Sashe 65
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gefen shi ta koma ta zauna shi kuma sai da ya kunna wayar sannan ya kai mug ɗin baki ya kurɓi coffea ɗin. Tun safe bai saka ma cikinsa komai ba rabon sa da wani abu tun jiya da daddaren da ya dawo ya sha tea. Barci ya yini yi na gajiya yanzu haka ma yana jin kamar kasusuwan shi suna naɗe tsabar gajiya.
Sama da wata ɗaya shi ke tuƙi saboda zai bar aiki da kamfanin don kar su bar shi ya tafi haka shi ne sai da suka wahalar da shi, yanzu dai ya samu sun karɓi takardan barin shi aiki sun saka hannu shi ne dalilin dawowar shi gida, nan da wattani biyu zai fara aiki da abon kamfani amma yana da sauran hutu kafin ya kama aiki.
Yana kurban tea din yana ɗan duba saƙonnin dake reto a saman wayarsa.
"In ka samu natsuwa ka kira Maimartaba da Fulani sun kirani suna tambayana kai, da cewa ba su same ka a waya ba"
Balkisu ta faÉ—a tana kallon shi. Kamar ba zai yi magana sai kuma ya ce a hankali
"Har su Ammah ban yi magana da su ba."
Sai kuma ya yi shuru ya É—an ka fasali kafin ya cigaba da faÉ—in." Zan kira su, "
Sai kuma ya kalleta kafin ya ɗan kurɓi tea ɗin hannun shi
"Ina so ma na je,"
Ta san bai gama maganarsa ba shi ya sa ba ta katse shi ba.
"Na samu sauyin kamfani. "
Numfashi ya fesar a hankali sannan ya a jiye mug É—in hannunsa a saman teburin gabansa.
"Zan yi hutun 2 month."
Jin ya yi shuru ya sa ta san ya gama magana.
"Ranka ya daÉ—e dogon hutu haka? Har Daura za mu je?
Ta tambaya cikin fara'a.
Kai ya É—an daga mata kafin ya ce" In sha Allahu."
"Har da ni za a yi tafiyar?
Ta tambaya
"In za ki je.".
Shima ya ba ta amsa a yanayin maganarsa.
"In ba za mu daÉ—e ba, zan iya É—aukan excuse a wajen aiki "
Sai ya jinjina mata kai, ta san halin shi zai ce in da takura ta yi zamanta
"Har da su Sultan?
Bai kalleta ba, amma dai ya É—an motsa kan shi alamun e, sai ta fara yi masa bayanin sun koma makaranta, amma dai ba matsala in dai ba za su dade ba
"Sai ki dawo tare da su."
Ya furta daga haka kuma ya tsuke bakin shi.
Ma'ana shi yana can ita za ta iya dawowa da yara.
Tana da murna da jin daÉ—i za su samu tafiya ita da shi da yaran su abin da ba sa samu sai a shekara bai wuce sau É—aya ba.
Duk da ba hira suke yi ba amma tana tare da shi har aka kira mangariba sannan ta kwaso fulas da mug din zuwa kitchen shi kuma ya sauya kaya zuwa jallabiya ya fita masallaci.
Bai dawo ba sai da ya tsaya ya yi isha'i bayan ya shigo ya ɗan bata lokaci a haraba suna gaisawa da su Baban Adila da Jamess, Lamiɗo kowa ya san shi mutum ne mara ƙyamar mutane duk da yanayin shi, da ya shigo falon ma haka su Sabuwa suka yi layi suna gaishe shi kansu a kasa duk ya amsa musu cikin yanayinsa.
Kafin ya dawo Debora ta shirya tebur da abinci sama da kala uku, Balkisu kuma ta sake wanka ta sauya kaya zuwa material doguwar riga.
Tana fitowa ta iske shi a falo tare da su Sultan suna masa hira Beena na hawa jikinsa tana sauka.
Sultan ko faÉ—i yake yi Papa zan sha icream, papa zan ci shawarma Papa sai hira yake yi masa shi dai sai ya yi ta uhm kawai yana É—an mirmishi, Beena kam tana ta wasa da gashin kansa kuma bai hana ta ba.
Balkisu ta kalle su cikin alfahari.
Tare suka yi Dinner jalop rice mai kaza sai kuma mandirice, shi Lamido Jalop din ya ci sai ya sha lemun abarba. Su kuma ita da yaran suka tsakura sauran abincin Beena ma madaran Naan na yara ta sha, Sultan kuma pepe chicken ya ci Bilkisu kum ta ci Mendi rice din da lemu.
Bayan sun gama cin abincin ba daɗewa Anitha ta zo ta tafi da su domin su yi shirin barci gobe makaranta, suma ba daɗewa suka shige ciki. Debora kuma ta zo ta kwashe komai na saman dining ɗin zuwa kitchen, abincin gabaɗaya ake dafawa su ɗiba na su da na su James ba shamaki, sannan Balkisu ba ta son a gama cin abinci a bar shi a wajen shi ya sa da sun gama take yin saurin kwashe komai zuwa kitchen.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L6zUax648eTERbvw8Bqyie?mode=gi_t
*16*
*Zone ,3. Jimeta*
BAYAN SATI ÆŠAYA.
Ummu Salma na zaune a tsakar gida a saman kujera yar tsugunno da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safiyar ranar talata.
Farin wake ne a cikin wani farantin silba tana gyarawa Ammah kuma na daga cikin kitchen tana É—ora sanwa amma jefi-jefi tana yi ma Ummu hira wacce ta yi shuru kamar ruwa ya cinye ta. Ammah ce ke ta maganarta ita kaÉ—ai. Baffa baya nan tun jiya suka tafi ibadan shi da Hamma Abdullahi.
Gidan sai ya rage daga Ammah sai Ummu Salma, Saddam ma ya koma makaranta shekaranjiya.
Gajiya da kwanciya ya sa take ɗan fitowa tsakar gida ko za ta samu abin da za ta iya taimaka ma Ammah da shi amma ba ta barinta ta yi komai sai ta ce ai Likita ya bata hutu, ita kuma ta bata tabbacin ta warke, jiya ne ma Hamma Abdurrahaman ya zo ya ji suna wannan takaddaman, shi ya yi ma Ammah magana ya ce aikin da za ta yi daga zaune ta riƙa bata saboda ta riƙa ɗan motsa jikinta hakan ma lafiya ce ga abin da ke cikinta shi ya sa yau ɗin Ammah har ta amince ta bata wake ta ce ta gyara mata.
"Saura fa kwana biyu zuwan su LamiÉ—o Auta, daga yau sai gobe jibi ne ya ce mini za su taho."
Ummu ta yi shuru hankalinta na kan waken da take gyarawa amma kuma hankalinta da tunanin ba ya wajen ta tafi duniyar tunanin rayuwarta.
Yau wajen kwana uku kenan Ammah ta kasa zaune ta kasa tsaye murnanta ya kasa ɓoyuwa tunda Hamma Lamiɗo ya kira ta ya ce za su zo shi da matarsa da yara ranar al'amis kuma za su ɗan kwana biyu ta kasa sukuni tun jiya ta tura matan su Hamma Abdullahi su Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim suka je gidan shi dake anguwan Jambutu Haske suka gyara suka yi share-share. Sannan yau da safen nan ta ji Ammah na waya da Hamma Abdullahi tana tunasar da shi Hamma Lamiɗo ya ce ya ɗauki motarsa ya kai ta wanki sannan a ɗan duba ta tunda ta yi wattani a ajiye ba a hauta ba, tana can gidan lullube a cikin tamfol.
Alhalin ba Ammah ya bama saƙo ba da kan shi ya kira Hamma Abdullahin ya faɗa masa, shi ma jiya ne kafin su wuce da Baffa yake mata maganar shi ne yau ta kira shi tana sake tunasar da shi har da cewa in ba za su dawo ba ne ya kira Abdularrahaman shi ya je ya ɗau motar ita dai maganarta kar shalelenta ya iso garin nan ba a yi masa abin da yake so ba.
"Da man Kabiru ya faÉ—a mini zuwan nan da ya yi kwanaki LamiÉ—o ya samu sauyin wajen aiki yanzu zai dinga samun hutun sosai tunda ya sauya wajen aiki."
Ammah ta sake faÉ—a tana daga cikin kitchen.
Ummu Salma dai na jin ta amma har a lokacin ba ta yi magana ba, tunani take yi in da ace tana da in da za ta je ta ɓoye ma ganin Hamma Lamiɗo da matarsa za ta je, har sai sun tafi sannan ta dawo, tana jin kunya da nauyin su zo su ganta a haka, su ga yadda rayuwarta ta dawo baya, yanzu kunyar mutane take ji da Ammah tayi baƙi ko tana falo za ta shige ciki tana jin nauyin haɗa idanuwana da Jama'a ko yayyenta kunyar haɗa idanuwana take yi da su, tana ganin kamar ita ba ta da sa'ar rayuwa ta tafi gidan aure amma ga shi ta dawo musu ba ma ita kaɗai ba tare da nauyin cikin jikinta. Duk da Ammah ta ce ba ta faɗa masa ba amma in ya zo ya gan ta ko bai ta tambaya ba Ammah za ta iya faɗa masa dalilin zamanta a gida tunda shi tambaya ba ɗabi'ansa ba ne ko zai shekara yana ganinta ba zai damu da ya tambayi dalilin zamanta ba.
Ta yi nisa cikin tunanin ta ba ta ma san Ammah ta fito tana yi mata magana ba, sai da ta ji ta taɓa ta sannan ta yi firgigit ta dawo hayyacinta.
"Ammah kina magana ne?
Ta faɗa tana kallonta lokaci daya tana koƙarin shanye hawayen da suka cika mata kwarmin idanuwanta.
"Auta"
Ammah ta kira ta, sai ta sunkunyar da kanta tana jin kamar ta kace da kuka.
"Ba an hana ki shiga zurfin tunani ba, sai yaushe ne za ki saduda ki fahimci duk abin da Ubangiji ya yi daidai ne? Sai yaushe za ki dogara da Allah ki san cewa Habibu ya shuÉ—e daga rayuwarki Ummu Salma.?
Ammah ta gama faɗa tana tsaye tana kallon Ummu wacce har ta fara tsiyayan hawaye a saman ƙuncinta
"Wallahi in na ga kina kuka da damuwa kan wannan yaron haushinki na ke ji, bai ma kamata kina yi masa kuka ba, an san da damuwa amma haƙuri ake yi tunda damuwa da kukan ba zai sauya komai ba. To gwara a yi hakurin yafi alheri in kika yi hakuri wata rana za ki ci riban haƙurin ki Auta."