← Book details Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 92

Sashe 80

Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haramun ne? Ai ya sake ki, kuma ko bai sake ki ba zan iya auransa in na ga dama. Amma ni ba zan iya zaman kishi dake ba shi ya sa nace ya sallame ki daga rayuwar mu."

"Da man ba don Allah kike tarraya da ni ba?

"A baya don Allah na ke zaune dake amma daga lokacin da kika auri Sweety na tsane ki Ummu Salma."
Ta dakata tana kallon Ummu da ta koma tana mirmishi kamar mahaukaciya

"Kuma na ja baya dake ne saboda bana son alaqar mu, bana son ki a rayuwata. Ki je ki cigaba da rayuwarki amma ki manta da kin taɓa sanina ballatana Habib. Mu zama kamar mun shuɗe daga tunanin ki."

Ummu ta girgiza kai ba za ta iya fassara a yanayin da ta ke ciki ba.
"Sannan kar ki damu kaf dangina ba su nan kin auri Habib ba, sun san shi ne kawai a matsayin sa na mijina."
Ta faɗa tana kashe mata ido ɗaya cikin dariyan shaƙiyanci.

"Na gode, da man tabbacin nake son sani tunda kuma na same shi daga wajen ki ba komai."
Ummu ta faÉ—a cikin aro jarumta.
Kawai sai ta juya za ta bar É—akin tana jin maranta na daurewa a waje daya, ga É—akin na juyawa mata amma ta daure.

"Ba ki ji ba."

Ummu ta juyo tana kallon ta.

"Na so ki zubar da cikin nan,  watakila da kin iya samun wani wanda zai kwashe ki, amma kika yi taurin kai ki ji be ki fa yanzu? Wa zai kwashi bazawara mai ɗa, ɗan ma mai kama da ɗan shege tunda uban cikin ya ce ba ya so"

Ta gama faÉ—a tana kwashewa da dariya har tana tafa hannuwanta
Juyawa kawai Ummu ta yi ta fice daga É—akin tana jan kafa, ita dai ta san ta bar gidan ta kuma yi tafiya mai nisa a hanya kafin ta samu abin hawa.

Ta san kamar hankalinta ya gushe domin ba ta ma san har ta faÉ—i sunan anguwarsu ba, ita dai an sauke ta a bakin titin gidansu ta sauka ta ba shi kuÉ—insa sannan ta yi tafiya zuwa gida da kafafunta.

Ba ta kuka ba ta komai amma tana ji kamar yau za ta bar duniya.
Masallatan anguwan har sun idar da sallar isha'i wasu ma sun daÉ—e da idarwa.
Ta shiga gida ba ta damu da Ammah ko Baffa su ganta ba.
Ba ta damu da su tuhumeta ba.

Kawai ta faÉ—a ne kai tsaye.
Hamma LamiÉ—o na tsaye wajen É—akin Baffa yana waya ya juya baya. Ba ta san shi ba ne sai da ya juyo shima ya ji ana ta jefa kafafuwa ne yaraf yaraf shi ya sa ya juyo.
Ido huÉ—u suka haÉ—a domin akwai hasken wuta a tsakar gidan.

Mamakin ganinta yake yi ga ciki a gaba sannan yarkace-yarkace kamar ba ta cikin hayyacinta. Ta kalle shi cikin wani yanayi shi dai juyawa kawai ya yi ya cigaba da wayarsa ita kuma ba ma ta shi take yi ba da sauri ta faÉ—a falon Ammah.

Tana shigewa ya bi bayanta
Da kallo  cikin mamakin me ya fitar da ita a cikin wannan daran? Me ya same ta ya ga kamar ba ta da lafiya. Duk da fa ya daɗe bai ganta ba, ba haka take ba.
Sai kuma ya yi tunanin watakila ciki ne ya mayar da ita haka.

Yana gama wayarsa ya koma cikin É—akin Baffa abinci yake ci aka kira shi a waya ya ta shi.
Ammah kuma ta shiga ciki ta je yin sallah. Komawa ya yi gaban abincin shi Baffa na gefen shi da man Ammah ce ke hiran bayan ta tashi sai É—akin ya yi shuru.
Shi Lamido da man bai iya hira ba shi kuma Baffa sanin halin shi ya sa bai ma bata bakin shi ba

Ammah na É—akinta ta idar da salla ta ji kamar an shigo
Ta fito haka dai daidai lokacin da Ummu ta shige É—akinta ta rufe kofa.
Sai Ammah ta É—auka ita ce ta fito falo ta koma, domin ba ta san Ummun ba ta a gidan ba, bayan fitan ta LamiÉ—o ya zo suna É—akin Baffa gabaÉ—aya.
Daga nan kawai ta fice ta koma É—akin Baffa.

Ummu ta sulale a kasan cafet tana jin zuciyarta na zafi kamar za ta mutu. Abubuwa suna gilma mata. Shamsiya da Habib.
Me ta yi musu da za su lalata mata rayuwarta haka?.
Shamsiya fa da suke ƙawance tun suna yara ita ce ta ci amanarta da namijin da ta ba ma Amanar rayuwarta.
So take yi ta daina jin zafin da ke ji a cikin zuciyanta.
So take yi duk wani damuwarta da take ji ta daina jin su, so take yi ta bar duniyan nan ko za ta samu yar salama.
Amsar kuwwan Kalaman Shamsiya sun kasa barinta ta huta, sun saka ta jin gwara kawai ta ji shuru gwara ta sama ma kanta natsuwan zuciya.

Miƙewa ta yi tana layi ta isa gaban madubi ta ɗauki reza sabuwa a cikin kwalinta ta buɗe. Rezan ba na ta ba ne na Ammah ne kwali ɗaya take siyab itama shekaranjiya cizgiya ne ya fito mata a gefen hannunta sai ta yi ma Ammah magana ta bata, bayan ta cire sai ba ta mayar mata ba sai ajiye a saman madubin ɗakin.

kallon kanta take yi a madubi tana tunanin yanzu rayuwarta ba ta da amfani hijabin jikinta ta cire ta na kallon cikin jikinta.
Ba amfanin ta haifa ma Habib yaro ko yarinyar dake cikinta domin bai cancanta ba, yadda zuciyanta ke zafi ne take son kawai ta hutar da kanta.

Ba tare da tunanin komai ba ta ciro rezan ta daidaita tsitsiyan hannunta na hagu za ta yanka lokaci ɗaya tana mai runtse idanuwanta hawaye na wanke mata fuska, sai ƙaran vibration ɗin wayarta ya dakatar da ita wayar na kan madubin ne, idanuwanta na ganin duhu amma sai da ta ga sunan mai kira, Sisna Baɗɗo ce take kiranta a lokacin da ba za ta saurare ta ba, a lokacin da ba za ta iya amsa wayarta ba.

Tana mai zubar ƙwallah wasu na fitowa wasu na ƙoran wasu ta sake daidaita hannunta
ta yanka sai ga jini ya tsartsu, ta runtse ido tana jin wani irin zafin azaba na ratsa ta daga ƙafafunta har saman ƙwaƙwalwarta.
Sake yanka hannun nata ta yi a karo na biyu jini ya sake tartsuwa, ta sake runtse ido sabo da azaba mai raÉ—aÉ—in da ya dabaibaye jinta da ganinta tana gani jininta na zuba a kan madubi yana gangarawa a kasan cafet da gudu kamar an buÉ—e famfo.

Azaba take ji amma kuma tana jin daÉ—i yanzu za ta daina jin abin da take ji a cikin zuciyanta. Gwara ta mutu in ta mutu za ta huta.
Tana mai kallon kanta a madubi tana hawaye ta fara ganin kanta biyu biyu kafin ta ji jiri ya kwashe ta, ta yi baya ta dafa gado amma ina ya rinjayeta, tuni idanuwanta suka hau lumshewa jikinta ya saki da ta kasa iya riƙe kanta
nan ta sulale ta faÉ—i kasa ta gefen hagu.

Hannunta kuma har a lokacin bai daina zubar da jini ba, ga rezan da ta yanka kanta nan a yashe a gefen ta
Ta ji daÉ—i domin jinta da ganinta ya tsaya cak zuciyarta ta daina aiki ta daina jin komai ta samu salaman da ta ke fata.
Ta ji É—if, ta samu natsuwa ta samu hutun zuciyan da take muradi.

*1k on Telegram 09069067488*

*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No. 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supplements wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

*20*

*DAAMA SPECIALIST HOSPITAL*
NO:70 72 Abubakar Atiku Rd. Jimeta Adamawa.
VIP:Room 23.

Ta daɗe tana jin wucewar iska a cikin kunnuwanta. Sannan kanta ya yi mata nauyi sosai tana ji kamar an ɗora mata katon dutse, idanuwanta take so ta buɗe amma ta kasa ji take yi kamar an danne idanuwanta nata da wani abu mai nauyin gaske. Tana ta ƙokarin motsa gangar jikinta lokaci ɗaya da fitar da numfashi sosai amma ta kasa jikinta ya tamke, ko ɗan yatsanta ba ta iya ɗagawa sai ma take ji kamar wuyanta ya rabu da gangan jikinta ne. Sannan bakinta da wani abu an yi mata takumkumi da ya hanata damar iya sakin numfashi sosai.

Tana jiyo ɗan maganganu daga can nesa da ita amma ba za ta tantance komai ba, tana cikin kamar tsakanin rayuwa da mutuwa ne. Komai daga nesa take jin sa kamar ba a kusa da ita ba ne, tunani take ko dai ta mutu ne tana cikin kabari, tabbas ta mutu ƙasa ne ya danne ta da ya sa ta kasa motsa gangan jikinta.

"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."

Ta furta a cikin zuciyanta, tana ta ƙokarin buɗe idanuwanta ta kasa sai da ta daddage sannan ta samu nasaran buɗe kumburarrun idanuwanta da suka yi mata nauyi kamar an ɗora mata jakan duwatsu a sama, dishi dishi ta fara gani kafin ganin ta ya ɗan fara washe.

Farin POP ta fara cin karo da shi lokaci ɗaya da karamar farar fanka a sama tana gudu sosai, shi ne iskar da take jin ƙaran wucewarsa a a cikin kunnuwanta.
So take yi ta tuna abin da ya faru da ita amma ta kasa tuna komai, tunanin ta ya fi karkata da cewa ta mutu ne, to amma in har ta mutu to nan ba a cikin Kabari take ba, domin a cikin kabari babu rufin É—aki sannan babu fanka.
Chapter 80 · 0% Book details