← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 97

Sashe 88

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashinta da yayi da asuba ma don babu yadda za ta yi ne.

Zancen zuci ta cigaba da yi wanda gaba
aya ya
are akan ba
uwar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki jiya.

Taj ya nuna mata so da
auna kamar ya ha
iyeta.

Wata zuciyar ta ce mata ya kuma saka ki kuka kamar zai
arar miki da hawaye ba.

Tunaninta na kaiwa daidai nan ya bu
ofar da sallama ya shigo.

Da sauri kuwa ta sake yin
asa da kanta ta rufe ko ina.

Taj murmushi ya yi ya je bakin gadon ya soma bu
e lullu
in da tayi.

Bata bari ya gama ba ta kama duvet
in da nata
arfin.

Sai ya saki, ya hau gadon daga gefenta ya turata ciki ta hanyar matsawa yana rufa shima.

"Matsa min, matsa min" ya dinga fa
i har su ka koma tsakiyar gadon sannan ya daina turata.

"Me ya hana ki bacci?

Ko jirana kike yi?" Ya yi maganar yana rungumota gaba
aya a
angaren damansa.

Hamdi ga tsoro ga tsiwa, ta ha
a biyun ta ce, "In jira ka kayi min me?" Da rawar murya.

Taj ya yi dariya "Hamdiyya matar Malam Tajo.

Maida wu
ar ni ba wani abu nake nufi ba."
"Waye kuma Tajo?
an uwanku ne?" Ta harare shi.

"Ni ne shi, shi ne ni." Ya nuna kansa.

Hamdi ta yamutsa fuska "A'a gaskiya."
"To ke ce shi, shi ne ke?"
"A'a fa." Ta
ara da tura baki.

Abin ya burge shi ya kwanta a jikinta "To ya abin yake?"
Murmushi tayi na kunya "Ni ce kai, kai ne ni...shi kuma Tajo bamu san shi ba."
"Taj
in ma in kin ce baki san shi ba sai a siyo rago a saka min sabo." Ya fa
i maganar da wani shau
i dake kwasarsa saboda shagwa
ar Hamdi "duk yadda kike so haka za a yi Mrs Happy."
Wani sabon shafin ya so a bu
e ta ce sam bata san zance ba indai ba sumar da ita zai kuma yi ba.

Ya dinga yi mata dariya.

Su na
ar hirarsu har bacci ya sake kwashe su.

Ba su su ka farka ba sai da aka kira Taj.
anwarsa ce wadda a jerin haihuwarsu bayan Kamal sai shi sai kuma ita Rawda.

Abincin amarya da ango na sati guda ta
auki nauyi saboda gidanta yafi na kowa yin kusa da na Taj.

Kullum safe, rana da dare take turo yaron gidanta ya kawo a babur.

Amarya da ango su ka sake samun lokacin sha
uwa da sabo da juna.

Taj ya bar Happy Taj a hannun yaransa.

Sai Abba Habibu dake zuwa amma ba kullum ba.

Taj yayi yayi ya
auki hutu amma ya
Wata irin soyayya Taj da Hamdi suke yiwa juna wadda bata da shamaki ko basaja.

Sak su ka fitowa juna tun farko, shiyasa ala
ar tasu tayi saurin
ulluwa.

Jin junansu suke yi tamkar tare da soyayyar juna su ka tashi.

Ga Taj gwanin zolaya wadda a sati gudan nan Hamdi ta koya.

Duk ba
on da ya shigo gidan sai ya fita da murmushi saboda nisha
in da zai samu daga masoyan.

Abu biyu ne su ka so damun Taj amma dalilai sun sa basu yi tasiri ba.

Na farko tafiyar su Kamal Umra bagatatan ko ha
uwa basu yi ba.

Yayi mita kuwa kamar ya ari baki.

A ranar da su ka tafi wadda ta kasance kwana biyu da tarewar Hamdi, da yamma ya tafi gida bayan wayar sallamar da Kamal ya yi masa daga cikin jirgi.

Cikin farinciki su ka gaisa da su Umma kafin ya hau sama da aka yi masa iso wajen Alhaji.

Gaishe shi ya du
a yayi Alhaji ya mi
a masa hannu yana girgiza kai.

"Kai ka san ba haka nake gaisawa da
ana ba."
Da sauri Taj ya tashi ya
arasa gaban Alhaji ya mi
a masa hannu.

Alhaji yayi murmushi sannan su ka zauna.

"Ina matar taka?"
Kai a
asa yana susar
eya Taj ya ce "tana gida.

Ta ce na gaishe ku."
"Ina amsawa idan da gaske kake."
Rantsuwa Taj ya fara sai yaga Alhaji yana murmushi.

Da alama dai yayi furucinsa da zolaya ne.

Sannan babu shakka yana sane da abin da ya yiwa Abba Habibu ya
ata ran Hamdi.

Ba dai zai
auko zancen ba saboda ba shi ya kawo shi ba.

Yana da mahimmancin da shi ma zuwa da zama na musamman ya dace da shi.

"Alhaji maganar Kamal ce ta kawo ni."
"Kayi aure Taj.

Bai kamata ka zauna kana
uni don ya tafi ba tare da kai ba.

Ya dace ka fara sanin ragamar rayuwarka da ta
ar mutane ce a wuyanka yanzu.

Ba dole bane Kamal ya daidaita tafiya da kai ba."
"Ba haka nake nufi ba" cewar Taj
Tausayi ya bawa Alhaji yadda ya yi maganar.

Shi kuma ya katse shi ne kawai saboda baya son hankalin Taj
in ya kai ga abin da ake
oye masa.

"To ina jinka."
Shiru Taj yayi.

Alhaji ya sami kansa da yin murmushi.

Yayi matu
ar kewar Taj da halayansa.

Idan kayi masa fa
a alhali bai yi laifi ba, haka zai yi ta marairaicewa sai ka koma rarrashinsa ko babu niyya.

"Ashe baka canja hali ba har yau?

Mijin aure fa kake."
"To ai ba maganar tafiyar nazo yi ba.

Duk da dai naji haushi.

Ko ba a je dani ba da sai a fa
a min.
an Adam ba ya rasa bu
atu a wajen Allah."
"To ka ro
a mana a inda kake.

Allah Yana ko'ina."
"Amma dai ba kamar idan ana shafa Ka'aba ana ambaton suna na da bu
atuna ba ko Alhaji."
Sake fa
a murmushi Alhaji ya yi.

Ya dubi Taj ya ce "welcome home."
Tsabar da
in da Taj yaji bai san lokacin da koma kusa da Alhaji ya rungume shi ba.

Alhaji ya gama basarwa amma a ransa da
i yake ji.

Da ya nutsu ne ya fa
a masa ainihin abin da yake tunani.

Yana magana Alhaji shiru kawai yayi.

Daga dawowa gida, bayan kwana biyu da tarewar matarsa ya zai yi idan yaji ciwon da yake damun
an uwa mafi soyuwa a gare shi?

"Baka yarda da ilimin Dr.

Mubina
in bane har kake tunanin wani ciwon ne yake damunsa?"
"Ba haka bane Alhaji.

Ban sani ba ko idanuna ne amma har wani kumburi naga yayi rannan.

Yanayin bai yi kama da
iba ba."
Shi da baya son
oye abu bai san dalilinsa na son bawa Taj
an lokacin samun farincikin aurensa ba kafin
wai ya fashe.

"Yanzu mece ce shawararka?"
"Idan kun tafi don Allah ka tilasta masa zuwa asibiti.

Idan da kai ne dole zai je ayi masa thorough check up."
Alhaji ya yi murmushi don ya
oye halin da yake ciki.

"In sha Allahu zamu je."
"Nagode." Ya dinga fa
i har ya fita.

A zuciyarsa yana mai fatan Allah Yasa babu komai.

To tafiyarsu Alhajin ne kuma sau biyu ya sake samun kansa a yanayi na
aukewar jin
amshi da
ano.

A na biyun da
yar ya iya
oyewa Hamdi ya shiga
aki yayi ta bulbula turare kafin daga baya abin ya daidaita.

Ranar da ya tasar masa na ukun kuwa ana gobe za su yi sati ne.

Saboda tsabar tashin hankali, yadda yaga rana haka yaga dare.

Cikin tsananin ki
ima ya zame jiki daga wajen Hamdi ya koma falo ya kira Kamal a waya.

RAYUWA DA GI
I 33
Batul Mamman
This page is sponsored by spicesbyMrsghaleetk....yep, MRS GHALEE TK.

Nace ba, wai kina cikin masu cewa girki da spices baya da
i?

Ko kuwa kin saba saya kina bari ya si
e a kitchen saboda baki gane
anon da yake bayarwa ba?

Albishirinki, Mrs Ghalee TK dai za ta yi Ramadan promo.

Dama ce ta samu gareki wajen sayen ingantattun kayan girki masu tallafawa cefane musamman a wannan marra ta tsadar kayan abinci.

Ke dai
ar uwa, harma da
an uwan da ya saba taimakawa iyayensa ko matarsa, ko kuma mai son burge iyali, ku yi tanadi don Mrs Ghalee TK ta zo da rangwame domin gyara tukwanenku.

Ku sai ku garzaya ku nemeta akan wannan layin ta manhajar whatsapp ko kiran waya 08032834178.

Taku ce Batul Mamman, ganau akan kayayyakin da nake tallata muku.

A cikin yanayin ciwo da gajiyar jiki Kamal ya bu
e idanu ya mi
a hannu zai
auki wayarsa.

A gadon asibiti yake inda yake samun kulawa ta musamman.

Da yake dokar asibitin ba a zaman jinya, shi ka
ai ne a
akin.

Alhaji da su Ahmad suna hotel kusa da asibitin.

Tafiyar just
afa ke kawo su.

Tare dashi su ke wuni sai takwas na dare idan an bu
aci duka ba
i da masu ziyara su fita sannan su ke tafiya.

Kwanaki goma aka bashi ya gama shan magani da allurai kafin a fara dialysis.

"Happy lafiya dai ko?" Ya ce cikin bacci da firgici domin kuwa ukun dare harda kwata lokacin.

Kamar an tsunkuli Taj ya
aga kai ya kalli kyakkyawan agogon bangon falon.

Baki ya bu
e gami da girgiza kai.

"Don Allah Happiness kayi ha
uri.

Kasan Allah ban duba time ba.

Ashe past one.

A nan uku ta wuce ko?"
Kamal ya gyara zama ya ce "Eh...mene ne ya faru?

Haka kawai ba za ka manta lokaci ba."
"Gobe sai muyi magana in sha Allah.

Am very sorry." Taj ya ce har zuciyarsa.

"Taj" Kamal ya kira shi da
arfi "me ya faru?"
onsa Taj ya fara yi akan ya jira safiya don har ya katse kiran amma ya sake kiransa.

Su ka
an yi ja'inja
insu sannan Taj ya fa
a masa abin da yake faruwa dashi game da
aukewar
ano da jin
amshi ko wari wasu lokutan.

"Zuciyata tana bani Covid ce.

Nayi browsing naga
aukewar sense of smell da taste suna cikin symptoms
inta.

Ni bana mura amma bayan magrib ina
irgawa sau bakwai Hamdi tayi atishawa."
Kamal yayi
ar dariya "sannu Doctor."
Taj ya
ata rai "Happiness its not funny."
"Na sani.

Shi yasa nake mamaki da kana zaune a gida ka yankewa kanka cutar dake damunka."
Murmushi ne ya kama shi.

Tabbas asibiti ya kamata yaje amma fargaba ta hana.
Chapter 88 · 0% Book details