← Book details Abu Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 108

Sashe 27

Abu Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hannunsa ri e da wata paper wacce babu wanda yasan da ita wajansa, sabida babu wanda ya iya karatu bare rubutu a cikin Rugar. Yana tsaka da duba paper ne yaji Muryar Lami o yana kwala masa kira da dukkan muryarsa, da sauri ya oye paper kana ya fito, Abinda idanunsa suka gani ne ya sanya shi zare ido, Julde a hankali tayi bayan Abu Maleek tana oye fuskarta domin a yanzu shi kawai take tunanin zai taimaka mata, Gyara Ar o yayi kafin yace. "Ardon Allah arya kake, shaiii kaci Ubanka ka biya mu Naggen mu, Lami o kawo mana ita nan ka tara mana jama'ar gari" Jin haka ya sanya Julde sanya ihu a gigice kuma ta sanya dukkan hannayenta a saman ququn Abu Maleek tare da ura fuskarta a tsakiyar bayansa ta amesa, da sauri ya runtse idanunsa sabida sarawar da kansa yayi masa ga wata halbawa da zuciyarsa tayi masa, Kasa motsawa yayi da sauri kuma yasa hannunsa ya dafe kansa saboda yadda yaji Julde ta ara.... *ABU_MALEEK NA KU I NE KIJI TSORAN ALLAH KADA KI TAFI LAHIRA DA ABINDA BA NAKI BA, IT'S 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK 08119237616* *_Nimcyluv 25-26_* Manne Jikinta a bayansa, tare da amesa sa sosai, hawaye na zuba daga cikin Idanunta, yayinda dukkan Jikinta ya auki rawa tamkar mazari, Abu Maleek kam abun ne yazo masa a bazata, jin yadda Julde ta rungomesa tana manna fuskarta a bayansa ne ya sanya shi janye idanunsa a hankali tare da rufe su ruff, ya shiga sauke numfashi a hankali yana mai an taune jajayen la ansa, o dake tsaye ya ara duban Lami o yace. "Maza ka auka shi ka kawo min shi nan" Ya fa a yana mai kallon Abu Maleek kafin Lami o yayi magana Ar o ya ara cewa. "Kai mahaukaci mene ya kawo ka rugar Mahinjo, me kazo yi a wannan rugar, ko kuma kasan wannan yaron Julde ne?", "JULDE!!!?" Sunan da Abu Maleek ya ara maimaita wa a cikin zuciyarsa kenan, to mene ma'anar wani suna Julde ne? A zahiri kuma raunatattun idanunsa ya bu e tare da saukesu akan Ar ara ware idanunsa ya yi akan Ar o fari ne tass an shawalwali dashi, baya da wani jikin arzi i sai dugun wuya, allah zai iya kaiwa Shekaru arba'in, janye idanunsa yayi ba tare kuma da yace komai ba, domin shi ba wannan yake bu ata ba, All abinda yake bu ata shine hanyar da zata sada shi da Birnin Bera wannan shi ne, Lami o ne kai tsaye ya nufi inda Julde take manne a bayan Abu Maleek tare da rufe fuskarta da tsakiyar bayansa, sai tsuma Jikinta yake, Yana zuwa ya mi a hannu zai jawo ta tare da rabata da jikin Abu Maleek ance. "Wait" Jin sautin zazza ar Muryar mai cike da ilhama da kuma tarin nutsuwa da kamewa ya sanya, Lami o tsayawa cak, sosai Muryar ta dakar masa zuciya ta sanya shi tuna wata makamanciyar Murya data huce a shekarun baya, a sauri Lami o na ya aga idanunsa ya kalli Abu Maleek cikin azama kuma ya janye idanunsa dan baya jin zai iya, ci gaba da kallon wayar idanunsa sai zuciyarsa ta buga, Ya kuma janye idanun ne dalilin wani tarin nutsuwa da kuma kwarjinin daya hango a cikinsu, Tsoro da fargaba duk ya cika zuciyarsa, saukar Muryar Abu Maleek kuma ya haddasa masa wani irin fa uwar gaba, sosai Muryar tayi masa kama data wani can a shekarun baya, Cikin son dakewa da kuma mazewa Ar o yace. "Haii yaron arzi i wasa ina maka, Hai ka fito daga Bayan wannan Mutumin" Ya fa a yana sakin Murmushin takaici, domin ba aramin cika masa ido Abu Maleek yayi ba, baya jin zai iya yiwa Julde wani abu akan idanunsa, Jin abinda Ar o ya fa a ya sanya ta sakin ajjiyar zuciya a hankali ta shiga zare Jikinta daga bayan Abu Maleek idanunsa a Lumshe tana sha ar wani fitananan amshi daya kawowa hancinta ziyara, Kallon Ar o Lami o yayi da alamar "ya haka?" Girgiza kai Ar o yayi kafin ya juya da baya yana fa "Noi indema?" (Ya sunanka)" Sarai Abu Maleek ya fahimci maganar kuma ya san dashi ake, sabida yana an jin fulatanci ba tare da kowa ya sani ba ake koya masa, Na zai manta sanda Hamida Zubaida take koya masa ba, akwai sanda Oumuu-Ayman ta koya masa, Lami o ne yayi murmushi yana kallon Abu Maleek cike da mamaki gashi dai sak mahaukaci amma sam muryarsa ba tayi kama data mahaukaci ba, "Muje daga ciki" Lami o ya fa a yana mai an dai-dai-ta Hausar sa, yadda Abu Maleek zai fahimta, jinjina kai yayi tare dabin bayan Lami o jin haka ya sanya Julde an mi a hannu zata ri esa da sauri yayi gaba yana mai har e hannayensa a irjinsa, Tsaya tayi cak jin ance. "Ko damata maa?" (Meke damunki?) Zare idanu tayi waje tana dafe irjinta saboda jin Muryar Barkido, Murmushi Barkido ya saki yana arewa Julde kallo, yana jin wata zallar soyayyarta a zuciyarsa, Wanda bai san lokacin daya fara ba haka kuma bai san lokacin da zai goshe ba, Ja baya tayi tana an girgiza kai ganin tsoransa ta keji ya sanya cikin asa da murya yace. "Babu abinda zan maki Julde kiyi ha uri dana baya ma" Ya fa a yana juyawa sabida baya sun Ar o ya fito ya samesa a wajan, shiru tayi ba tare da tace komai ba, Kamar zai kuka Barkido ya ara bu e baki yace. "Julde kiyi ha uri jin? Zaki ha ura ko, bana ara yi maki komai" Ya fa a idanunsa na ciccikowa da hawayen so da kuma aunar ta, asa tayi da kanta a hankali cikin aramar muryarta tace. "To na ha ura" Ajjiyar zuciya ya sauke kafin yace "Nagode, muje ciki na baki kindirmo mai zafi" Farin ciki ne ya kamata hakan ya sanya ta fara bin sahun tafiyarsa har suka isa wata bukka, ciki ta shiga tana zaune ya je ya kawo mata kindirmo mai yawa a warya, kana ya sake fita babu jimawa ya dawo hannunsa auke da wasu kayan Fulani masu an haske ya bata tasa. o ne a gaba Abu Maleek na bin bayansa a hankali cike da Zallar nutsuwarsa irin ta an sarakai, wanda jinin sarauta ya gama ratsa su, Wata bukka mai kyau wacce aka cikata da kayan ado irin nasu na Fulani, Ar o ya sanya kansa cikin Bukkar, Abu Maleek kam tsayawa yayi cak,yana mamakin ta inda zai shiga bukkar gaba aya bukkar a tsakiyar cikinsa ta tsaya, baya tunanin cikin bukkar ma zai Wada cesa, waro manyan gajiyayyun idanunsa yayi waje ganin yadda Ar o ya sunkuya sosai kamar zai dafa asa kafin ya samu ya shiga cikin bukkar, cije lips insa yayi yana fesar da iska daga cikin bakinsa, a hankali cikin kuma asaitacciyar muryarsa mai cike da kamala ya ware softness lips insa masu taushi da an kauri cikin asa da murya very slow yace. "Goodness" Ya fa a yana janye idanunsa daga kan Bukkar, Ar o dake ciki ne yaji Shiru ba on mahaukacin nasu bai shigo ba, ya sanya shi le o dakai ganin Abu Maleek yayi a tsaya hakan ya sanya yace. "Ai shaii ka rarrafa ka shigo" o ya fa a yana mai tsare irjin Abu Maleek da kallo saboda wani ba in zane daya hango, kwance a saman faffa irjin nasa, Ganin hakan ya sanya Abu Maleek ha e rai kafin ya auke idanunsa yana fa "Wicked and stringy man" Ya fa a a fili amma Murya asa, Murmushi kawai Ar o yayi ba tare da yace komai ba, A hankali ya sunkuya sosai, cikin rashin Sa'a kansa ya bugu da gefen bukkar, kwa e fuska yay sosai kamar zai sanya kuka, a hankali cikin Muryar ta a ra yace. "Auchhhiii! Daman salon mugunta akai wannan guntuwar abar, an san ai ba i zasu iya zuwa, mtwss!" Ya fa a yana arasa shiga cikin Bukkar duk ya marai-raice fuska kamar zai kuka, ganin ya shigo yasa Ar o fita tare da warya a hanunsa, Not too long ya dawo da waryar cike da kindirmo mai kyau, wanda yake zalla babu algus, Kindirmon yabi da kallo kafin a hankali ya ha afafuwansa waje guda, bai son Kindirmon sabida sam bai yarda da tsaftar mutanan garin ba, Amma idan ya i sha bai san abinda zai samu nan gaba yaci ba. Zama Abu Maleek ya gyara tare da aukan ludayin Dumar ya sanya cikin wayar kindirmon da aka kawo masa, ganin yadda Kindirmon yake da haske sosai ga wani irin kyau da yayi masa a idanu, ya sanya a hankali cike da nutsuwa ya ara na afarsa kana ya ebi Kindirmon yakai bakinsa, da sauri ya ja idanunsa ya rufe saboda wani da i da kuma gar i daya ratsa cikin kunnuwansa, shan Kindirmon kuma ya taso mata da duka yunwar daya keji a haka yaci gaba da sha, sai da yasha fiye da rabi kana ya ajjiye, Murmushi Ar o yayi yace. "Birnin Bera kace ko, haii daga wannan rugar sai Birnin Bera tafiyar kwana guda ce rakk, amma ha arin tafiyar yafi na shekara guda" Kallonsa Abu Maleek yayi sai kuma ya an ta e baki, yana tsotse la ansa wanda har yanzu da in Kindirmon ya i barin saman harshansa, Lumshe idanunsa yayi harga Allah matsu ya samu maganin ya koma Benin kana ya ga King Tunde Muhammad Jalal ya samu lafiya daga nan kuma sai koma Madrid baki aya, ya samu ya huce dukkan gajiyarsa a can!. Kai tsaye waje Ar o yayi yana zuwa ya nufi wajan Lami o ba tare da yayi magana ba, yaja hannun Lami o zuwa wata bukka, "Meka fahimta dan gane da wannan ba on?" o ya tambayi Lami o yana share zufar data karyo masa, Gaba aya Abu Maleek ya gama firgita Ar o da kwarjininsa, har baya iya tsayawa inda yake saboda tsoro, Lami o ne yaja numfashi kafin yace. "Ban fahimci komai ba, amma dai kamar bashi da lafiyar walwa, duba da yanayinsa da kuma shigarsa, ga kuma yadda kansa gaba aya ya i tsayawa
Chapter 27 · 0% Book details