← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 92

Sashe 25

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita ko Ummu a zuciyarta addu'a take yi Allah ya sassauta zuciyar Habib in ya rabu da ita ina za ta saka kanta tana ji gwara su cigaba da zama a haka ta tsira da shi, sannan ta tsira da cikin jikinta da auran ta gabaɗaya tunani take yi zuwa nan gaba kaɗan Habib zai yi nadama zai dawo ya ba ta haƙuri su gyara rayuwan auren su, in shi ba ya son ta ita tana son shi sannan za ta iya jure komai saboda ta tsira da auran shi, shi ya sa ba ta kaunar mganar ta je kunnen Baffa, in ya ji kamar duka yayyenta sun ji, in kuma akwai waɗanda za su yi shuru to akwai fusatattu irin su Hamma Kabiru da Hamma Abdulrahaman da ba su da wasa ko kaɗan tana da tabbacin ko za ta mutu sai sun raba auren ta da Habib, ita kuma tana son shi tana fatan ta rayu da shi har karshen rayuwarta.

Washegari ma BaÉ—É—o ta yi ma Ummu abin da za ta karya kunin gyaÉ—a ta dama mata sai ta yi musu fanke. Habib da BaÉ—É—o sun haÉ—u lokacin da ta fito daga kitchen shi kuma ya yi shirin fita zai bar gida kowa ya yi kamar bai ga kowa ba
Baɗɗo ta kitchen ta ke leƙen Habib har ya bar falon lalle Duniya juyi juyi na gaba ya koma baya yau wai ita ce Habib zai gani ya yi kamar bai gan ta ba, ita fa mamaki ta ke yi yadda lamarin nan ya sauya. A baya ganin irin dacen da Ummu ta yi sai ta ke mafarkin ta samu miji kamar sa, amma yanzu ta ji auren da namijin ma gabaɗaya sun fita kanta, ba su da tabbas ba su da garanti ka aminta da su su ha'in ce ka, ka ba su Amana su ci, sun san salon yaudara kala kala, su kuma ga su ba tukwane ba ne ballanta ka fara ƙwanƙwasa wa kafin ka ɗauka, ba ka isa ka gane manufar su ba sai ka shiga da ga ciki, tana aiki tana hawaye Habib ya cutar da zuciyar Ummu, sannan ya cutar da kuruciyarta suma na tare da ita ya cutar da zukatan su. Damuwarta ɗaya tunanin halin da Ummu za ta shiga matuƙar Habib ya sake ta ko in iyaye suka shiga mganar ba a samu masalaha ba, tana tsoron kar damuwa da zafin zuciya su yi ma Ummu illa. Sai da ta gama shan kukanta ta share hawayenta saboda kar Ummu ta fahimci ta yi kuka itama ta fara ta samu ta yi shuru ta daina kukan da ta kwana tana yi.

Su na gama karyawa Baɗɗo ta wanke abubuwan da suka ɓata ta ɗan gyara mata gidan ta yi wanka ta yi shirin tafiya Ummu ta fara hawaye ita mai idanuwan kuka da cewa Baɗɗo ta ƙara kwana.

"Aa ba zan sa ke kwana ba, kar mijin ki ya zo ya sake ganina, karon mu ba zai yi daÉ—i ba."

Ummu ta na ji tana gani Baɗɗo ta yi mata sallama ta tafi ta bar ta, bayan ta jadadda mata ta kula da kanta ta riƙa samun hutu domin kiyaye dokar likita. Sannan in ta ga wata matsala kar ta zauna ta kira gida in tahowar ba zai yuyu ba Ummu ta amsa da to za ta kiyaye. Baɗɗo na tafiya ta koma ta kwanta tana ta kuka, kukan da ya fara zame mata jiki a acikin kwanaki nan.

Bayan tafiyar Baɗɗo maimakon lamarin Habib ya gyaru sai ma ya sake lalacewa. Ba ya ma nuna cewa akwai wata hallita a gidan, in sau goma Ummu za ta yi masa mgana ba zai amsa ta ba, a cewarsa in ta ga ya dawo yana kula ta sai in har ta bi umarnin sa, umarnin da Ummu ta gwammace su zauna a haka da ta amince da buƙatar sa na zubar da cikin, cikin da duk duniya yanzu ba ta da wanda take so sama da shi. Ba ta san dare nawa ta ɓata tana kuka ba, ba ta san sau nawa ta duka a gaban Habib tana kuka akan cewa ya yi hakuri ya yafe mata. Amma bai kalle ta ba yana nan akan bakan sa, ko ta zubar da ciki ko kuma su cigaba da zama a haka kafin ya yanke hukunci a kanta.

Baya cin abincin ta, ba ya neman ta bai damu da ita ba ko za ta mutu bai damu ba, ba shi da asara sai ya raba dare yake dawowa sannan ya zauna a falo ya yi ta waya cikin harshen turanci. Ummu ta yi kuka, kuka har ya zame mata jiki saboda halin da ta ke ciki. Wato ga ta jahila wacce ba ta jin turanci shi ya sa in zai yi waya sai ya sauya yare, ba kuma wai ba ta jin turancin ba ne, ta na ji daidai misali na iya karatun ta, mayarwan ne ke yi mata wahala ko in an faɗi wasu manyan kalamai a cikin turanci sai ta daburce shi kuma Habib ya iya turanci na fitina kamar wanda aka haifa a ƙasar waje.

Har kuma gobe ba ta ji Fargar jaji ya kamata akan rashin cigaba da karatun ta ba, ra'ayin ta ne kuma har yau ba ta ji ta sauka akan wannan ra'ayin ba.

Kullum sai BaÉ—É—o ta kira ta a waya domin ta ji lafiyan ta. Har Ummin ikki sun yi mgana ta yi mata sannu tun da BaÉ—É—o ta faÉ—a mata ba ta jin daÉ—i. Baffa ma suna waya amma ba su fahimci wani abu ba, tunda ba ta ba da damar haka ba.

**
Zuwan BaÉ—É—o da kwana goma Shamsiya ta zo, kwatsam kamar daga sama domin sun daÉ—e ba su yi mgana da Ummu ba. Sannan ba ta kira ta ba shi ya sa ba ta san da zuwan ta ba sai dai ta gan ta, ashe sun samu hutun makaranta ta dawo gida shekaranjiya ta yi kewarta ne shi yasa ta zo domin ta gan ta.

"Allah sarki Bestie ya makarantan?

Ummu ta faÉ—a tana mai zama a gefen Shamsiya wacce ke zaune a saman kujera mai zaman mutum uku bayan ta kawo mata ruwa.

Shamsiya Black beauty ce, sai dai siririya ce sosai da ba ta da wani tsarin jikin mata, a shekarun ta ba za ta wuce sa'ar Ummu Salma ba.

"Alhamdulillah Bestie, mun gama mun dawo gida hutu muna komawa kuma za mu shiga aji uku."

Shamsiya ta faÉ—a cikin mirmishi, Ummu ta sake rumgumeta tana yi mata fatan alheri.

Shamsiya sai kallon Ummu take yi cikin alamun tambaya yadda ta ga ta koma amma ba ta yi mgana ba.

"Ina Habib? Ko yana wajen aiki ne?

Da kai Ummu ta amsa mata, ba tare da ta yi mgana ba.
Sun fara hira Shamsiya dai ta ga ramar Ummu ta yi yawa sannan lokaci bayan lokaci tana ta shi ta shiga tiolet ta zubda yawu.

"Bestie me ke damun ki ne? Kin rame!

Tana so ta danne yanayin ta amma ta kasa domin damuwar nata ya fara bayyana a saman fuskarta.

"Ko kina da ciki ne?

Shamsiya ta tambaya lokaci É—aya tana washe baki.

Wannan karon ma kai Ummu ta sake ɗaga mata alamun haka ne, da sauri Shamsiya ta rumgume ta cikin tsananin farincikin da ya kasa ɓoyuwa daga zuciyarta ya bayyana har a saman fuskarta.

"Congratulations Bestie na. Mun kusa zama iyaye ni da BaÉ—É—o."

Ba ta sani ba Ummu kuka take yi, sai da ta ji tana shashesheƙa sannan ta ɗago ta sai ta samu fuskarta caɓe-caɓe da hawaye.

"Subhanallah kuka kuma Bestie? Me ya faru?

Shamsiya ta faÉ—a cikin harshen fillanci.

Kasa mgana Ummu ta yi, ban da kuka ba abin da take yi kuka kuma sosai har da sauti. Hankalin Shamsiya ya tashi ta ruÉ—e gabaÉ—aya tana tambayan Ummu abin da ke faruwa. Sai da ta gama shan kukan ta sannan ta iya labarta mata abin da ya faruwa da wanda ke kan faruwa.

Shamsiya ta yi tsam kafin ta ce" Topha, innalillahi shi Habib É—in ne duk ya aikata miki haka Bestie?

Ummu ta jinjina kai kafin ta ce'" Na yi duk abin da zan iya yi na gaza bestie. Ban san sau nawa na duka na ba ma Habib haƙuri ba amma ya ce yana nan akan mganarsa. In ina son mu cigaba da zama kamar baya har sai in na amince na zubar da cikin jikina."

Shamsiya ta kalle ta kafin ta ce" To ki bi umarninsa mana Bestie"
Cikin mamaki Ummu ta kalle ta kafin ta amsa cikin mamaki.
"Na zubar fa kika ce?
"Yes, ai ba matsala ba ce. Wata kila ba yanzu ya shirya ku haihu ba ki bi umarninsa ki zubar Bestie nan gaba za ki samu wani a lokacin da shi ya shirya ma hakan"

Sai Ummu ta yi shuru tana mai kallon Shamsiya sai take ɗan hango ƙamshin gaskiya a kalamanta ganin haka ya sa ta riƙo hannayen Ummu cikin na ta tana cigaba da faɗin.

"Kuma ina tunanin duk mganar da ya faɗa miki na ran shi so ko wani abu cikin fushi ne da haushin ƙin bin umarnin sa ne, amma ina da tabbacin Habib na son ki , ke ma kuma kin san haka"

Kalaman Shamsiya suna shigar ta sai ta ji ta aminta da mganarta amna kuma tana son cikin ta ba ta son rabuwa da shi.

"To amma Bestie ina son cikina fa."

"Allah zai kawo miki wani, kin manta a baya ma kin samu ya zube, yanzu kuma ga shi Allah ya sake baki wani ba? To haka anan gaba zai sake baki wani in sha Allahu.'"

Lamarin ba mai sauƙi ba ne, tana son auran ta, tana son ta yi komai saboda tsira da auren ta amma ba ta jin za ta iya zubar da wannan cikin da ta faro dukkan wata gwagwarmaya saboda shi ba.

"Da na ce zan bi shawaran BaÉ—É—o ne na je gida na sanar ma Baffa watakila in ya shiga mganar komai zai yi daidai ba sai na zubar da cikin ba Bestie."
Chapter 25 · 0% Book details