← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 97

Sashe 12

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ummi ta ce ki kwaso mata kayanta idan ba haka ba duk makarantar nan kowa sai ya gani"
"To" ta amsa da sauri tare da du
awa ta fara
aukar kayan.

Yarinyar ta yatsina fuska "no, ta ce da
ai za ki
auka."
"To" Hamdi ta sake amsawa da rawar jiki.

Banda akwatuna biyu akwai manyan ledoji uku.

Haka tayi sawu biyar tana zuwa hostel
in su Ummi.

Bata ganta ba sai da ta kai ledar
arshe ta sameta zaune akan gadonta.

"Ina za ki baki jera min ba?"
Cak ta tsaya ta dawo da sauri ta jera kayan a kwanar Ummin.
akin su ka zuba musu ido suna ganin ikon Allah.

Bayan ta gama a gadarance Ummi ta ce mata gobe ta zo da wuri ta
ebo mata ruwa.

Ta amsa kawai ta fita.

Da ta fita ko ganin hanya bata yi saboda hawayen da ya cika mata idanu.

Da ha
a hanya ta isa inda sauran kayanta su ke ta kwaso.

An soma yayyafi ga iska mai
arfi.

Saboda haka akwatin da jakar sun yi bu
u-bu
u.

Zuciyarta a
untace ta tafi nasu hostel
in.

Ajiye kayan kawai tayi ta hau gado ta dun
ule jikinta tana kuka.

Nan da nan wurin ya cika da mutane ana tambayarta me yake faruwa amma ko
ago kai bata yi ba.

Sai wata ce da taga yadda ta dinga
iban kayan Ummi ta basu amsa.

"Wannan hutun da alama ita Ummi Maje za ta takurawa."
Alhini da tausayi su ka dinga nunawa bayan ta fa
a musu me ta gani.

Abin bai yi musu da
i ba domin kuwa Hamdi bata rigima.

"Lallai Ummi bata da sauran rabo don ko mu masu baki da take zalinta bamu yafe ba balle mara baki irin Hamdiyya."
Wadda tayi maganar tana rufe baki wata ma ta kama.

Su ka taru su ka gama
ebe mata albarka (mu guji irin wa
annan laifukan da bama
aukarsu a bakin komai.

Babu wani ha
i abin rainawa) sannan su ka watse.

RAYUWA DA GI
Batul Mamman
Sanarwa
In sha Allah post zai dinga zuwa ranakun Litinin zuwa Juma'a.

Ummi dai baje kolin rashin mutumcinta tayi akan Hamdi har ya kasance sauran
alibai suna samun sararawa.

Kowanne aiki Hamdi, kowacce bola da shara ma ita
in dai take nema.

Wanki harda na su pant ita take mata.

Su
ebo ruwa da kwafar note dama tuni ta daina saka wasu.

Kuma ko da wasa Hamdi bata ta
a fa
in wata kalmar neman sau
i ba.

Komai Ummi ta ce 'to' ce amsar.

Ita dai burinta ta bar makarantar ba tare da kowa ya san ko waye mahaifinta ba.

Da yake a cikin hutun da su ka aka yi jarabawar JAMB, yanzu
an kwanaki su ka rage kafin a fara WAEC.

Kowa ya du
ufa da karatu ba ji ba gani.

Wa
anda basu
auki karatun a bakin komai ba irinsu Ummi kuwa shagalinsu suke yi.

Ranar wata laraba da safe aka tashi makarantar babu ruwa.

Abin ka da lokacin zafi.

Tsakanin April da May a garin Kano dama ba a cewa komai.

Rijiyar makarantar mai dama dama ba a samun komai sai wani ruwan dau
a wanda zai iya sati bai kwanta ba.

Kowa ya shiga damuwa don ko darussan aji ba a shiga ba.

Ga
an karen zafi ana ta zufa.

Principal tun safe ta fice sai wajajen shabiyu ta dawo da tankokin
ruwa har bakwai a bayanta.

Yara sai murna.

Aka umarci malamai da su kula da
aliban wajen bin layi ta yadda kowa zai samu.

Sannan an ja musu kunne babu mai
ar ruwa sau biyu.

Kuma bokiti biyu ka
ai za a cika wa kowa saboda kada wasu su rasa.

Layi layi aka jera
aliban na ajujuwansu.

A sammakon Hamdi ita ce ta talatin da hu
u a layinsu.

Kafin a zo kanta rana ta gama dafa ta.

Ana zuba mata taji wani sanyi ya ratsata.

Ta
auki bokatan hagu da dama ta wuce
aki.

Tun kafin ta isa bakin matattakalar hostel
in ta hango Ummi da
awayenta a zaune kan dandamalin wurin suna ta hayaniya ana dariya.

Fuska a ha
e Ummin ta tarbeta da ta
arasa.

"Kin da
e a layi gaskiya.

Ke ko irin turereniyar nan baki iya bane?"
Take takenta Hamdi ta gane sai dai ta riga ta yiwa kanta al
awarin ko me zai faru ba za ta bata ruwan da ta wahala wurin samu ba.

Jikinta gaba
aya
ayi yake yi mata.

Ga
ishi ga yunwa.

"Ban iya ba."
"Mtswww, wuce ki kai min ruwan in samu nayi wanka kafin a gama abinci."
Wata za
ura ta ce "Ummi kin ce fa nima za ki sa ta
ebo min."
"Ki bari ta juye min mana." Ta cewa wadda tayi maganar a wula
ance.

Juyawa Ummi tayi taga Hamdi ta ajiye bokatan ta sar
e hannu a
irji.

Rai a
ace ta ce mata "
auki mu tafi mana."
"Ki je ki bi layi don babu wanda za a zubawa sau biyu.

Har ticking suna ake yi."
"To sai ki san yadda za ki yi.

Ni ki wuce ki zuba min zafi nake ji."
Hamdi ta rasa daga ina take jin wani
warin gwiwa kawai ta ce "naga kamar baki gane ba.

Wannan ruwana ne.

Ki je ki
ebo naki."
Wata uwar shewa Ummi tayi tana dafa
irji "dani kike?

Har kin manta abin da zan iya yi miki idan ki ka
ata min rai?"
Tunawa da alamun mutumcin su Iyaa tayi sai take ganin kamar duk haukan Ummi ba za ta fitar da bidiyo
in ba.

"Kin da
e baki nunawa duk makarantar nan waye ubana ba."
"Kanbu, dani kike?" Ummi ta fa
i cike da mamaki.

Sai kuma ta fasa fa
an ta ce
awayenta su
auko bokitin.

Suna kai hannu Hamdi ta tare kayanta ta hanyar dur
usawa a gaban bokatan ta tarosu da hannuwanta.

"Wallahi ba zan baki ruwan nan ba."
Mamakin me Hamdi ta taka a yau ne ya kama Ummi.

Taga gara ta nuna mata idan tace za ta yi abu lallai babu fashi.

Waya ta
auko daga aljihun wandonta na kayan prep.

Gaban Hamdi na fa
uwa amma idonta yau ya
ashe.

Tana ji kamar kowa muryar Abbanta ta
arade wurin.

Kan kace meye wannan
alibai sun taru suna jin bayanin Ummi na cewa wannan zu
iyar muryar fa ta mahaifin Hamdiyya Habib ne wanda ya kasance
an daudu.

Aka dinga tururuwar le
a bidiyon ana cewa ga kama nan.

Kallon Hamdi aka fara ana zun
e tayi kamar bata jinsu duk yadda ranta ke suya ta du
a za ta
auke ruwan sai taji Ummi tayi wata maganar da ranta ba zai iya
auka ba.

"Mamanta kuwa cangal ce mai
afa
aya da kwata" ta cilla
afa
aya ta ban
aro
irji
ari
aya "idan tana tafiya sai ka rantse Awilo ne zai yi rawar wa
arsa."
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

Hamdi ta iya fa
i don dariyar da aka tuntsire da ita a yayinda Ummi ke kwatanta tafiyar Yaya ta mugun ba
anta mata rai.

Sakin bokiti guda tayi ta
aga
ayan da hannu biyu ta juye shi tas akan Ummi.

Kowa kuma sai ya bar abin da yake yi aka tsaya kallo.

Ummi bata gama dawowa hayyacinta ba Hamdi ta cakumi wuyanta ta soma kai mata duka.

Dambe sosai ya
arke a tsakaninsu inda Hamdi ta dinga tumurmusata da
asa.

Tunda kayanta a ji
e suke sai jikin ya yi futu-futu kamar an tonota daga rami.
awayen Ummi da suka ji ta fara neman ceto ne su ka
waceta sannan su ka yiwa Hamdi taron dangi.

Mutum uku ne su ka danneta a
asa suna duka.
an hostel
insu na ganin haka su ma suka saka hannu wurin kai mata
auki.

Wurin ya hargitse aka dinga
arin ruwa ana doke doke.

Prefects ma basu iya yin komai ba sai malamai da aka kira.

Duk wadda take waje a lokacin da
an kallo da
an dambe aka tasa
eyarsu sai ofishin Principal.

Baiwar Allah ji tayi kamar ta fasa ihu da taga yadda yaran nan su ka
annatar da ruwan da ta wahala wurin nemowa.

Ba'asi guda ta nema shi ne su waye su ka fara fa
an.

Aka nuna Hamdi da Ummi.

Ta kar
i bulala kuwa ta zane musu jiki ta zauna tana haki.

Mataimakinta ne ya kar
i shari'ar saboda abin mamaki yau Hamdi yake gani kuma wai ita ta fara fa
an.

Duk yadda aka yi a sanin da ya yiwa shai
anci na Ummi ya san laifin ba zai wuce nata ba.

Masu tarar aradu da ka ya ha
a da displine master sannan ya zauna sauraron abin da ya ha
a yan matan.

Ummi ta kitsa
arya da gsskiyarta ita kuwa Hamdi ko tari bata yi ba.

Mutumin nan ya ka
a ya raya amma
ememe ta
i magana.

Sai ajiyar zuciya kawai take saukewa.

Waje ya tura su ya tattauna da malamai.

Kowa ya riga ya san halin Ummi da Hamdi.

Duk da haka tunda Principal tayi rantsuwa ya ce a dubo lambobin iyayensu a sanar dasu ana nemansu washegari Juma'a.

Duk wanda bai zo ba
arsa ba za ta yi jarabawar da za a fara ranar litinin ba.

Hamdi a yau ko a jikinta.

Ta riga ta sanyawa zuciyarta
oyon uba bashi da wata fa'ida.

Da tun farko ma an san shi Ummi bata isa tayi amfani da wannan damar akanta ba.
angaren Ummi ne dai hankalinta ya nemi gushewa.
aryarta ce za ta
are nannda
an awanni.

Kiran iyayenta ba ba
on abu bane ko ka
an.

Inda gizo ke sa
ar dai shi ne wani Sugar Daddy
inta ne yake zuwa a matsayin kawunta.

Wai ita marainiya ce.

Baba Maje da ke kawota kuma yaron kawun nata ne.

Har ila yau baban nata yana kar
ar wayarta duk ranar komawa makaranta tun da aka bata wayar.

Wadda take amfani da ita ba tare da sanin hukumar makarantar ba wata
awarta take bawa ajiya.

Babbar waya ce da wani saurayin daban ya saya mata.

Tun kafin a dawo taje gidansu yarinyar ta tura wannan bidiyo
in da ta yiwa Abban Hamdi.
Chapter 12 · 0% Book details