Sashe 52
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abin da ma yasa ya saurin duba saƙon a group ɗin sai a yi wata uku ba wanda ya yi ko sallama a ciki kwata-kwata group ɗin ba ya active kuma duk suna ciki hatta da Hamma Lamiɗo, kuma shi da kan shi ya buɗe group ɗin shekaru biyu da suka gabata ya sanya masa suna AMMAH AND BAFFA HAPPINESS. su takwas ɗin su cur ƴa'ƴan Ammah da Baffa suna ciki da Hamma Lamiɗo cikon na tara domin ba wanda ya isa ya cire shi a cikin jerin ƴa'yan Amma da Baffa.
Ba su fita ba amma ba mai magana farko farkon ma buɗewa Saddam na raya group ɗin da ɗan turo jumma'at mubarak, ko irin short-short vedio haka na ban dariya kawai ranar Hamma Kabiru ya fito ya yi Viocenote na kusan sakwan hamsin a ciki yana yi ma Saddam faɗa da jan kunnen cewa daman ya buɗe group ɗin ne ya tara su domin ya riƙa turo musu Vedios ɗin ban dariya! Hala yara ne su irin shi ko marasa aikin yi kamarsa! To in dai abin da ya sa ya buɗe group ɗin kenan gwara ya gaggauta cire su ya rufe group ɗin su suna da abin yi.
Wannan maganar ta ɗan muzanta Saddam ya ji zafi, tun ballanta yadda Ummu Salma ta kira shi tana masa dariya da ya so ya cire kowa ya rufe group ɗin ne amma sai bai yi haka ba da Hamma Jibo ya kira shi ya lallasheshi da cewa ya san halin Hamma Kabiru da gwasala ya ƙyale shi kawai. Dalilin da ya sa bai rufe ba kenan amma ya kama kan shi, bai sake tura komai a ciki ba, ko addu'an jumma'at mubarak ya daina turawa kuma ba wanda ya yi cigiyarsa tun daga ranar ya san ba su damu da turowan nashi da rashin shi ba, tun daga lokacin sai group ɗin ya yi wata sama da uku ko sallama ba wanda ya yi wasu ma mantawa suke yi da shi, akwai ma waɗanda ba su taɓa magana ba irin su Hamma Lamiɗo, shi wataƙila ma ba lalle ya san an buɗe ba mutumin da sai ka yi masa mgana a chart sai ya yi sama da sati biyu yake dubawa ba kuma lalle ne in ya duba ya baka amsa a lokacin ba sai a lokacin da ya samu dama.
Hamma Jibo ne daman ko Hamma Mustapha kan ɗan sanar da wani ƙaruwa ko jaje in ya samu ɗaya daga cikin su, suma ɗin suna dai yi ne kawai saƙon da sai su tura ya yi sama da sati ba wanda ya nuna ma ya gani ballanta ya tanka alhalin akwai waɗanda suka gani ɗin amma su yi magana suna ganin ɓata lokaci ne.
Shi ya sa yau yana ganin saƙon ya shiga da sauri sai ya ciro karo da labarin da ya razana shi.
"To wai me ta yi masa ya yi mata wannan sakin a lokaci É—aya?
Ya faÉ—a saboda mamaki shi abin yake ba shi.
Ummin ikki ce ke bashi labarin yadda lamarin ya fara har zuwa yau Ammah ba ta yi maagaana.
"Kai innalillahi."
Ya faÉ—a yana mai zaro ido.
"Wallahi ai yaron nan ya gama cutar mu."
Hamma Saddam ya yi shuru kafin ya ce" Ni gabaÉ—aya ma na rasa abin cewa. Kamar ba zaai aikata ba sumu sumu da shi munafuki.".
Shuru ba wanda ya tanka shi.
"To yanzu ina ita Ummun?
"Tana cikin É—akin ta."
Ummin ikki ta faÉ—a tana nuna masa É—akin da hannunta da sauri ya wuce ya shiga a bakin kofa ya tsaya yana kallon Ummu na zaune kawai tana kallon waje É—aya.
BaÉ—É—o na gefenta ta yi tagumi É—akin shuru ba ka jin motsin kowa kamar an yi mutuwa.
Sai jikinsa ya sake yin sanyi jiki a sanyaye ya ƙariso ɗakin.
"BaÉ—É—o."
Ya kira sunan ta cikin sanyin murya. Kallon shi ta yi kafin ta amsa itama a sanyaye.
"Naam Hamma Saddam yanzu ka dawo?
"Tun jiya fa na dawo"
Ya bata amsa yana kallon Ummu da ya ga ba ta ko motsi
"Ta ƙame ne?
Ya faÉ—a yana É—an ware ido.
"Ko ta suma ne a zaune?
Ya sake faÉ—a yana É—an yawo da hannunsa a wajen idanuwanta sai ya ga ta É—an kifta ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Ummu sorry amma don Allah ki daina damuwa kin ji ko?
Shege mara mutumci kawai "
Ya faÉ—a yana kallon ta, kallon shi ta yi da luhu luhun idanuwanta na wani lokaci kafin ta É—auke ba tare da ta yi magana ba
"Ummu"
Shuru ba ta amsa shi ba ya saka hannu ya dafa kafaÉ—anta nan ma ba ta sake kallon shi ba, BaÉ—É—o ya kalla cikin mamaki da sauri ta ce" Tunda muka je muka É—aukota haka take ba ta yi kuma magana ba."
Hamma Saddam ya ware ido kafin ya ce" Kar fa shock ya kamata zuciyarta ta buga ba a sani ba."
Baɗɗo ta yi shuru tana kallon shi, hannun Ummu ya kama ya riƙe yana kallon ta.
"Ke Ummu kina jina?
Ya faɗa lokaci ɗaya yana saka ɗayan hannunsa ya ɗan taɓa kumatunta sai ta runtse idanuwanta na wani lokaci kafin ta buɗe sai ga hawaye sharr, ajiyar zuciya ya saki kafin ya ce" Gwara dai a dinga ganin alamu zuciyarta na tafiya."
Ya faÉ—a yana share mata hawaye da gefen jallabiyan jikinsa
"Ki daina kuka kin ji, a matsayina na yayanki sai na rama miki abin da ya yi miki."
Yake faÉ—a yana sake share mata hawaye.
"Shi ne zai ce ba ya son ki? Kaf duniyan nan akwai wacce ta kai ki kyau ne da zati?
Sai da ta kalle shi, hawaye suka sake kwaranyo mata. Duk da kyan da zatin shi Habib ba shi yake so ba jikinta yake so kuma tunda ya gama amfana shi ya sa ya yada ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda kamar yadda ya faɗa sannan ya jaddada mata.
"Wallahi sai mun rama miki. Mugu kawai."
Ya sake faÉ—a yana kallon ta yana yi ne domin ta ji sanyi a zuciyarta bai san a lokacin ma jin wani irin zafi take yi yana ta so mata ba ta so ana zagin shi domin har yanzu tana jin soyayyarsa a cikin zuciyarta
"Ta ci abinci?
Ya faÉ—a yana kallon kulan abincin dake gefe.
Da kai BaÉ—É—o ta amsa masa da Aa ba ta ci ba
"To ya za a yi ta zauna da yunwa"
Ya faÉ—a yana jawo abincin.
"Ta ƙi ci Ummi har tea ta haɗo mata ta zauna tana lallashin ta amma ba ta karɓa ba. Ga shi kuma ina jin tun jiya ba ta ci komai ba."
Ta faÉ—a hawaye suna kawo mata, Hamma Saddam ya kalle ta kafin ya ce" To ke ma kina kuka ita wa zai lallashe ta?
"Wallahi ina tausayin Ummu. Ina tausayin halin da za ta shiga."
BaÉ—É—o ta faÉ—a tana kecewa da kuka, shi ma ba domin yana namiji da shima ya kece da kukan tausayin Ummu amma shi namiji ne ya kamata ya daure.
"To ki yi haƙuri ki daina kuka. Ke za ki zama ƙarfin gwiwanta."
Shuru ta yi tana cigaba da kukanta mai sauti yayin da na Ummu sai dai kawai zuɓar ƙwalla.
"Ummu ya kamata ki ci wani abu."
Ya faÉ—a yana kallon ta, sai ta kalle shi amma ba ta yi magana ba.
"In haÉ—o miki tea É—in?
Shuru ta yi masa amma tana kallon shi.
"Kina da juna biyu Ummu kar wani abu ya same ki"
Ya faÉ—a yana sake kallon ta.
Sai ta lumshe ido hawaye na kwanranyo mata.
"Na kawo miki tea É—in?
Karo na farko ta girgiza masa kai.
"Me ya sa Ummu? Za ki zauna ki mutu da yunwa ne. Mai faruwa fa ta faru sai dai mu yi haƙuri kawai.".
Ya faɗa cikin sigan lallashi duk dai ta samu ta jiƙa maƙoshin ta.
"Na kawo miki?
Ya faÉ—a cikin sanyin murya.
Sai ta sake girgiza masa kai a karo na biyu.
"Haba mana Ummu."
Ya faɗa yana miƙewa tsaye.
"Bari na je na haÉ—o miki, ki sha ko kaÉ—an ne."
Yana shirin barin É—akin a karon farko Ummu ta yi magana.
"Ba z.. zan sha ba."
Ta faÉ—a cikin dashewar murya.
"Ko kaÉ—an ki sha Ummu"
BaÉ—É—o ta faÉ—a tana kallon ta.
"E ko kaÉ—an kin ji?
Hamma Saddam ya sake faÉ—a domin a yadda bakin ta ya bushe ya tabbata ma cikin ta a bushe yake.
"Na ce ba zan sha ba. Ba zan sha ba don Allah ku ƙyale ni."
Ta faÉ—a lokaci É—aya tana kecewa da wani irin kukan, muryanta ma baya fita sosai.
"Zan mutu, ina ji kamar zan mutu zuciyata ke zafi ciwo take yi.."
Haka ta faÉ—a tana nuna saitin zuciyarta cikin kuka.
"Zuciyata na zafi, ji nake yi kamar na kashe kaina."
Ta faɗa cikin kuka kafin ta fara buga saitin zuciyanta da hannu tana wani irin kuka da gudu Baɗɗo da Hamma Saddam suka yi kanta suna riƙe ta amma kamar an ƙara mata karfi tana fizge kanta tana kuka tana faɗin su bari ta kashe kanta, hayaniyarsu ya kawo su Ammah ɗakin ganin abin da ke faruwa ya sa ke raunana Ummin ikki ta fara kuka ita kuma Ammah ta fita tsakar gida da sauri domin ta kira Baffa sai suka ci karo da juna
"Me ke faruwa ne! Na ji kuka?
Ya faÉ—a cikin tashin hankali.
"Ummu ce ke kuka tana faÉ—in za ta kashe kanta."
Ammah ta faÉ—a cikin rawan murya.
"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."
Ya faɗa da gudu yana faɗawa falon Ammah. Daidai lokacin da Hamma Abdulrrahman ya shigo tsakar gidan da sallama. Lokacin da ya ga saƙon Hamma Jibo fitowar shi kenan daga wata sharia da ya jagoranta. Shi da man ya san sai an zo wannan matakin.
"Ammah"
Ya kira sunanta ganin ta cikin wani yanayi.
Tana ganin shi ta nufe shi da sauri.
"Abdulrrahman."
"Ammah"
Ya amsa yana kallon ta cikin mamakin ganin yanayin ta.
"Ummu Salma ce."
Ido kawai ya sakar mata yana kallon ta.
"Tana ciki tana kuka wai za ta kashe kan ta."
"Za ta kashe kanta?
Ya maimaita cikin mamaki.
Sai Ammah ta gyaÉ—a masa kai, goshinta har yana tara zufa saboda damuwa da firgici.