← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 97

Sashe 73

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya zance ki duba waya ki tsaya amsa kira kuma?"
"Sorry, na zata kiran Salwa kake nufin na duba." Ta nuna masa missed calls.
yaleta.

Nayi miki text nace na taho da Mami bata da lafiya.

Gobe zan kai ta asibiti in sha Allah."
"Subhanallah.

Shi ne muke nan?

Bari na
auko su Aisha mu tafi."
"Kada ki damu.

Salwa na gidan.

Bana so mu koma ne kiga ba
i.

A can ma ya dace na sanar dake to kuma ban sami nutsuwa ba."
Murmushi tayi masa "babu komai.

Amma Salwa fa ta ce min tana waje."
"Waje kuma?"
"Eh, kati take so in..."
"Koma ciki."
Yayi maganar yana sauko matattakalar da za ta sada shi da hanyar fita.

A waje ya ganta tsaye can gefe ta raku
e kamar wata almajira.

Duk sauron wajen nan ya tabbata ya gama cinyeta.

Ta
an bashi tausayi amma bai nuna mata ba.

"Taho mu je."
Masu gadin suna ganin shi su ka bata hanya ta wuce.

Magana ta so yi masa amma babu fuska.

Da sauri sauri ya ding tafiya sai da su ka shiga hall
in sannan ya nuna mata inda ango da amarya suke.

Taj da Hamdi ke tsaye a filin rawa ta
i motsi.

Ya ri
e hannayenta yana magana tana dariya.

Ce mata yake ko dai ta saki jikinta ko ya kama break dance yanzun nan.

"Kin gani Salwa?

Ke ya fara sani kafin Hamdiyya.

Da yana sonki da kece a tsaye a can.

Don Allah ki samawa kanki lafiya ki jira naki mijin."
"Na ha
ura Yaya.

Tafiya ma zan yi." Ta ce kamar gaske.

"Jirani a nan in fa
awa Zahra.

Nan da kamar 15 minutes sai mu tafi."
Yana barin wajen tayi gaba.

Ido rufe ta nufi inda su Taj su ke.

Sun bar rawar sai hotuna da ake ta
auka.

Tun kafin ta
arasa inda suke Hamdi ta hangota.

Gabanta ya kama fa
uwa sai ta soma karanta Ayatul kursiyyu.

Salwa na zuwa ta shige tsakaninsu ko sallama babu.

"Ya Taj ayi mana hoto."
Yadda kafa
arta take gugar tasa ko Hamdi da suke tsaye tun dazu bata yi wannan tsayuwar dashi ba.

Matsawa yayi da sauri yana a'ziyya a zuci sai ji yayi ta ri
e masa hannu.

Wani mai
o mai
o da danshin da ya yi zaton na gumi ne daga hannun nata duk ta shafa masa.

Idanun Hamdi a take su ka riki
e sai dai ganin idon mutane sai ta daure zuciyarta.

Taj na jan hannunsa ya fara jin ciwon kai Salwa sai ta sake
arfin ri
Basu san daga ina ba kawai sai wani hannun su ka ji ya kama hannayensu dake ha
e ya raba.

"Zan ci mutumcinki Salwa akan yarona kin ji ko."
A matu
ar tsorace Salwa ta dubi Inna.

Hanjin cikinta su ka ka
a.

Layar da take shirin sakawa a baki ta tauna sannan ta umarce shi da ya biyota ta sa
ule ba tare da ta sani ba.

Barin wurin tayi da wani irin sauri.

Tana tafiya Inna ta du
a da sunan Allah a bakinta ta
auki layar.

Sunan
anta ta gani
aro
aro a jiki.

Ta ha
a ido da Hamdi da taga komai ta matsa kusa da ita.

"Kama shi ku zauna.

Zan fa
awa Amma a rufe taron haka."
Kai Hamdi ta gya
a.

Ta ri
o Taj da idanunsa su ka birkice.

Bayan sun zauna tana ta tofa masa addu'a a fakaice ya dawo daidai.

Ya ce ta tashi ya kaita gida.

"Su Yaya fa?"
"Bishir zai kai su.

I need alone time with you."
"Na'am?"
"Nace muje na kama mana hotel."
"Wallahi ba haka ka ce ba." Ta fa
a a tsorace.

Dariya ya yi mata "Ki ka ce baki ji ba."
"Da wasa nake."
"Matsoraciya."
Addu'ar rufe taro aka yi.

Kowa ya tashi cikin murna da jinda
in wannan biki mai ban sha'awa.

Baballe ya
auki Zee, Safwan ya
auki Sajida sannan Taj ya tafi da Hamdi.

Ahmad da Anti Zahra kuwa mamakin duniya ne ya kama su da su ka shiga gida su ka tarar ana bushashar cin shinkafa dafaduka da farfesun kifi wanda
aya daga cikin
an Anti Zabba'u ta dafa.

RAYUWA DA GI
I 28
Batul Mamman
This page is sponsored by SAFFADEMPORIUM the world of amazing scents.

Kun san da wuya na tallata abin da ban sani ba.

To jama'a akan saffademporium ni
in jiyau ce kuma ganau.

Ido ya gani, hanci ya shaida!

Safiyya Ummu Abdoul our one and only Chairlady ta Fikra Writers Association ita ce mamallakiyarsa.

Komai na Fikra kuwa daban yake.

Akwai Raudha turaren carpet da kujeru, Naeema airfreshner, oils zafafa guda biyar, turaren kaya na maza da mata.

Khumra masu tsayawa a rai da kuma turaren wuta.

Za ku iya samunta a manhajar instagram @saffademporium ko wannan layin 07010137848.

Sayen nagari...mayar da
amshi gida!
~~~~~~~~
Kun kira
Kun turo sa
Kun zo dubiya har asibiti
Ni kuwa me zan ce da masoyan SonSo idan ba kyakkyawar addu'a da fatan alkhairi ba?

A yayinda da nake post babu abin da yake yi min da
i sama da kyawawan addu'o'in biyan bu
ata da ku ke yi min.

Wannan addu'ar ita ce babban abin dake
arfafa min gwiwar typing ko da jikina baya min da
i domin bawa bai san alkhairin bakin mutane ba.

A yau ina mai
ara godiya ga Allah da ku baki
aya.

Na sauka lafiya na kuma sami lafiyar jiki bayan aikin da aka yi min.

Ahmad Amir dani da duka ahalinmu muna godiya da karamcinku.

Nayi kewarku da sharhinku mai sanya ni nisha
i.

In sha Allah zan cigaba da posting sai dai ba zai zama kullum ba.

Sai kun
ara ha
uri saboda yanayi ya
ara canjawa.

Ga
aramin goyo, yara,
awainiyar gida da aiki.

Duk da haka kada ku sare da tunanin jira zai dinga tsaho.

In Allah Ya yarda labarin zai cigaba cikin amincin Allah.

SonSo
Idan kaga yadda ake shiga gidan Alh.

Hayatu sai mutum ya rantse gayyar mutane ce masu zuwa biki.

Nan kuwa kaf
insu ahalin gidan ne.

Babu bare ko
aya sai masu aiki.
ansa ne da jikoki.

Kuma a haka wasu ba a nan za su kwana ba.

Falon kamar ba zai
aukesu ba saboda yawa.

Da yake an gama gajiya, rabon wajen kwana kawai aka tsaya yi.

"Duk wanda ya san ya fita ya bar kaya a falo ko cikin
akuna tun wuri aje a kwashe.

Ba za ku dame mu da cigiya ba gobe." Cewar Ummukulsum ga jikokin.

Ita ce babbar
ar Yaya Hajiyayye kuma jika ta farko a gidan ta girmi Firdaus
ar ajin su Hamdi.

"Ni dai ban ga kayana da na ajiye a nan ba..."
Cigiyar da take gudu tunda ta san komai wajenta
annen za su zo nema mazansu da matansu aka fara yi daga rufe bakinta.

Kula su ka yi falon a gyare yake.

Aka tambayi masu aiki kowacce ta ce ba ita tayi ba kafin su tafi.

Abin da mamaki dai.

"To ko dai Alhaji ne?

Naga motarsa..."
are bakin mai maganar Yaya Samira tayi kafin ta kai
arshe.

"Baban namu ne zai yi muku gyaran falo don rainin wayo?"
"Gani Mugenbo shugaban marasa kirkin duniya ko?"
Muryarsa su ka ji kafin su gan shi yana fitowa daga
ofar
angarensa dake cikin falon.

A gurguje masu
uruciyar ciki su ka yi kansa saboda sabon da su ka yi dashi.
an matasan kuwa su ka shiga sunne kai.

Manyan kuma dariya su ka yi.

Su sun fi sanin baban nasu akan
an baya baya da su ka taso lokacin da ya fara fushi da Taj.

Tsaurin ra'ayinsa bai hana shi kamanta mu'amalantar iyalinsa yanda addini ya tsara bakin gwargwado a lokacin ba.

Dalilin da yasa ma ya sami damar iya tafiyar dasu akan ra'ayinsa kenan koda zu
atansu basa son abu.

Ya yi
arin toshe duk wata kafa da zata sa iyalinsa su butulce masa.

Cikin jikokin wani
an shekara biya
r zuwa ya yi jikinsa ya tsaya yana fuskantar wadda ta ce ko Alhaji ne ya kwashe kayan.

"Alhaji ba ya yin aikin mata.

Shi ba
an daudu bane."
Tsit falon yayi.

Kunya ta kama su aka rasa mai kwa
arsa.

Alhaji ya jinjina maganar musamman da ya karanci yadda kowa ya sha jinin jikinsa.

Duk sai yaji babu da
Murmushi ya yi na jin kunyarsu ya dafa yaron "kwashe kaya da ninkewa ai ba aikin mata bane ka
ai Amir.

Duk wanda zai iya saka kaya ya kamata ace zai iya ninke su."
"Laahhh, Uncle Taj ma ba
an daudu bane kenan ko?"
"Me yasa ka ce haka?" Alhaji ya tambayi yaron da sakakkiyar fuska don ya bashi amsa.

"Saboda duk wanda ya iya cin abinci shi ma ya kamata ya iya dafawa."
Mahaifiyar Amir kasa tsayuwa tayi saboda tsoron me Alhaji zai yi bayan jin amsarsa.

Ta kalli yayyenta su Yaya Kubra tana neman ceto.

Matan gidan ne
arshen shigowa dama.

Saboda haka daga baki bakin
ofa suke tsaye.

Hajiya tana kallon idon Alhaji ta yiwa Amir tambaya.

"Kai ka san waye
an daudu?"
"Eh mana" ya amsa da karsashi na yaron da aka yiwa tambaya mai sau
i "sune masu yin haka..." ya
aga hannuwa ya tafa da iska "ahayyyeee cass, rass... ko?"
Hannuwansa Bishir ya yi saurin ri
ewa ya ce "dare ya yi, ayi shirin bacci a kwanta haka nan."
Da sauri sauri su ka dinga watsewa aka bar Alhaji a tsaye cikin tunani da wata irin kunya.

Yau kuma yaro
an shekara biyar ne ya shiga sahun masu fa
a masa gaskiya?

Kuma wannan karon a gaban mutanen da yake jin ya isa dasu ta kowacce fuska!

"Alhaji na ce Allah Ya bamu alkhairi."
Da muryar Umma tunanin da ya fara ya kau ya dawo da hankalinsa ga matansa.

Hajiya ma sai da safen tayi masa ta shige yayinda Mama tayi masa tambayar ko ya gama da kwanukan abincin dare da ta ajiye masa domin ta kwaso.

Amsa ya bata sannan ya mayar da dubansa ga neman Inna don tunda su ka shigo ko tari bai ji tayi ba.

Jiran ta ce masa sai da safe kamar
an uwanta yake sai yaga bata wajen.

'Fushi take?

Me kuma nayi?
Chapter 73 · 0% Book details