Sashe 99
Abu Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da Hadima suka kalli juna Jon wuro kam mamaki yay kafin Malamin Alaafin yace. "Kina tunanin ban sa me nake ba ko? Bayan kin cilla Yarinyar ki cikin kogi ke kuma an harbeki, bayan duk sun tafi na dawo wajan duba yarinya ban same ta ba, har zan tafi sai naga kina motsi da sauri na auke ki zuwa asibiti akai Maki aiki, kai tsaye na kaiki cikin Alaafin akan Sabuwar Hadima, cikin Sa'a kuma late King Tunde Muhammad Jalal ya mayar dake Amintacciyar Hadimar sa, nasu na janye tunaninki domin kina yimin aiki, sai na kasa saboda tsarin dake jikinki, sosai na fahimci akwai abinda kike oyewa sai ban fahimci komai ba, dole na rabu dake, wannan Yarinyar kuma bayan naje Rugar Mahinjo naga Yarinyar hannun wata tsohuwa a nan wani Madibbo yake shida min cewa ar gidan MUIDO ce, ya tsince ta a ruwa dalilin da ewar da tayi a ruwa kuma idanunta sun samu matsala, har wasiyyar da Mahaifin ta ya bayar ya nuna min, Ni kuma na samu Ar o na fa a masa akan duk yadda za'ai yaga bayan Madibbo Sannan ya auke wasiyyar daga wajansa" Wani irin da i ne ya ziyarci zuciyar Hadima Zubaida tace "tun kallon farko da nayi wa Julde nasan tabbas ita iyata ce, Allahamdulillah" kuka ne ya kwance wa Julde ta fa a jikin Abu Maleek tana kuka. Queen Roomana ce tace "kamar yadda wasu suka sani wasu basu sani ba, nidai ban haifi Jalaluldeen ba, ban kuma haifi Khaleluddeen ba, Adams shine ana, wanda na haifa da ciki na, ina tare da Oumuu-Ayman tun ina budurwar inda na kasance kuma wara ga King Muhammad Jalal, ranar da Akace ya rasu ranar ta same ni, nida Mai Babban aki take fa a min cewa zan zama madadinta na kuma Queen Roomana madadin wara, shiru nayi domin bana jin zan iya wannan aikin,amma da tace akan rayuwar Jalaluldeen ne da sai na kasa yi mata mosu, a wannan lokacin daman Tunde ba'a asar yake da zama ba shi da matarsa Queen Ayoola, hakan yasa tun a can aka ha a plan dashi cewa idan yazo zan zama Queen Roomana amma dai a oye ni in zan zama wararsa kamar yadda nake warar Muhammad Jalal, a zahiri kuma Oumuu-Ayman itace warar anyi haka ne kuma saboda fahimtar cewa akwai munafukai, aka sauya komai na Alaafi a wannan lokacin ma hadda Otun da Agba Akin aka shirya, amma dake suma butulu ne suka fara cin dudduniyar mu, duk da cewa babu wanda suka fa awa, lokacin Jalaluldeen yana arami ni kuma ina tare da Adams ya an fara wayo, saboda shima an King Muhammad Jalal ne amma kasancewar ni warar ce yasa bashi da ikon gadar sarauta, lokacin da Late King Tunde Muhammad Jalal ya dawo Alaafi aka bashi sarauta ya fara bincike akan komai, lokacin yaransa biyu Shakiru Sharefddeen, bayan Queen Ayoola ta haife su sai suka samu Matsala ta fita ta auri wani a nan ta haifi Salimerh mutumin ya mutu sai aka mayar da Auran su da Tunde Muhammad Jalal, komai Oumuu-Ayman ke yiwa Jalaluldeen yayinda ni kuma aka sanya min idanu domin tunanin duk na kowa ni matar King Tunde Muhammad Jalal ce saboda ya fa awa Queen Ayoola yana da mata a Nigeria da yara biyu, Adams da Jalaluldeen, ansha kawo min hari za'a kashe ni kowa yana zaton nice uwar Jamaluddin amma rashin sani duk yasa suke haka, asalin mahaifiyar Jalaluldeen itace Oumuu-Ayman, soyayya mai zafi ce tsakanin Oumuu-Ayman da Abu Maleek, wanda duk mai hankali idan ya duba yasan cewa ba iya sha uwa ce zallar so da auna ne da jini dake yawo a cikin ko wannan su, kwanci tashi tafiya tayi nisa Oumuu-Ayman ta fahimci tana da ciki, ashe tun baya akwai cikin amma kwanciya yay, sai na rufe kace Oumuu-Ayman babu lafiya a bata hutu, dake kowa ba sonta yake ba, saboda tsananin girmamawar da King Tunde Muhammad Jalal yake mata, a haka ciki ya tsufa tana haihuwa aka bawa Hadima Zubaida rainon yaron mai suna Khaleluddeen, bayan suna shima aka zana masa Taswirar Alaafi, ban sa n wanda ya sace ni ba, saboda kullum fuska a rufe ake zuwar mu, dani da Oumuu-Ayman mu kaje aka cirewa Abu Maleek sha'awarsa ya zamana baya son ko wacce mace, dalilin dukan kuma da akai masa ya samu matsala wanda yanzu Allhamdulillah ya dawo dai-dai" Shiru kuwa yay yana tunani yayinda Salimerh kuma tace. "Uhm arasa aikin ka" gyara tsaiwa Malamin yay yace "babu abinda zan maka kawai Taswirar jikinka muke son auka" wani irin mugun kallo Abu Maleek yaywa Malamin yace "idan kana da arfi kazo ka auka" Murmushi Salimerh tayi tace "haka kace?" Wani banzan kallo yay mata dan shi a tsarin shi baya sanya mata, musamman da yaji wai itace ta kashe mata Maaamahh in sa, "Uhm shut him" Malamin ya fa a yana bawa Ar o bindiga cikin bada umarni, amsa Ar o yay yana nuna Abu Maleek da bindiga kafin kuma da sauri ya ura bindigar akan Malamin yace "Muhammad Jalal my name not Ar o, na dawo hankali na yau in nan bayan komai daya dawo cikin bacci na, idan Taswirar kake so gata har biyu za i wacce kake so, da sauri Julde ta zare rigar jikin Cucuu, cikin sauri Ar o ya zare rigarsa nan take Zanan Taswirar ya bayyana a irjin ko wannan su, da wani irin sauri Salimerh ta..... Allah Ubangiji ya nuna mana Monday lafiya idan nai kuskure feel free bawai ka zagen ba dan Allah, an Adam ajizi ne,a kullum muna yiwa Ubangiji laifi bare an Adam *SARAUTAR MARUBUTA* *_95-96_* Tai baya luuu zata fa i Junaid yay saurin tare ta, da wani irin hargitsastsan kallo take bin kirjin ko Wannan su, a hankali kuma cikin ru u ta fara bin zanan Taswirar dake irjin ko wannan su,sosai tai mamakin ganin zanan Taswirar yana da bambanci da wacce take jikin Ar o da kuma wacce take jikin Abu Maleek, Murmushi Muhammad Jalal yay yana wani an lumshe idanunsa kamar yadda Abu Maleek keyi Salimerh ya kalla yace. "Mamaki ko? Ban san ki ba, i have no idea akan who are you, amma ke har kin samu damar farautar abinda yake ba naki ba? Kin samu damar da zaki kwashe dukiyar da ko mahaifiyar ki bata da iko a kanta balle kuma ke? Uhm kamar nasan da haka, hanyar fitar da kaya ta ashin asa a Alaafi guda biyu ce, ko kin samu Taswirar jikine Abu Maleek akwai inda zaki ata a hanya, domin an cire zanan ofa biyu na ashin asa, kina tafiya hanyar zata bau e maki, Wow! The you know what? Zaki koma hanyar Zanan Taswirar jikina, ita kuma bakinsa yadda zata fitar dake waje ba, hakan yasa zaki ata att, ki asa dawowa Alaafi kuma ki asa fita wajan gari, hakan na nufin zaki are rayuwarki ne a cikin ashin asa" Shiru yay yana sauke numfashi yana jin yadda kansa ke masa ciwo kafin a hankali ya dawo da dubansa ga Malamin Alaafin yace. "Ka sauya min fuska, kasa anyi min juyan tunanin Mutumin da bashi da imani ko aya a ransa, ko iya haka na Barka Ubangiji zaimin sakayya dakai, na amince maka na yarda da kai na baka dukkan amanata amma kai watsi da hakan ka ruguza farin ciki na, bana aunar fuskar daka sanya aka samin Kamilalliyar fuskata tafi wannan da take jikina, kamar yadda ka sani mu biyu mahaifin mu Jalal ya haifa, da Tunde da kuma ni Muhammad, nine babba amma ko da nayi aure ban samu haihuwa da wuri ba, sai ya zamana Tunde ya rigani haihuwa ya haifi Sharefddeen, Tunde ba yaji he's very stubborn wannan dalilin tun kafin yay aure yabar asar, sai da yay auran muka samu labari, lokacin Mahaifin mu ya rasu, Ni kuma naci gaba za ri e kujerar sarautar Kanzaf, bisa taimakon Otun da Agba Akin, da Mai Babban aki, sai kuma wara ta Roomana" shiru yay yana jin wani hawaye na kawowa fuskarsa cikin dauriya ya kalli Salimerh yace. "You killed my wife, me tayi maki? Akan kawai biyan bu atar ki? She's so nice, friendly Educated ina da tabbacin komai kika ce kina so zata baki, kin kashe min matata ba tare da laifin komai ba, ilan abinda take gudu kenan shi ne yasa ta maida kanta matsayin wara, akwai yakkyawar fahimta tsakanin matata da brother na, akwai wasan anin miji yana girmama ta sosai, shiyasa take kula da shi amma kalli yadda kika kasheta,ta hanya mai muni you killed my wife Salimerh" ya fa a yana zubewa a wajan tare da fashewa da kuka, jikin Abu Maleek ne ya auki rawa ko ina na jikinsa tsuma yake, duk da cewa ya samu lafiyar walwarsa amma zafin zuciya ya riga daya samu gurbi a cikin zuciyarsa.. Zame hannunsa yay daga cikin na Julde a hankali yake tafiya zuwa inda Da ile take wacce ta kasa koda mutsi, yana zuwa ya sanya hannunsa tare da auke ta da wani ba hagon bari, arfin marin yasa tai baya da sauri zata fa i Junaid ya sake ri e ta. Jiki na rawa Abu Maleek ya ara aga hannunsa tare da sauke mata wani marin jiki na rawa kuma ya ri e wuyanta tare da sha e ta, wani irin nishi ta fara Idanunta ya shiga fitowa. Ganin hakan yasa Junaid fa in "Abu Maleek ka sake ta please na ro e ka, nasan tayi abinda ya cancanci kisa, amma kayi min alfarma saboda cikin dake jikinta" da sauri Queen Roomana ta kallesa jin Abinda yace a hankali kuma tace.. "Wanne ciki kuma? Cikin daya da e da bin rariya lokacin data fa i tun baya, ka kuma manta lokacin da tayi jinya ko ita tace maka tana da ciki" Baki ya saki cikin rashin fahimta yace "kamar yaya? Bayan ina da tabbacin akwai ciki a jikinta" Murmushi Queen Roomana tayi kafin tace "to gata nan ai, Jalaluldeen sake ta sai tayi masa bayani" Abu Maleek baya gane zan can, idanuna kawai yakkyawar fuskar Oumuu-Ayman suke hasko masa da wani irin arfi yace. "Kin cuce ni, you blackmailed me, kin kashe min uwa mahaifiya, sai yanzu na fahimci