Sashe 31
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Habibu kuma bai san abin da ke faruwa ba kiran Alhaji Shariff kawai ya samu da cewa ya zo gida yana son ganin shi, a ranar ya je bayan ya taso daga wajen aiki ya ji mamakin jin maganar cikin Ummu a bakin shi, faÉ—a ya yi masa kaca kaca da cewa bai isa ya sa a zubar da cikin ba. Tunda ya bari aka samu cikin sai an haife shi
Kuma kar ya sake jin wata magana nan da nan Habib ya ce shi bai tilasta mata sai ta zubar da ciki ba. Shi kuma Baffa Umaru ya ce Habib ɗin ya turtusa ma Ummu akan ta zubar da ciki, jin haka ya sa Alhaji Sheriff ya kira Baffa Umaru ya ce ya zo garin su haɗu a gidan Baffa tare da su Habibun a yi magana gabaɗaya.
Â
Shi kuma ya bashi tabbacin, zai zo cikin satin in sha Allahu.
Habibu dai ya san matsayar mganar tun da Alhaji Sheriff ya faÉ—a masa ga matsayar da aka tsaya. Ita dai Ummu ce ba ta sani ba sai ana gobe zaman Baffa ya kira ta a waya ya faÉ—a mata ba domin shi ba da ba za ta sani ba. Tunda Habib ba ya magana da ita ballanta ya sanar da ita.
Kuma adaran ta fito shan ruwa suka haÉ—e da Habib ya fito daga tiolet tana ganin shi sai da gaban ta ya faÉ—i tunda yanzu ganin sa ba alheri ba ne a wajen ta.
Ta yi saurin faÉ—awa Kitchen tana sauke numfashi, ta É—an jima kafin ta fito bayan ta sha ruwan sai dai me tana fitowa ta ga Habib na zaune a falon abin da ya daina yi tun bayan lalacewar zaman su, sun haÉ—a ido ya yi mata wani kallo gabanta na faÉ—uwa ta dukar da kai za ta wuce ta ji maganar sa a sama.
"In da kike tunanin kin kaini da niyar na fasa ƙudirina to kin yi kuskure domin nan duniya ba wanda ya isa ya sauya mini ra'ayi na "
Ummu ta É—ago tana kallon shi cikin mamakin kalaman shi..
Ido ya zare mata sannan ya gyaÉ—a mata kai alamun tabbatarwa.
"Haka na faÉ—a, saboda haka kin yi kuskure kuma sai kin yi nadama."
Yana gama faÉ—in haka ya yi tsaki, ba domin ta matsa ba da ya ture ta, in kuma ta faÉ—i ba shi da asara. Da kallo ta bishi na tsantsan mamaki da al'ajabin maganganunsa yana nufin iyayen ta da iyayen shi, ba su isa da shi ba kenan.
Ta tabbata Habib da gaske yake yi tun tana tunanin lamarin shi wasa ne har dai ta amince da cewa Habib ya sauya duk abin da ya faÉ—a akan ta gaskiya ne tunda ga shi nan yana aikatawa a aikace.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t
*08*
Asabar.
*8:30am*
Washegari ta kama asabar ɗin karshen mako ne, tun ƙarfe takwas da rabi na safe Alhaji Sheriff ya kira Habib da umarnin ya zo gida yanzu-yanzu yana son ganin shi, yana barci ne ma ya tashe shi haka nan yana tura baki da ƙunƙuni ko wanka bai tsaya yi ba ya sauya kaya ya fita.
A tunanin shi ma ko ya kira shi daga can su wuce gidan su Ummu Salma ne, sai kuma ya ji akasin haka. Domin É—aki Baffan na shi ya saka shi yana ta yi masa faÉ—a da jan kunne.
"An juma za mu haɗu acan gidan su iyalin naka. Habibu kai da kanka ka zo ka same ni cikin girma da arziƙi, ka ce kun daidaita da wannan yarinya mu je a nema maka auran ta, ga shi iyayenta masu mutumci da dattako ne. Ba za ka dawo daga baya ka kunyata kanka sannan mu ma iyayenka ka kunya tamu ba, don Allah in mun je ka ba ma iyayenta haƙuri maganar ciki kuma tunda har ka ɗiga shi to sai dai ka yi haƙuri bayan ya fito duniya daga baya in har kun gama daidaitawa da matarka to wannan ruwan ku ne, ku tsayar da haihuwa har na tsawon shekarun da kuke so ba ruwan mu a aciki. Amma yanzu maganar zubar da ciki ka janye ta Habibu."
Shuru kawai ya yi yana sauraran shi, amma ba ya jin zai iya aikata abin da ya ke so bai shirya ba. Ko ma ya shirya to ba da Ummu ba amma sanin ko ya zauna yana yi ma Baffan na shi bayani ba zai gane ba shi ya sa kawai ya yi musu shuru, sai dai maganar zubar da ciki ba gudu ba ja da baya.
"To Abba in sha Allahu"
Haka Habib ya faÉ—a ba wai domin ya saduda ba yana nan akan bakan shi.
"Allah ya yi maka albarka."
Ya amsa da amin kansa na ƙasa.
"Abba ko za ka shirya ne sai mu je daga nan?
Habib ya tambaya nan take ya ce masa aa ya koma gida ya ɗau matarsa su haɗu acan ƙarfe goma ne kar su makara. Habib ba haka ya so ba domin shi ba ya ƙaunar ma Ummu Salma ta sake zama a kusa da shi, yadda ba ya son ta haka ya tsani ya gan ta a kusa da shi amma saboda kar ya yi masa gaddama a yanzu anan gaba ya ƙi yi masa amfanin da yake so shi ya sa ya amsa masa da to.
Yana fita daga gidan ƙanin mahaifin na sa, ya shiga mota ya bar anguwa yana hanya ya ɗau waya ya lalubo lambar wayar Ummu Salma da tuni ya daɗe da blooking ɗin ta shi ya sa ko ta kira shi ba ta samun shi, wayar tana ta ringing gabda za ta yanke ta ɗauka murya a cunkushe ta yi masa sallama da mamaki a muryanta na dalilin me ya sa Habib ya kira ta kuma yau?
"Kar ki fita ki jira ni gani nan zuwa."
Haka kawai ya faɗa lokaci ɗaya ya yanke kiran yana mai sakin tsaki shi kaɗai, ba domin yana da wata manufa anan gaba ba, da ba wanda ya isa ya saka shi zuwa gidan su Ummu shi fa ya daɗe da gamawa da ita, sai dai in ya yi gaddama nan gaba ƙwaɓarsa za ta iya yin ruwa shi ya sa yake bi a hankali a yanzu.
***
Kiran da Habib ya yi mata a waya ya ɗaure mata kai. Yaushe rabon da ya kira ta a waya har ta manta. Da man tana ɗan share falon ne ganin ya yi ƙura ta ɗan jima ba ta share ba tana fama da kanta ta ji ana kiran wayarta a ciki tana zuwa ta ga shi ne, tunda ya ce ta jira shi gabanta ya yanke ya faɗi ta kasa sukuni domin ba ta san da abin da zai zo da shi ba.
A haka ta gama sharan ta yi wanka tana cikin shiryawa ya shigo gidan bai neme ta ba ya shiga ciki sama da mintina talatin ya fito sannan tana jin ya sake fita amma bai neme ta ba, tana zaune gefen gado ta yi tagumi ya sake kiran ta a waya.
"Malama ki fito ina waje"
Haka ya faɗa a fusace kamar zai kai mata duka ta cikin wayar, jikin ta a sanyaye ta ɗau hijabin da ta fito da shi dogo jalbab, ta zura lokaci ɗaya tana rataya baƙar jakarta haka ma takalmin kafanta ma baƙi ne keys ɗin gidan ta ɗauka sannan ta fita ta kulle ƙofar baya cikin haraban gidan a can wajen get ta gan shi yana jiran ta a cikin mota.
Tana zuwa ta buɗe ta shiga a sanyaye ko kafin ta gama ma rufe ƙofar motar ya fizgi motar a guje sai da ta firgita.
Kallon shi ta yi ya haÉ—e fuskar nan kamar hadari, da sauri da kauda kanta saboda hawaye sun kawo mata sai ta yi saurin shanye su.
"Ina kwana."
Ta faɗa muryan ta a sanyaye, yau da ta ga Habib sai ta ji ba za ta iya ɗaukan kaddaran rasa shi ba, tana son shi kuma tana son ta ƙarishe sauran rayuwanta da shi har abada.
Da ta gaishe shi da farko bai amsa ba sai ta sake gaishe shi nan ma sai ya yi mata banza kamar bai san tana ma cikin motar ba, ita kuma tana ce sai ta gaishe shi ya amsa.
"Ina kwana Noori?
Ta sake faÉ—a cikin marairaicewa.
Wani kallo ya yi mata na tsana da takaici ita wai ba ta da zuciya ne haka ya faɗa a cikin zuciyarsa? Duk yadda ya ke share ta da nuna mata ba ta da wani muhimmanci a rayuwarsa bai sa har yanzu ta fahimci da gaske yake yi ba, watakila sai ya sake nuna mata matsayinta sosai wataƙila a lokacin za ta fi gane matsayin ta.
Kallon da ya yi mata ne ya sa ta kama bakinta ta yi shuru, har suka isa gidan su dake anguwan Zone 3, da suka iso ta ga bai fito daga motar ba ya dai yi parking a bakin get É—in su, itama ganin bai fito ba sai ta zauna shi kuma ya É—auko wayarsa yana dubawa shuru ya ji ba ta fita daga motar ba sai ya juya yana mata wani kallo cikin mamakin ta.
"Sai na ce ki fita za ki fita?
Ya faɗa yana ware mata idanuwanta da sauri Ummu Salma ta buɗe motar ta fita tana kallon shi, kauda kansa ya yi lokaci fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba. Jikinta a sanyaye ta taka ta nufi get ɗin su, ta tura ta shiga ciki amma sai da ta tsaya a haraba ta daidaita kanta sannan ta shiga cikin gidan. Ammah da Baffa tare da Baffa Umaru suna cikin ɗakin Baffa suna ta hira can ta nufa ta shiga da sallama ta duka a gaban su tana gaishe shi.
"Auta kin iso?
Baffa ya faɗa, sai ta gyaɗa masa kai, ba su daɗe da gama karyawa ba tunda ga kayan karyawan nan a gaban su Ammah ba ta ɗauke ba. Sannan tun wajen tara na safe Baffa Umaru ya iso Jimeta.
"Sannu Ummu Salama."