← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 92

Sashe 12

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wai saboda Lamiɗo! Waye wani Lamiɗo! A lokacin da ya ke zanin goyo da jinin haihuwa a jikinshi da ba a samu damar wanke shi ba, mahaifiyar shi ba ta duba Lamiɗon a lokacin ba, ba ta duba shi ba ta saka ya yi ma rayuwarta mummuman taɓon da har ta koma ga Allah ba za ta taɓa mantawa ba. Shi kuma ya aiwatar da Umarnin mahaifiyarsa saboda kare martaban masarautar su me ta aika ta? Wani laifi ta aikata da za a sake ta a lokacin da zufan naguda bai gama safka daga jikinta ba? Saboda ita ba yar masu kuɗi ba ce, saboda ita ubanta ba sarki ba ne, tuna haka kawai in ta yi sai ta ji yanayin ta cikin kuka, yanzu ma hawaye ne suka kece mata, shi ya sa har abada ta tsani duk wani abu da ya shafi Sarauta daga kowani bangare ne, abin da ta sani su ɗin masu son kan su ne marasa adalci abin da suka yi mata ya munin da har abada ba ta fatan kafarta ta sake takawa Daura, tun bayan fitar ta ɗauke da jinin haihuwar dake jikinta ta yi alƙawarin ita da wannan garin har abada.

Duk da ko da har gobe akwai dangin mahaifiyarsu a garin ba ta taɓa jin marmarin sake saka kafarta a cikin sa ba, domin a cikin sa ta samu farinciki amma kuma ya gurɓata da baƙincikin rayuwarta duk farincikin da rayuwarta da ta ke ciki yanzu da ta tuna da rayuwarta ta baya sai ta ji komai na duniya ya yi mata ƙunci. In tana tuna wahalar da ta sha, deperession ne ya nemi kama ta, Allah ya saka ma Baffa da Ammah da alheri sune suka zama silar da ta zama Fatima a yau, in ta kalli rayuwarta yanzu sai ta ji ba za ta iya saka ma Baffa da Ammah ba domin sun yi mata komai anan duniya.

Ammah kuma ita ce ta sakar ma É—an ta, ita ce ta yi wahala da shi, shi ya sa nan duniya kowa ya shaida LamiÉ—o ba shi da wata uwa sama da Ammah itama ta shaida haka, yadda ta wahala da Kabiru haka ta wahala da LamiÉ—o, kawai ita mahaifiyarsa ce a haihuwa, Ammah kuma uwa ce a gare shi da ta sadaukar da duka rayuwanta wajen kula da shi.

Hawayenta take sharewa, tana jin sanyi a cikin ranta tunda tun a duniya Fulani ta ga sakamakon ta, domin sai da ta zo ta roƙe ta gafara akan abin da ta yi mata sannan ɗan da ta guda tun yana cikin jinin haihuwa shine Sanyin idaniyar masauratar Dauran da suke taƙama da shi, ko a haka aka tsaya sun ga sakamako mai kyau, su ƴa'ƴan sarakunan da ta aura masa ba su iya ba ta abin da take so ba, dole dai sai ita ita ɗin da ba ƴar kowa ba ita ce ta sama mata abin da take muradi, to a haka aka tsaya ita Fatima ta yi nasara.

Tissue ta zaro daga cikin motarta ta goge fuskarta a fili ta furta" Allah ya jiƙan ka da Rahama Abba. Marigayi tsohon Sarkin Daura Muhammad Shitu Daura."
Tana tuna yadda ya ƙauna ce ta wata ƙila da yana raye da an yi mata adalci. Shi ne ya ce in ta haifi namiji sunan yaro Muhammad Lamiɗo in mace ce kuma Ummu-Kursum shi ya sa lokacin da ta iso Jimeta ta ce ma Baffa ya yi ma jaririn huɗuba da Muhammad Lamiɗo, ko ba ya raye za ta saka masa da ƙaunar da ya nuna mata wajen cika wasiyyarsa.

Ita ce za ta ba da labarin mutuwa mai tonon asiri domin mutuwa ce ta yi sanadiyar tonuwar asirinta, ta yi sillar gurbata rayuwar farincikinta zuwa baƙin ciki, ta wani bangaren kuma hakan ya yi sillar sauya rayuwarta daga wannan Fatimar yar mubi bafullatan ƙauye mara ilimi zuwa wata Fatima ta dabam da ta samu cigaban rayuwa ta ƙo'ina. Tabbas ta wannan bangaren za ta gode musu domin sun ma yar da rayuwarta yadda ba taɓa tunanin komawa ba.

Kimtsa kanta ta yi, gilashinta ta fiddo a cikin jaka ta saka saboda kauda idanuwan mutane a kanta bayan ta duba madubin motar ta ga idanuwanta sun yi jajir, sannan ta ɗau jakarta ta fito daga cikin motar ta yi amfani da key ɗin ta rufe motar. Tana fara takawa zuwa office ɗin ta daliɓan da take ɗauka yan level 1 suna ta gaishe ta ita kuma tana amsawa cikin sakewa daliɓai suna son ta saboda tana da sauƙin kai da taimako har malaman ma sun san Dr Fatima Baba wajen karamci da kyautatama duk wanda take tare da shi.

****

Su Ammah sai da suka yi kwana goma sha ɗaya sannan suka dawo, washegari Ummu-Salma ta je yi mata sannu da dawowa. Ta iske kayan biki niƙi-niƙi ga su nan a ɗakin Ammah har da bag da aka raba mai ƙaton hoton Amarya a ciki ake saka atamfa mai kyau da mayafi har da turaruka, ga kayan su fulawa tun da ta zo Ammah ke ba ta labarin abin da ya faru a wajen bikin nan, Hamma Sadam ma ba a bar shi a baya ba shima yana ɗorawa da na shi, su Ammah fa kaya suka dawo da shi niƙi niƙi ita da Ummin ikki, bayan kala ukun da aka yi musu Fulani ta ba su turame goma da dubu 200k Maimartaba Sarki ya ba su naira dubu 500k tukwaici Gimbiya Shahida ma da turamen zannuwa 20 da kuɗi har shaddodi aka ba da aka wo ma Baffa sun je ɗaurin auran amma tare da Hamma Abdullahi, Hamma Abdulrahaman bai samu zuwa ba, shi kan shi Hamma Sadam shaddoji sun fi kala biyar sabbi gezner masu tsada da takalma haɗe da hulana da ya dawo da su, cikin jin daɗi suke ba da labarin zuwan su Daura da man haka ne in dai Ammah ta je to haka za a rako ta da kayan arziƙi niƙi-niki Ammah kuma ta shiga rabo gidajen yan'uwa da Dangi, har can Mubi saƙon na iske musu. Ta ciccire ma su Umma Balki na su kason, da matan su Baffa Umaru.

Duk da ba ta samu zuwa ba tare da na Umma Salamatu da Umman A'i, Hamma Sadam ne zai je ya kai musu gobe, jibi zai koma makaranta.
Sannan ta ɗibar ma matan su Hamma Abdullahi, ita dai Adda Nauwara an ba ta na ta acan, amma na su Hamma Kabiru da Mustapha Amma ta ajiye musu abin biki, ita kanta Ummu da ta je an ba ta jaka da kayan fulawa sai turare. Sannan ta karɓan ma Baɗɗo itama.

"Amma na Bestie fa?

Amma ta ce za ta ijiye mata in ta zo da kanta sai ta ba ta.

Ummu tura baki ta yi kafin ta ce" Amma ni zan ci ne? Zan ajiye mata ne tana can makaranta sun kusa farawa jarabawa."

Amma ta ce Allah ya sa a yi cikin sa'a amma ba za ta ba yar ba.

"To na Noori na Ammah."

Ummu ta faÉ—a, Amma ta yi mata wani kallo kafin ta ce" Waye kuma haka?
Ummu na dariya ta ce" Kai Amma Habib É—in ne ba ki san sunan shi Noori ba?
Ammah ta aika mata da daƙuwa kafin ta ce" ƙaniyar ki Ummu Salma."
Sai ta fara dariya ƙarshen ta dai sai da Amma ta ba da nashi shima tana cewa" Ya kira ni ina can ya gaishe ni, ya cancanci ya samu tsaraban Daura."

Saboda tana so ta tsokani Ammah ya sa ta sake cewa " Amma to ina na Mami na? Na ga ba ki cire mata ba ne"
Wannan karon sai da aka wurgeta da mafici sannan aka ce" Mamiyo, in tana son tsaraban me ya hana ta je da kanta? Uwar nan taki zuciyarta ba ta da kyau ko a waya ba ta kira ni ba, nima ko na ce ba zan kira ta ba ina nan za ta zo ta same ni."

Ummu ta gyara zama tana faÉ—in" Ammah to suma sauran da kika ba su ai ba su je ba."
Ta gama faÉ—a tana tura baki.
Amma ta miƙe ta fice tana faɗin" Ba zan ba yar ba, na ƙarfi ne ki ƙwatan mata mai uwa."
Ta fita ta bar Ummu na dariya da man ta san ba za ta ajiye mata ba amma ta yi son kai za ta aika da shi Mubi, ita Mami ko oho.

Ummu har dare tana gidan, labari kam sai da ta gaji da shi, Hamma LamiÉ—o dai bai zo ba wai yana cikin aiki, matar shi ce dai ta samu zuwa da yaran shi itama Ammah ta ce ana gama biki daga Abuja ta hau jirgi ta koma Lagos saboda aikinta.

Da man Baffa baya nan ko da Ammah ta dawo ya je kwatano
Habib ya zo ya ɗauki Ummu da yamma, daga nan suka ƙarisa gidan iyayen shi dake anguwar Doubeli, Baban Habib ya tsufa yana zaune ma ba ya iya tafiya mahaifiyar Habib ce ta rasu, amma akwai sauran mata uku a cikin gida. Suna da yawa wasu duk sun yi aure mata da mazan wasu kuma yanzu suke tasowa. Da ya ke lokacin da aka yi ma Ummu buɗar kai(Fansa) akwai sunan da suka sanya mata bisa al'ada Tafisu da shi duka ahalin Habib suke kiranta da shi, shi ya sa in dai ta shiga cikin su ba sunan ta Ummu Salma ba, sunan ta Tafisu nan suka yi dare sai wajen tara na dare suka koma gida.
Chapter 12 · 0% Book details