rage da ban gama lashewa ba."

Ya faɗa yana dariya ƙasa-ƙasa har yana kashe mata ido ɗaya.

Ummu na kuka tana kallon Habib kamar zai yi mata gafara tana rokon shi Allah da Annabinsa kar ya sake ta, amma ina bai ƙara sauraran ta sai da ya gama rubuta abin da ya yi niyya sannan ya miƙa mata , ta kasa karɓa lokaci ɗaya tana girgiza kanta cikin kuka.

"Karɓi mana "

Ya faɗa yana mai sake miƙa mata takardan.

"Don Allah Habib. Kar ka. Sa ke ni."

Ta ƙarishe faɗa kamar za ta shiɗe domin har numfashinta ya fara ɗaukewa.

"Ai na ma riga na sake ki Ummu Salma."

Zuciyarta ta tsinke, idanuwanta suka fara rawa, hannaunta É—aya ya kama ya tusa mata takardan lokaci É—aya yana faÉ—in" Tunda dare ya yi na yi miki alfarman ki kwana amma gobe da safe ki tattara kayanki ki koma gidan ku, kayan É—aki kuma suma ki zo ki kwashe kafin masu gidan su bukaci dakin su."

Yana gama faÉ—in haka ya kwashi takardansa da biron sa ya wuce yana sake faÉ—in" Alhamdulillah."
Har yana wani harba ƙafafuwansa, Ummu ta bi shi da kallo cikin zubar ƙwalla takardan ta matse a hannunta tana sakin kuka da ƙarfin iyawanta, kuka ta fashe da shi da duka muryanta da ubangiji ya ba ta, kanta a ƙasa kamar tana sujudda take rusa kuka kamar ranta zai fita Habib ya gama tozarta, irin tozarcin da bata taɓa jin labarin an yi ma wata mace ba, Habib ya sake ta da ƙaramin ciki bayan ya gama lalata mata rayuwa ya mayar da ita ƙaramar bazawara, ya kunya ta iyayenta ya cutar da ita sannan ya cutar da zuciyan ta.

Koda ta ɗago daga durkushen da ta yi ruwan hawaye da majina ya gama jiƙa cafet ɗin gabanta sannan fuskarta har ta jirkice tsabar kuka da tashin hankali, a hankali ta miƙe tana jin jiri na ɗiban ta, kanta na sara mata da ƙarfi, cikinta ya cure waje ɗaya daƙyar ta iya jan kafafunta tana dafe bango ta koma ɗakinta tana matsanacin kuka takardan sakin na matse a hannunta ta kasa dubawa, ba ta son gani ba ta son ganin wannan baƙin rubutun Habib a gare ta, kukan ta kawai take yi da karfi ba ma tunanin ta yi shi a cikin zuciyarta, yi take yi tana shessheƙa, tana fidda sauti ga majina na shatata, ga ruwan hawaye kafin kace me gaban riganta ya jiƙe da hawaye, fuskarta ta kumbura saboda kuka idanuwanta sun tasa sun yi jajir kamar gawarshi, daga karshe ma da ta gaji da kukan dole ta haƙura ta koma ajiyar zuciya tana faman sauke numfashi a jejjere kamar wacce ta yi gudun tsere tana zaune a ƙasan tayels a gefen gado kanta na gefen gadon ta ɗora saman hannayenta lokaci ɗaya hawaye na kwaranya har a saman hannayen ta amma ta daina kuka da sauti sai dai a cikin zuciyanta take jin wani ɗaci da raɗaɗin da ba za ta iya misalta yanayin ba.

Takardan sakin na jimƙe a hannunta ganin zufan hannunta ya fara jiƙa takardan ya sa ta ɗan ɗage zanin gado ta tura takardan ta koma ta kwantar da kanta tana ta tsiyayan hawaye yadda ta ga rana haka ta ga dare barci ko ɓarawo bai sace ta ba a cikin kunnuwanta aka fara kiran sallan asuba, duk kuma tana zaunen har wasu masallatan suja tayar da salla amma ta ƙasa tashi saboda kuka ga jikinta duk ya yi tsami kanta saboda ciwo ba ta ma san ma ɗago shi, sannan ga idanuwanta sun kumbura sumtum ko iya buɗe su ma ba ta yi, ko'ina na jikinta ya yi tsami saboda kwanan da ta yi a zaune cikin yanayi mara daɗi, da rarrafe kamar yar koyo ta shiga tiolet ta kama ruwa sannan ta wanke fuskarta da ruwan zafi ta ɗauro alwala haka ta fito da rarrafe nan domin ba za ta iya tashi ba ji take yi kamar kafafunta ba za su iya ɗaukan gangan jikinta ba.

Salla ma a zaunen ta yi, ta daina zubar ƙwalla amma raɗaɗin dake cikin zuciyarta kaɗai ya isa ya yi ajalinta. Domin zuciyarta wani zafi take yi ga wani abu mai ɗaci da ya tokare mata a ƙirji tun jiya ya kasa wuce miyan bakinta ya daɗe da kafewa sannan bakin nata ya yi ɗaci kamar maɗaciya, sannan ga ciwon kai mai tsanani yunwa take ji amma a bakinta ba ta bukatar cin komai maranta ya cure waje ɗaya da ya haifar ma gangan jikinta rawa, bayan ta idar da sallan ta kura ma waje ɗaya ido tana ma rasa abin da take tunani, yanzu fa wata sabuwar rayuwa ce ta tunkaro ta bayan barin ta gida na wattani takwas a matsayin matar aure yanzu kuma za ta koma gida a matsayin bazawara har da ƙaramin yaron ciki, yanzu a wannan kadamin wa za ta kira? Ina za ta nufa? Rayuwarta ta gama lalacewa ba ta da sauran wani abu na mamora a tare da ita.

Tuna gargaɗin da Habib ya yi mata ajiya ne ya sa ta rarrafa ta ɗauko wayarta dake saman side drower ɗin gadon. Gwara ta bar gidan tun kafin ya fahimci ba ta tafi ba ya yi mata wulaƙanci, agogon wayarta ta duba sai ta ga shidda ne da mintina biyu na safe wataƙila Baffa na masallaci sai ta kira wayar Ammah amma tana ta ringing ba ta ɗauka ba ta kira ta kamar sau uku amma shuru, sai ta mayar da akalan kiran zuwa ga Baffa, domin nan duniya su ne kaɗai ne suka rage ba za su guje ta ba, amma ta rasa komai na ta. zuciyarta na sake yin duhu in ta tuna yadda Habib ya zaunar da ita yana cin zarafin iyayenta da ƴan 'uwanta.

****

*6:13am*

Shidda da mintina sha uku Baffa da Hamma Saddam suka shigo gidan daga masallaci, jiya da yamma Saddam ya dawo daga makaranta can Bauchi. sun gama jarabawa za su yi hutun sati uku kafin su koma.

Ɗakinsa ya wuce shi kuma Baffa ya ƙarisa cikin gida, ɗakinsa ya wuce kai tsaye yana shiga ya iske Ammah na zaune saman darduma da casbaha a hannunta bakinta na motsi, yana takawa zuwa gefen gado wayarsa dake cikin aljihun rigan jikinsa ta ɗau ruruwan kira, bai duba ba sai da ya zauna sannan ya fiddo wayar yana duba sunan mai kiran..

"Auta."

Ya faÉ—a a sarari cikin mamaki, Ammah na lazimi sai da ta kalle shi cikin mamaki.

"Auta kuma! Ummu Salma?

Amma ta faɗa cikin ƙarin mamakin gabanta na faɗuwa, shima ita yake kallo amma sai ya aro jarumta a matsayin shi na namiji.

"Bari na ji Allah ya sa lafiya."

Ya faɗa shima cikin ƙarfin hali, kafin ya ɗaga kiran ma ya katse hannunsa na rawa yana ƙokarin sake kiran ta sai ga kiranta ya sake shigowa da sauri ya ɗaga kiran yana mai kiran sunan ta.

"Auta"

Ya faɗa yana jin bugawar zuciyarsa na ƙaruwa da sauri da sauri.

Ummu Salma daga can bangaren jin muryan Baffa ya sa rauninta ya karu, hawaye ya kece mata mai hade da kuka Baffa sai jin sautin kukan kawai ya yi ta cikin wayar.

"Ummu Salma."

Baffa ya faÉ—a cikin tashin hankali, Ammah na jin yadda ya kira sunanta cikin sauri ya sa ta bar saman darduman ta dawo gefensa ta zauna ta kafe shi da idanuwanta cikin damuwa tana faÉ—in.

"Baffa me ya faru da Auta?
Chapter 41 · 0% Book details