← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 97

Sashe 39

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don ko kina gama secondary aka aurar dake to fa Alhaji zai yi da wajewa da mijin.
arsa dole tayi karatu kamar yadda ya yi.

Aiki ko kasuwanci ko zaman gida kuma za
in mijin ne idan ta gama.

Yadda su ka zo haka su ka tattara su ka tafi gida domin ganawa da iyayensu.

Taj kawai aka bari ya shige
akinsa ya kwanta.

Addu'a kawai yake yi Allah Ya basu ikon yi masa uzuri kada laifinsa ya yi yawa.

Zuwa Abuja already ya kama shi.

Ya ma
udurce a ransa ba zai
auki wayar Amma ba ko ta kira.

Gara su ha
u kawai ayi ta ido da ido.

Abin farinciki shi ne irin tarbar da iyayen su ka yiwa zancen.

"Nan da ku ka taho a ayari kun zo yi mana kwarjini ne?

Alhaji ya riga ku fasa
wan.

Har mun fara shirin biki." Umma ta fa
i tana dariya.

Kamal ya ce "Tunda baku yi fushi ba mu ai Alhamdulillah."
Kafin su watse Hajiyayye ta sake tado maganar lefe bayan iyayen sun tashi.

"Bishir kai zan bawa aikin bu
e mana sabon group a whatsapp.

Sai a sake maganar a gaban wa
anda basu zo yau ba.

Kada ka sako mana Taj dai kaji ko?"
Murmushi ya yi akan maganarta ta
arshe
"Zan kiyaye.

Yanzu mece ce shawararki yadda idan na bu
e kawai zan rubuta inda aka kwana sai kowa ya fa
i ra'ayinsa." Kowa ya yi na'am suna saurarenta.

"A nawa ganin ko sisi kada Taj ya kashe da sunan lefe.

Na sani cikin gidan nan babu wanda bai mori arzi
in Taj ba tun baya gari.

Mu da
anmu kullum cikin hidima yake damu.

To lokaci ya yi da za a ramawa kura aniyarta.

So nake ayi lefe na kece raini amma babu ku
in ango.

Ya ji da muhalli da sauran abubuwan da su ka sauwa
a kawai."
Abinka da gidan yawa.

Amincewar tasu ka
ai sai da ta kawo amsa kuwwa a falon.

Wai a haka ma don mata sun fi yawa.

Sun tsayar da shawarar yadda Bishir zai tsara jawabin.

Sai kuma a bawa kowa damar fa
in me zai kawo daidai
arfi.

Wasu don zumu
i tun kafin a tashi su ka fara fa
in nasu.

Ha
in kansu gwanin ban sha'awa.
akin Mama yafi kusa da inda suke zaune saboda haka taji duk abin da su ke cewa.

A zuciyarta ta raya lallai wannan zaman lafiya da
ullewar zumunci tsakanin matan gida da
a shi ne mafi girman arzi
in Alhaji.

Ba don haka ba da tuni gidan yafi
arfin duk wani zafin rai da tsare girarsa.

Yawan mutane
an Allah Ya sanya alkhairi a gidan ya mantar da Abba damuwar da ya tsinci kansa
azu a dalilin Alhaji.

Murna ake taya shi da zuciya
aya.

Cikin hikima ta Allah ya aurar da duka
ansa ba tare da tsumi ko dabararsa ba.

Amaren ne ma dai Sajida ce kawai take walwala.

Zee kuka, Hamdi kuwa ba a cewa komai.

Tana can
akin Halifa ta rufe
ofa tana fama da ciwon kai saboda uban tunani.

Dukan ne goma da
ari ba ma ashirin ba.

Ita ta sani sarai cewa ha
uwar farko ta kamu da son Taj.

Irin son nan mai shigar farat
aya.

A ha
uwarsu ta biyu lokacin ta tabbatar da gaske zuciyarta take.

Sai gashi ha
uwa ta uku da ya dace su yi musayar zu
ata ya zo ba a yadda take so ba.

Tarin
aunar da take masa take ta bi iska saboda sana'arsa.

Kuma don abin haushi bai tsaya a nan ba shi ne harda sake dulmiya mata uba cikin sana'ar da tafi tsana.

Me namiji zai yi da girki don Allah?

Ita mace da tun
uruciya ake horata da ayyukan gidan miji da girki ake farawa.

Komai manya za su ce game da aure da maganar
a'ami suke farawa ko su
are.

Sai dai kaji ana kiran tsafta, iya kwalliya, ladabi da biyayya...sannan uwa uba girki.

Shi fa girkin nan sai an
ara masa UWA UBA saboda mahimmancinsa.

Shi ne zai zo ya koya har ma ya fita iyawa.

Don tayi imani girkinsa da nata zai sha bambam.

Ya riga ya
wace abin tin
ahon da ta
amar.

To ita me za ta yi?

Shara da wanke-wanke?

Muskutawa tayi tana sauke numfashi da ta tuna rashin kunyar da tayi masa rannan da irin abubuwan da ya ce mata shima.

Ba shiri ta tashi ta zauna tana sakin murmushi.

"Da kansa ma zai sakeni tunda ba sona yake ba." Ta fa
awa zuciyarta.

Da wannan tunanin taji wani irin kuzari na shigarta.

Tunda Sajida tayi aure ai nata ba dole bane.

Salin alin za su rabu.

Haka kawai ba za ta iya rayuwar uba girki, miji girki ba.

Duniya ma sai tayi mata dariya.

Abin da tafi gudu da
i ace shi ne a tare da ita muddin rai?

Inaaaa!

Kamar ba ita ba ta fito tsakar gida.

Ana ta taron yinin Sajida.

Ita da Zee taji ana cewa tunda ko kamu ba ayi musu ba, za a jira mazajensu su fa
i lokacin da su ke so su tare.

A zuci tayi dariyar sai dai su kai Zee ita ka
ai.

Sai ta kalli Zee
in.

Idanunta luhu luhu sun kumbura.

Tayi zuru zuru ba a bu
atar likita wurin gane bata da lafiya.

Tausayin
anwar ya kama ta.

Gashi tana ganin wannan auren mai raba shi sai Allah.

Irin amincin gidajen nasu biyu da soyayyar da aka ce Baballe na yiwa Zee bata hango mata fitowa ba.

Da su ka shiga
aki, dafa ta tayi cikin rarrashi ta ce "Allah Sarki Zee.

Allah Ya sanya soyayyar Baballe a ranki.

Na kula yana da mutumci da sanin darajar mutane."
Zee ta sake fashewa da kuka "kema kin ga babu alamun auren nan zai rabu ko?

Yaya zan yi?"
"Ki kwantar da hankalinki.

Bawa bai isa ya
etare
addararsa ba.

Wani ba ya auren matar wani.

Yanayin yadda aka yi auren ka
ai ya ishe ki ishara."
Kasa
e Zee tayi tana sauraron nasihar Hamdi kafin tayi magana.

"Ke baki da matsala kenan da auren?

Kodayake me zai sa ki
i Taj?

Nima ba don abin da Ummi ta yiwa Abba a school
inku ba da na ha
ura." Wayarta ta mi
awa Hamdi "kin gani.

Tun
azu yake ta turo min message."
onnin har guda shida duk abu guda biyu su ke
auke da shi.

Na farko ha
uri Baballe yake bata akan rashin sanar da ita da neman yardarta.

Na biyu kuma yana jaddada mata ba auren alfarma bane tsakaninsu.

Sonta yake.

Kuma yana fata za ta bashi dama ya koyar da ita son shi ita ma.

Murmushi sosai Hamdi tayi.

Bata ta
a sanin soyayya za ta burgeta ba a zahiri sai yanzu.

Da alama Baballe zai yi saurin siye zuciyar Zee ta ce a ranta.

Tsarin kalaman sun taho da rarrashin da mai karatu zai ji a jikinsa.

Ai dole ma ta rabu da Taj.

Ko don rashin irin wannan text
in na Zee da wayar da Safwan ya yiwa Sajida
azu yana
ara bata ha
urin abin da ya faru.

"Allah Zee kada ki tada hankali da yawa.

Na san irin auren nan babu da
i.

Amma ki godewa Allah da mai sonki aka ha
aki.

Kuma kina ganin yadda Abba da Yaya ke ta murna.

Yawan kukan zai sa su ji babu da
Sajida ce ta shiga
akin a lokacin.

Ta kalli
annen nata tana murmushi.

"Su Hamdi malaman aure.

Irin wannan hu
uba haka?

Ko dai dama soyayya ku ke da Ya Taj bamu sani ba?"
Idanun Hamdi hango mata Taj su ka yi a gaban tukunya sai taji tsigar jikinta na tashi.

Wannan aure ba da ita ba.

Ba dai za ta iya labartawa
an uwanta niyyarta bane saboda kada yanzun nan su kaita gaban iyayensu.

"Gani nayi an riga an
aura.

Gara mu ha
ura kawai.

Kukan ciwo zai sa mata."
"Da gaskiyarki.

Amma ni ke ce damuwata.

Jiya da baki san da naki auren ba sam baki da damuwa sai tamu.

Yau kuma an
aura naga kin yi saurin ha
ura kamar ba ke ce ki ka suma ba
azu...

Don Allah mene ne tsakaninki da shi?"
Da Sajida da tayi tambayar, da Zee idanu su ka zuba mata.

Tana son gilla musu
arya amma ta rasa wadda za ta fi dacewa.

Allah ne Ya taimaketa
an matan danginsu su ka shigo
akin ana tsokanar amare.

A dalilin Abba dukkaninsu basu da wasu
awayen kurkusa da su ke shawara dasu.

Su ne dai
awayen juna sai cousins
insu.

Gabanin Magriba da ba
i su ka sarara ne Hamdi ta shige
uryar
akinta da wayar Sajida da tata a hannu.

Numbar Taj ta kwafa ta gama karanto addu'o'in neman nasara ta kira shi.

"Happy kana ganin ka kyauta kuwa?

Duk fa irin yadda Yaya ya damu da mu ita ma Salwa jininsa ce."
Kamal ne yake yi masa wannan tambayar a yayinda yake shiryawa zai je
aukan Abba su je wurin Alhaji.

Yadi ne ya saka mara nauyi ruwan bula mai kyau.

Rigar tasa ka
an ya rage ta
arasa gwiwa.

Hannunta kuma ya
an zarce gwiwar hannu ka
an.

Aikin wuyan da aljihu da aka yi ruwan madara ba mai yawa bane.

Hula ya
ora a kansa lokaci guda ya zama kamar ba shi ba.

Ya yi kyau sosai.

Sai da ya gama fesa turare sannan ya juya ya fuskanci Kamal.

"Ya kake so nayi da ita?

Me ma nayi mata?

Banda na bi shawararka ka san Allah da ko text
in da take yawan yi min ba zan kula ba."
"Na sani.

Amma yanzu da ta shige
aki tun
azu ya dace ka kirata ka
an rarrasheta."
Taj ya ware idanu "in yi me?

So ka ke tayi zaton aurenta zan yi?

Gaskiya Happiness ka rage sau
in kai.

Zai iya kai ka ya baro."
"To ko Yayan ka
an yiwa magana mana.

Sharewa kamar baka san komai ba fa ba daidai bane.

Please." Kamal ya ce da damuwa.

Baya son rigima irin wannan ta cikin gida.

Su duka
annen Ahmad ne.
Chapter 39 · 0% Book details