Sashe 21
Fargar Jaji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da wuri Habib ya dawo tun kafin ma a kira sallar isha'i ya shigo gidan da niƙi-niƙin ledoji ya siyo balangu da su lemon exotic. Yana ganin ta ya buɗe mata hannuwana ya ce ta taho ita dai ba ta saki jiki ba, ta tafi gare shi ya rumgume ta yana wani shinshina wuyanta cikin sanyaya murya ya ce.
"Na yi kewar ki Baby."
Hawaye suka kece ma Ummu, amma Habib bai bar ta haka ba sai da ya ɗago ta ya saka harshen shi yana lashe mata hawayen fuskarta, daga nan ya fara yamutsa ta, duk da zuciyarta na son ta hana shi amma ta kasa cewa ta ke yi Habib ne, Habib ne fa mijinta masoyinta. Tun a falo ya raba ta da rigan jikinta sanyi take ji shi ya sa duk tsigan jikinta ya tashi ga shi jikin na ta ya ɗau zafi amma Habib bai lura da wannan ba. Haka ya iza ta zuwa cikin bedroom ɗin su ya mora jikin Ummu fiye da yadda ya saba mora tana ji ana ta sallar isha'i a masallatan kusa da su amma Habib bai saurara mata ba, ta gaji ba za ta iya ba amma bai fahimta ba, lamarin na shi babu tausayi da ya kawo kamar zai sauka sai ya koma tun Ummu na kuka a ɓoye har ta dawo tana yi a sarari babu in da jikinta ba ya rawa, sai ta ji kamar ba Habib ba sai ta ji yau ba ta ji daɗin abin ba kwata kwata ta ji wani haushi na sukan zuciyarta amma bai saurara mata ba sai da ya gaji domin kan shi ya kuma tsallake ta ya shiga tiolet domin tsarkake kan shi.
Kanta ta tusa cikin bargo tana kuka amma ta rufe bakin ta kar ya yi sauti, tana jin shi ya fito yana ce mata ta tashi ta yi wanka su ci abinci yana jin yunwa, ko tsayawa bi ta kanta bai yi ba ya fice ya bar ta nan kwance tana kuka. Da kyar ta iya rarrafawa ta shiga tiolet mene ne ya sa Habib ya yi mata haka! Ko yana so da karfin tsiya sai ya yi ajalin cikin jikin ta ne, Allah ya fi shi domin tun da ta gano manufarsa ta ke saka shi cikin addu'o'in ta na Allah ya tsare ta ita da cikin ta daga sharrin Habib, amma me ya sa har yanzu ba ta daina jin ta daina son Habib ba, tana son shi tana son cikin jikinta sannan tana son auransu shi ya sa yau ɗin ma ta kasa yi masa gaddama.
Jikinta zazzaɓi ne rau haka ta rarrafa ta fito ta sauya kaya ga shi kanta ya jike kuma ciwo yake yi mata ba ta ko samu damar busar da shi ba Habib ya zo ya dame ta da cewa yana jin yunwa haka ta fita daga ita sai wata riga doguwa ta wani yadin material ita ce a farkon wardrope shi ya sa ta saka ta. saman dinning suka zauna ta yi serving ɗin shi ganin ita ba ta saka ma kanta ba ya sa ya tambayeta a sanyaye ta ce ba ta ci ko ta ci sai ta yi amai.
Sai ya É—auko mata balangun da ya siyo ya ce ta ci ko kaÉ—an ne.
"Ba zan iya ci ba."
Ta faÉ—a a sanyaye ajiye spoon É—in hannun shi ya yi yana kallon ta hannunta guda É—aya ya kama yana faÉ—in" Sannu Sorry ki ci ko kaÉ—an ne sai ki sha wannan lemun in sha Allahu ba zaki yi Amai ba"
Tana cewa ba za ta ci ba yana É—aukowa ya nufi bakinta da shi tana kauda kai amma sai da ya saka mata shi a cikin bakin ta da ta tauna sai ta ji daÉ—in shi, shi ya sa sai ta sake É—auka ta kai bakinta tana taunawa lokaci É—aya tana kallon shi.
"Kin gani, ba za ki yi amai ba"
Ya faɗa yana yi mata mirmishi, yake ta yi masa ba ta yi mgana ba, abin da ya ba ta mamaki da ya sa ta sake jin a ran ta cewa Habib ba shi da gaskiya, lemun exotic guda biyu ya siyo da zai tsiyaya mata na ta dabam ne, na shi ma na dabam sai ta fara tunanin tunda sha za su yi me ya sa sai ya buɗe har guda biyu, kawai sai ta ji ba ta aminta da cewa Habib ba yana wannan abin don Allah ba ne. Yana yi ne ba domin komai ba sai domin cimma manufar da ya so ta biye mishi ya aiwatar. Ita kuma ta shirya masa da sanin ta ba za ta taɓa bari ya yi galaba akan ta ba.
Guda huɗu ta ci balangun sai ta cire hannunta da sauri ya kalle ta." Kin ƙoshi kenan?
Sai ta jinjina masa kai, da sauri ya miƙo mata lemun da ya saka kofin tangaran yana faɗin" Sha wannan sai naman ya kwanta miki yadda ba za ki yi amai ba."
Kallon shi ta ke yi kafin ta ce ta ƙoshi.
"Sha mana."
Ya sake faɗa yana tura mata kofin a bakinta da sauri ta kauda kai, maimakon Habib ya bar ta haka sai ga shi har yana miƙewa ƙoƙarin sa ya tura mata wannan lemun na dole sai ta sha ganin haka kawai ya ba ta tabbacin koma mene ne yana cikin wannan lemun na hannun Habib.
Ganin ta yi Habib na neman yi mata É—ure, tunda ya tashi daga zaune ya matso kusa da ita, ya rike kanta yana tura mata kofin zuwa bakin ta yana faÉ—in ta sha.
"Ki sha mana."
Ya faÉ—a yana kallonta.
"Na ƙoshi, zan yi amai in na sha."
Ran shi ya fara ɓaci ko ta fahimci akwai wani abu a cikin lemun ne
" Ki sha na ce miki ba za ki yi Amai ba."
"Ba na so na sha."
Ummu ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙokarin miƙewa zaune shi kuma bai sani ba ya kawo hannun shi sai ta kaɓe kofin da lemun suka tarwatse a saman dinning ɗin.
Jikin Ummu na rawa take kallon shi, shi kuma lemun da fashasshan kofin ya ke bi da kallo ran shi na ɓaci.
"Ka yi haƙuri."
Bai ce mata komai ba ya wuce kitchen ya sake ɗauko wani kofin ya zuba mata yana faɗin" Wannan ki sha, ki sha na ce Ummu Salma kafin ki ɓata mini rai."
Ai kafin ya nufota ta bar wajen Dinning É—in zuwa falo sai ya yi tsaye da lemu a hannun shi yana kallon ta.
"Ke me ye haka?
Ya faɗa ganin Ummu ta nufi bakin ƙofa ta tsaya.
"Dawo nan malama."
Ya faÉ—a yana takowa tsakiyar falon.
Ummu ta sake matsawa jikin kofa ta saka hannu ta murza key ɗin ta buɗe ƙofar lokaci ɗaya tana faɗin" Na ce ba zan sha ba dole ne."
"Dole ne, dole ki sha wannan lemun domin cikin jikin ki ya zube."
Ya faÉ—a cikin tsawa har yana zare mata idanuwansa
Da man ta san za a rina hawaye suka kece mata cikin rauni ta ce" Me ya sa Habib? Wai me ya sa kake son raba ni da gudun jinina ne?
"Saboda bana so ki haihu. Ban shirya hakan tare da ke ba."
"To me ya sa?
Ummu ta katse shi a tsawa ce da karfi sai kawai ya tsaya yana kallonta ga ƙofa a buɗe kar saboda hayaniyarta ta tara musu jama'a da ya shiga uku.
"Ki dawo cikin falo mu yi mgana."
Ya faɗa yana ɗan kwantar da murya har lokacin kuma lemun na hanmun shi dama yake so ya samu ya yi mata ɗuren shi chemist ɗin da ya siya mganin mai wajen ya ba shi tabbacin in ya saka mata guda biyu a cikin lemu ya tabbatar ta sha ko kaɗan ne cikin nan ba zai kwana ba zai zube, hankalin shi da natsuwar kawai yanzu ya ga cikin nan ya zube, idanuwansa sun rufe kawai cikar burin sa ya ke nema ko ta halin ƙaƙa ne.
"Ummu-Salma ki rufe ƙofar nan ki dawo nan ki zauna ki karɓi lemun nan ki sha tun kafin raina ya ɓaci."
Ya faÉ—a yana kallonta ita ko sai ta sake matsawa kamar za ta fita tana faÉ—in" Wallahi ba zan sha ba, kuma kana cewa za ka matso ni zan fita na yi maka ihu."
Ta faÉ—a cikin kuka yadda ta yi É—in ya san za ta aikata haka, shi kuma ba zai so mutane su taru akan sa ba, kowa ya ji ga abin da ke faruwa za a ba ma rashin gaskiya.
Kansa ya dafe da hannu É—aya da yake jin yana sara masa lemun ya koma ya ajiye a saman dinning sannan ya dawo tsakiyar falon yana faÉ—in.
"Ki dawo nan mu yi mgana "
"Ba zan dawo ba,"
Ummu ta mayar masa da amsa da iya gaskiyan ta domin tana da tabbacin in har ta bari Habib ya kama ta to ba cikin jikinta ba har ita zai iya yi ma lahani tun da alamomin sa sun nuna duka abin da ya faɗa gaskiya ne.
Ba ya son ta sannan ba ya son haÉ—a zuru'a da ita, ya faÉ—a ya kuma nuna shi a aikace kamar yadda yake nunawa yanzu.
Habib ya fara rasa control É—in shi, ya nufi Ummu da sauri ita kuma ta fita waje ya fito sai ga megidan flat É—in gefen su, yadda ya gan su kamar zakaru ne ya sa ya É—an tsaya ganin shi ya sa Habib ya yi saurin wayancewa da cewa" Baby mu yi wasan a É—aki mana kin ga nan saboda dare"
Jin haka yasa magidanci ya yi mirmishi ya wuce yana shigewa shashen shi Habib ya kalli Ummu cikin tsana da baƙin ciki ya ce.
"Ke wata irin daƙiƙiya ce, komai sai an yi miki bayani ne za ki gane?
Ya faɗa a fusace har jijiyon kansa sun miƙe saboda yanayin da ya ke ciki.
"Sau nawa zan faÉ—a bana son ki, ba kuma don ki haihu na auro ki ba."
Ya faÉ—a yana yarfa hannnuwansa yarinyar nan tana so ta bashi matsala tana so ta rusa duka shirin sa.