← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 92

Sashe 84

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BaÉ—É—o ne da Mami suka kwana da ita, can dare Mami ta dawo da abinci da kayan da aka samu aka sauyawa Ummu.
Sai a daran Ummu Salma ta sha tea cikin ta ya warware sannan ta É—an ci abincin kaÉ—an.

Washegari ma yan'uwa suna ta zuwa duba ta, don ma nurses É—in suna hanawa, sai a ranar aka É—an rike Ummu zuwa tiolet É—in Mami ta É—an yi mata wanka amma ba a bari ya taba hannun ba.
Bayan sun fito Baɗɗo ta kama mata suka sanya mata wata doguwar riga mai bubu, ta samu ta rarrafa ta yi rama sallolin da suka suɓuce mata daga zaune.
Wasa wasa sai da Ummu ta yi sati a asibiti sai da ta yi ras suka tabbatar da ba wata matsala sannan suka ba su sallama bayan an cire bandejin hannun ɗinkin ya fara shigewa ciki ya ɗan yi baƙi wajen sun ce ta samu hutu saboda jininta ya hau da kuma lafiyan jaririn jikinta.

Har aka sallameta Mami ne da BaÉ—do ke jinyarta
Ammah ta zo ta duba ta sau daya itama haka ta riƙeta tana kuka tana cewa ta yafe mata Ammah ta ce ba komai amma ta sani in ta kashe kanta saboda Habib ko Shamsiya ta sani ba za ta taɓa yafe mata ba.
Yan'uwan Ammah duk sun zo har su Umma Salamatu.
Bangaren su Baffa Umaru dai Baffa bai faÉ—a musu ba yace kar a tayar musu da hankali.
Hamma Kabiru da Hamma Mustapha sun koma wajen aikinsu tun kafin a sallami Ummu ganin ta samu sauki sosai.

Ummu tana so ta tambayi Hamma LamiÉ—o domin ba ta ganin shi ba tun bayan da ta farka amma ba ta samu hali ba, sai a daran da suka koma gida ta ji Ammah na faÉ—a ma Hamma Jibo a waya da cewa komai na asibitin nan shi ya biya. Ashe baya nan tun washegarin ranar da abin ya faru ya koma Lagos, amma yana kiran Ammah da Baffa yana jin yanayin da ake ciki.

Ummu Salma kunya take ji in aka ba ta waya za a gaisheta sai ta yi ta tunanin shike nan yanzu kowa ya ji labarin ta kusa kashe kanta. Har matar Hamma LamiÉ—o ta kira a wayar Ammah an ba ta sun gaisa, haka ma Hamma Jibo da Adda Nauwara amma ba a fasa zahirin abin da ya faru ga kowa ba.

Hamma Saddam da Hamma Abdulrahim ba a gaya musu ba. Saboda suna nesa ba amfanin yayata maganar tunda lamarin ba mai daÉ—i ba ne.
Ummu ta yi nadama ko da yaushe kuka take yi tana neman gafaran Allah tun ballanta da Baffa ya kirata ya zaunar da ita ya sake tunasar da ita abin da ta manta.
Ya horar da ita hakuri da imani, Ammah kuma faÉ—a ta yi ta yi, domin daman ta ce tun lokacin da ta ji Shamsiya na wannan maganar ta É—ora mata ayar tambaya.
Ta kuma ce in Ummu Salma ta haifu to ta manta da Habib ballanta Shamiya har a gaban Ka'aba ta yi ma Allah kirari da kukan cewa Allah ya saka musu, yadda Habib ya wulakanta su shima Allah ya mayar masa da abin da ya yi musu.

Ita dai Ummu sai kuka ta yi nadama sanadin Habib ta goga ma kanta taɓo, yankan hannunta ko da ya fara warkewa har abada za ta koma ga Allah da wannan tabon a hannunta in ta kalli hannunta sai ta tuna da wannan bakar ranar.

Baɗɗo ta cika ƙawa kuma yar'uwa domin bayan ta yi jinyarta a asibiti da suka dawo gida kullum sai ta zo, makaranta ma daina zuwa ta yi a cewarta karatu kawai suke yi wacce suke tare ke saka mata attendence in za a yi test kuma tana yi mata, Ummu ta riƙe alherin Baɗɗo a cikin zuciyanta, tana fatan nan gaba kafin ta mutu Allah ya ba ta ikon da za ta iya saka ma Baɗɗo da tarin alherukan da ta yi mata.

Ba BaÉ—É—o ba hatta Ummin ikki ba ta zauna ba ita ke zaune da Ammah a gida lokacin Ummu tana asibiti. Ita da zuru'anta ba aminta ba sun zame ma Ammah ahali ita da ya'yanta da Æ´an'uwanta gabaÉ—aya.

Mami dai wannan karon ta ce kafarta kafar Ummu Salma. Za ta ɗauke ta gabadaya daga Jimeta ta koma Kaduna a can kuma za ta haihu. Baffa ma wannan karon bai yi gaddama ba, shima zai so Auta ta ɗan yi nesa da wannan garin na wani dogon lokaci duka yayyenta ma sun amince da haka domin sauya muhalli da jama'a da yanayin iskar gari na kawo kwanciyar hankali. Ummun ma ta aminta daman ko Mamin ba ta ce kafarta kafarta ba ita za ta ce za ta bita domin ta gaji da Jimeta ji take yi gabadaya tana kuntace ne da zaman garin, da Umma Balki ce ta ce za ta tafi da Ummun Mubi Mami ta ce Kaduna za ta tafi da ita har sai da ta ji haushi wai a cewarta ita kanta Mamin yarinya ce ba za ta iya kula da Ummun ba sannan biye mata za ta yi ba za ta yi mata faɗa in ta yi ba daidai ba. Baffa ya yi ta dariya ya na ce ma Umma Balki mai ɗa kamar Lamiɗo ne yarinya? Ta ce E mana ai auran wuri ta yi ta haife shi Lamiɗo ai ɗan yarinya ne. Baffa kamar cikinsa zai kulle Mami dai tana jin ta ba ta saka baki da man tun tana gida kafin ta yi aure a Kaduna in dai Umma Balki ta zo gidan sai sun yi tsiya ba ta gani ta ƙyale.

Baffa ya raba gaddama ya ce Auta ta zabi in da za ta je ita kuma ta ce Kaduna. Umma Balki ta ce Allah ya kiyaye hanya amma ba haka taso ba. Hamma Abdulrahaman ya ce itama dai Umma Balki da rigima nauyi kawai Ummu za ta kara mata, gwara dai Mamin ta tafi da ita can Kaduna zai fi. Haka ko aka yi tuni suka fara shirin tafiya Kaduna kayan Ummu masu dan kyau kaÉ—an Mami ta ce za ta tafi da shi sauran har na wajen Habib ta ce duk Ammah ta aika da su Mubi a kyautar da su in suka je can Kaduna za ta yi mata sabbin É—inkuna. Alhaji Isa ne zai zo da yara ranar asabar in suka kwana lahadi sai su koma gabaÉ—aya tare da Ummun da Mami.

Shi ya sa ranar jumma'a da safe Mami ta É—auketa suka je can asibitin da take awo Hamma Abdullahi ya kai su ta yi musu bayanin za ta tafi da Ummu tana son report na bayananta saboda in sun koma can in za ta fara zuwa sabon asibiti sai ta nuna musu. Abu na kuÉ—i ba daÉ—ewa suka rubuta duka bayanan suka ba ta, wajen sha É—aya suka dawo gidan nan Ammah ke faÉ—a musu Hamma LamiÉ—o ya zo bayan fitan su ba daÉ—ewa sun fita tare da Hamma Abdulrrahman.

Gaban Ummu sai da ya faÉ—i saboda jin sunan LamiÉ—o, in ta tuna da shi sai ta tuna da cewa jininsa na yawo a cikin jinin jikinta sai ta ji wani iri a acikin zuciyanta.

Ita dai ciki ta shige ta É—an cigaba da kimtsa kayanta, ta É—auko tsohuwar wayarta bayan ta cire layin ta karya ta ba ma Ammah tace ta kyautar. Ta sake komawa ciki tana cikin har aka yi azahar Mami na falo suna ta hira da Ammah.
Ta idar da salla kenan ta ji shigowar su gidan ba ta ji dai muryansa ba amma ta san da shi tunda ta ji Ammah na kiran sunan shi
Ba ta aikin komai yanzu tunda dai ba ta fara amfani da hannunta na hagu ba, duk da dai É—inkin ya shige kuma wajen yana warkewa.

Saboda Hamma LamiÉ—o ta ki fitowa ga shi tana jin yunwa ta so ta je ko kitchen ne ta samu abincin tunda Ammah ta gama shinkafa da miya tun É—azu, amma ba ta son kallon Hamma LamiÉ—o kunya take ki shi ya sa ta kasa fita, ta aikata abu yanzu kuma daga baya tana jin matsanacin kunya idan aka danganta ta da abin da ta aikata. Allah ya sa ma ba a yayata lamarin ba iya na gida ne da na jiki jiki na kusa suka san meke faruwa ko can su Baffa Umaru da suka ce sun ji cewa Auta ba lafiya sai Baffa ya ce kawai rashin lafiya ne ta yi, to babu amfanin faÉ—in komai tunda dai ba abin daÉ—i ba ne.

Haka ta naÉ—e yunwarta a cikin É—aki ba wanda ya tuna da ita tana jin hiransu a falo da alama ma abinci suke ci domin tana jin Hamma Abdullahi na cika baki da abinci yana magana yau daga Ammah har Mami sun manta da ita, to ai gwara Mami yau watakila ta sha'afa ne Ammah kuma yau tunda LamiÉ—o ya zo ko Baffa sai ta manta da shi ba ma ita ba.

Tana cikin halin yunwar nan Mami ta shigo yin salla ita ce ta taimake ta, bayan ta idar ta ce mata yunwa take ji sai ta fita da sauri ta je ta zubo mata abinci ta kawo mata sannan ta fita falo ta É—auko mata ruwan gora da ake ajiyewa saman frizan saboda Ummu ba ta shan ruwa mai sanyi ba duka ake sanyawa a firizan ba.

Tana jin Hamma Abdulrrahman na ce ma Mami wai tana shagwaɓa ta, ta kai mata abinci har ɗaki ruwan ma da shi za ta bita.

"Kafafunta ne ke ciwo? Haba Mami."

Amsar da Mami ta bashi ne yasa tana cin abinci sai da ta yi dariya sai da ta kusa ƙwarewa.

"Ina ruwan ka? Nan kuma Ammah ke rawan jiki da ku ban yi magana ba, ta manta da mai juna biyu, nima shine na miƙe na ke kula da ya'ta."
Chapter 84 · 0% Book details