← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 97

Sashe 83

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari Yaya ta kar
i numbar Amina (08036387204, instagram @meens_incense).

Ta kira su ka yi ciniki akan farashin da idan ka kar
i turaren ma sai ka ce sadaka kawai aka baka.

Da turarukan su ka iso kasa rufe baki tayi don murna.

Ta dai
oyesu kafin Hamdi ta dawo gida ranar saboda ko za ayi mata fa
a sai ta kunna.

Soyayyarta da
amshi ta daban ce.

Ga dai turaruka kala kala, kwalaccam
inta kuwa abar du
irji ce (I mean it, the scent simply calms the heart), sai kuma humra irin wa
anda sai hancin da yaci karo dasu ne kawai zai gane.

Haka aka tattara komai aka zuba a mota domin kammala gyare gyare kafin zuwan amarya.
aki Ummi ta shiga da waya ta turawa Alh.

Usaini sa
o cewa jiya ma Salwa ta sake shafawa Taj turaren nan.

Kuma da alama anyi nasara domin ta sami labari a daren aka kai shi asibiti.

Daga maganar da taji Baba Maje da Iyaa suna yi bayan wayarsa da Abba Habibu da safen ta fahimci ba rashin lafiya bace kawai ta kama shi.

Salwa kuma ta tabbatar mata a text.

Ita Iyaa da wuri ta tafi gidan bikin.

Ta barsu in sun gama girki da gyaran gida sai su biyota kafin dai a fita da amarya.

Yana karantawa ya kirata.

Da ta
auka tsoro ya bata da taji ya fashe da wata irin dariya mara da
in ji.

Da jinda
i ya ce "
arshen wannan
an daudun ya zo."
"A'a fa, ba
an daudu bane" Ummi taji ba za ta iya shiru ba.

Ko makaho ya shafa Taj ba zai kira shi
an daudu ba, balle mai ido.

Idon ma irin nata mai son abu mai kyau.

"Ummi kenan.

Wai me ya hanaki cewa ayi aikin da za ki sami soyayyarsa maimakon wannan sakaryar Salwan?"
"Bana ra'ayin namijin da kowa ke rububi." Tana ji Alh.

Usaini ya yi dariyar rashin yarda.

Tunanin Taj ya so ta bai zo kanta ba saboda tayi nata binciken akan waye shi.

Labarin mahaifinsa ka
ai ya isheta dalilin mayar da kwa
ayinta.

Sannan ta san cewa ko ana muzuru ana shaho a yadda Baba Maje yake ganin darajar Abban Hamdi, da wuya ta gaske a barta ta aure shi.

Ita kuwa abin da take ji a kansa ba na irin mu'amalarta da banzayen samarinta bane.

Ya girmi hakan.

Shi yasa kawai taga babu mafita sama da rusa shi.

Ita da Hamdi kowa zero.

Mafi munin hassada kenan.

"Ki tabbatar kin je kai amarya kuma kin bibiyi me suke ciki na
an kwanakin nan.

Kin san na fa
a miki aikinsa a hankali yake ci."
"Bana son yin abin da zai sa a zargeni.

Ba wani shiri muke da Hamdi ba kuma kowa ya sani."
"Sai ki san yadda za ki yi." Ya
aga mata murya kamar wata
arsa.

Bai san bashi da wani kwarjini a idonta ba.

Yana shiru ta ce "Ban gane ba?

Wannan abu fa duk kai ne da riba.

Idan ka damu ka sa malamin da ya yi maka aiki akan Taj
in ya tura aljanu su binciko maka mana.

Mtseww"
Wayarta ta kashe ta sake buga tsaki.

"Aikin banza.

Ni za ka
agawa mur..."
iye maganar tayi cikin tashin hankali saboda ha
a ido da tayi da Siyama.

Ita kuma cikin sauri da ta karanci fuskar Ummin sai ta kama
aga
afa.

"Fitsari, fito don Allah."
Fitowar Ummi tayi tana wasiwasin Siyama taji wayar da tayi ko kuwa.

Gaba na fa
uwa Siyama ta dakata a bakin
ofa ta nemi mafita don ka
an daga aikin Ummi tayi mata wani abu idan ta san ta ji.

"Naji kina ta gunaguni da tsaki, ba dai flushing ki ka yi ya
i tafiya ba?

Kada na shiga nayi gamo."
Ba kunya Ummi ta saki fuska harda
ar dariya "shiga ki ganewa kanki" ta turata ciki.

Siyama na nuna kamar bata son shiga ta bari Ummin tafi
arfinta.

Fitsarin da ya kawota da gaske ta daina ji.

Tabbas akwai mana
isar da Ummi take shiryawa Hamdi da Taj tunda taji sunayensu.

Hankalinta ya tashi.

Har su ka tafi gidan bikin tana faman satar kallon Ummi.

Da zuwansu babu da
ewa ta nemi ke
ewa da Iyaa.

Ummi kamar an tsikareta ta tashi tayi musu la
e.

Da taimakon Allah ta sami basirar lauya zancen.

Wata maganar daban ta
auko har Iyaa za ta fara yi mata fa
an me yasa ta janyota akan shirme, sai ta
ifta mata ido.

Ganin haka sai ta kalli bakin Siyama da ta fa
i sunan Ummi iya le
e.

Wannan yasa ta fahimta.

"Iyaa za ki barni zuwa kai amarya har ango yazo?

Ni fa ban ta
a zuwa ba."
"To naji sai ki biyo yayanku don na san zai je ko don
auko Zee."
Murna ta kama yi harda rungume Iyaa.

Da wannan ta samu Ummi ta daina saka mata ido har ta sami damar sanar da Iyaa wayar da taji.

"Ban ji ance komai ba amma ko da wani abu zai biyo baya to da hannunta wallahi."
Sallamarta Iyaa tayi ta jingina da bango domin gaba
aya jikinta ya mutu.

Nauyi taji jikin yayi mata ta sulale a wajen kawai ta zauna.

Babu abin da take yi sai kiran sunan Allah da neman agajinSa.

Ha
a kowane
a da halinsa yake zuwa.

Tarbiya bakin gwargwado sun bawa
ansu.

Amma tun
ananun shekaru tan
wara Ummi ke wahalar dasu.

Bata da bakin
orawa
awaye alhakin
ata mata
a domin kuwa duk inda Ummi ta zauna ita ke shugabantar wa
anda take mu'amala dasu.

Ita ce boss mai sawa da hanawa.

Ko dai kawo
ara da wasu iyayen ke buri da alfaharin gara a kawo musu
arar
ansu akan su kai na wasu da tayi ke bibiyarta?

Duk inda Ummi ta zauna sai tayi fa
a kuma ana bincike ita ce mara gaskiya.

Kuskurenta a lokacin da suke cikin yaran yarbawa a tsakiyar Agege shi ne na jinda
i da Ummi bata ta
uwa.

Babu mai yi mata kwarjini ko ya bata tsoro.

Kana cewa kule take ce maka asss.

Wata ma
ociyarta bahaushiya a lokacin ta kan ce
"Iyaan Baballe ki daina murna.

Duk da cewa ba ma son a zalinci yaranmu to amma fa idan sun fita ya dace ki dinga addu'ar kada su ta
an kowa.

Babban abin alfaharin rayuwa shi ne kayi dace kai ko wani naka bai zama silar
unci ko zubar hawaye ko jinin wani ba.

Sannan kaima kada
an kowa ya yiwa naka.

Ko babu komai akwai baki da ido kuma su
in gaskiya ne.

Allah Ya kyauta."
Amsarta a lokacin ita ce tunda suna zaune a waje irin wannan ba za ta so yaranta su zama lusarai ba.

Wannan mata kuwa ta nuna mata cewa duk runtsi ai gara idan an je gaban Allah ka zama mai kai
ara da a kai
ararka.

Za ta koyawa yaranta su
waci kansu amma kada su zama silar rigima kuma banda zalunci da wuce gona da iri.

Manzon Tsira SAW cewa yayi kada mu cutar kuma kada mu bari a cucemu.

Hawaye ya zubowa Iyaa.

Ta
auki laifin ta
orawa kanta.

Cin zalin da Ummin da dinga yiwa Siyama ne yasa ta canja tsarin tarbiyar lokacin.

To amma
an wannan guntun sakacin da kuma halayyar fi
rar da aka haifeta sun riga sun yi tasiri.

"Allah na tuba.

Allah Ka duba min."
Wata walwala da jinda
inta duk sai su ka kau a lokacin.

Ciwon kai ta
orawa laifin hakan da Yaya ta tambayeta game da sauyin da ta gani a tare da ita.

"Kai Happiness me ya same ka haka ka kumbura?"
A madadin sallama abin da Taj ya fara cewa kenan da ya shiga
akin Kamal.

Son fa
awa Happy gaskiya yayi sai dai kuma a ganinsa fa
a a yau ba
aramin rashin adalci bane.

Babu yadda za ayi Taj ya san gaskiya kuma ya tare a gidansa a yau.

In ya yi haka kuwa ya cutar da Hamdi.

"Wai ashe kifi ne jikina baya so yanzu ni ban sani ba?

Jiya da ka kula tun a wajen dinner bani da kuzari.

Kifi na ci last kafin mu tafi."
"Subhanallahi.

Kuma Alhamdulillah tunda an gano.

We'll just avoid it don a zauna lafiya."
"We?

Kai kuma me zai sa ka daina ci?" Kamal ya tambaye shi.

"Ai ka sanni da kirki.

Ba zan so na dinga ci a gabanka ba."
Da dabara Kamal ya sauya zancen da dai yaga Taj ya yarda.

"Wai ni ya na ganka haka kamar ba wanda ya kwana gida
aya da Hamdi ba?"
"Akwai
ura fa Happiness.

Alhaji ya
allo min ruwa jiya." Ya fa
a masa abin da ya faru.

"Tab
ijam ake cewa ko cab
ijan...yanzu kana nufin ni da kai yau duk pillow za mu runguma?"
Bugu Taj ya kai masa ya goce "ta Allah ba taka ba.

In sha Allahu gadona da naka yau sai an sami bambanci."
"Salman Khan na Hamdiyya wato ana yi maka kallon salihi ashe ashe ba haka bane." Kamal ya fa
i yana yi masa dariya.

"Aure dai nayi...idan mutum yaji haushi wata asabar
in mu kai shi
akin doctor"
"Maimakon ka zo mu zanta yadda za ayi a shawo kanta tun kafin
an kai amarya su watse ka zauna tsokana."
"On a serious note kana ganin abin da take so zai samu yanzu?

Alhaji fa take so ya canja yadda yake yiwa Abba.

Bata san na fita son hakan ba ta
auki fushi dani."
Shawarwari Kamal ya soma bashi sai dai a yau ko kusa zancen ba shigarsa yake ba.

Ya riga ya san da me zai kama Hamdi a hannu.

Damuwarsa yanzu canjin da ya gani tattare da Kamal mai yawa tsakanin jiya da yau.

Happiness is hiding something.

Yana ji har cikin
argonsa.

Ko maganganun da suke yanzu yana hango pain
in da
an uwansa yake
arin
oye masa.

Dole zai yi wani abu a kai.

Kamal bai fi shi wayo ba.

Wannan asabar ta kafa tarihi mai girma a gidan Alh.

Hayatu.
Chapter 83 · 0% Book details