← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 97

Sashe 57

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dinga juye juye akan gado har Allah Ya kawo masa bacci.

Da gari ya waye ya
an ji sau
i amma ba sosai ba.

Ya lalla
a ya tafi boutique
insa ya shige office ya kwanta.

Idan yana gida damunsa za ayi da tambayar ko lafiya.

Nan kuwa yaransa ba za su neme shi ba sai ya zama dole indai ba da kansa ya fito ba.

Yana kwance cikin ciwon nan ne Hamdi ta kira shi.

Ya sani sarai ciwon wasa ba zai sa Taj nemansa ba.

Haka ya tashi ya lalubi mu
ullin motarsa.

Kafin ya kai
ofa amai ya taso masa.

A cikin office
in ya fara da
yar ya
arasa toilet.

Tun yana yi a tsaye sai da ya yi zaman dirshan a
asa.

Kusan minti sha biyar kafin yaji dama-dama ya tashi yasa tissue ya goge duk inda ya
ata a office
in sannan ya fita.

Wayar Taj ya kira domin yaji jikin tare da bashi ha
uri akan rashin fitowa da wuri.

"Ya naji muryarka a sha
e?

Allergy
in ne?

Me ka ci?" Taj ya manta da ciwonsa ya tashi zaune da kyau.
warewa nayi.

Baka ganni ba harda amai saboda tari."
Komawa Taj ya yi ya sake kwantar da kansa "ai ka
i jin magana akan shan abu kana surutu."
"Ba za ka yi min sannu ba to?"
"Sannu ba don halinka ba."
Kowannensu ya yi maganar cikin dauriyar ciwo.

Su ka yi sallama Kamal ya cigaba da tu
i.

Yana son fa
awa Taj lalurarsa amma mene ne amfanin sanya shi cikin damuwa?

Da nasa ciwon ya
arasa gidan Abba ya
auke shi.

A soro ya yi sallama da Hamdi don ya ce turarenta hijab
in da ta
ora ma bai hana shi mara lafiya ji ba.

"Allah Ya baka lafiya."
"Amin."
"Za ka kirani idan kun gama da asibitin?" Tayi magana tana kallon
asa.

"Dole na.

Ko don na baki ha
uri."
urin me?"
"Wanka da shirin tarbar maigidan da ki ka yi mana.

Ni kuma nazo na ha
aki da jinya.

Maimakon na yaba miki da kyau tunda babu kowa a gidan.

Mtswww, Allah ban jida
i ba."
"Allah Ya shiryeka." Ta tura shi.

"Ya shiryemu dai Hamdi.

Ni dake idanunmu iri
aya ne."
"Wane iri?" Ta tambaya don bata gane ba.

"Zan miki bayani a gaba."
Motar Kamal ya shiga su ka tafi asibiti aka yi masa allura da bashi magani.

Bai ga komai a tattare da Kamal ba domin ya daure sosai yana danne nasa ciwon saboda yadda yaga Taj.

Da wuri Yaya Kubra tayi clearing schedule
inta ranar litinin.

Ta tabbatar bata da sauran aiki na gaggawa a asibitinsu sannan ta fita domin ganawa da Dr.

Mubina.

Hankalinta a
an kwanakin da su ka gabata sam ba a kwance yake ba.

Tana dai daurewa ne kawai saboda kada kowa ya gane.

Ta dai sakawa Kamal ido fiye da koyaushe.

Duk wani motsinsa tana bi.

Zuwanta biyu Happy Taj ma tana siyayyar dole duk don ta sami ganinsa.

Bata son kiransa ta
ora masa wahalar zuwa gidanta ko asibiti.

A reception ta bada katinta ta ce don Allah a mi
awa Dr.

Mubina idan tana nan.

Matar ta kar
a ta duba.

"Tun
azu ta ce idan kin zo a nuna miki inda take.

Bismillah."
Babu mamaki ko ka
an a tare da Mubina da zuwan Yaya Kubra.

Wannan yasa da ta shiga office
in ta ce ,
"Allah Yasa ban
ata miki lokaci ba.

Naga kamar jirana kike."
"Na san yanayin aikin.

Ina da niyyar jira har zuwa dare ko za ki zo." Ita ce amsar da bata sannan su ka gaisa.

Yaya Kubra ta
ora ledar kwalin maganin akan tebur tana fuskantarta.

"Na sami sa
onki.

Amma mene ne dalilinki na breaking doctor-patient confidentiality?

Laifi ne babba kin sani."
Murmushi Mubina tayi "domin mu ceci Kamal kamar yadda ki ke tunani.

Sannan ban karya doka ba.

Magungunan ba a same su a nan ba shi ne nayi masa order daga India.

Da su ka iso ni bana nan ina wajen conference a Ghana.

Za ki iya duba date
in.

Na kira shi bana samu.

Kuma ban san numbar kowa nasa ba, sai sunanki da na asibitinki.

Shi yasa na tura."
"Kema kin san dai ba zan yarda da wannan zancen ba."
Mubina ta dage ta
i bari fuskarta ta nuna ta san bata kyauta ba.

Dags
arshe dai ta ce,
"Tura miki kawai nayi.

Ban san za ki bu
e ba."
Dariya Yaya Kubra tayi.

Da alama babu yadda za ayi ta kama wannan matashiyar likitar da laifi.

"Ki yi min bayanin ciwon Kamal baki da baki ba abin da nake zargi daga magani ba."
oda ce.

Duka biyun.

Idan ciwon ya sake tashi sai dai mu fara dialysis.

Shekara guda kenan yana fama.

Kusan duk wani magani da na sani mun gwada.

Amma they are barely functioning." Mubina ta fa
i da rawar murya.

Jikinta har yafi na Mubina rawa Yaya Kubra ta ce "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

Doctor kun ta
a shawarta yi masa transplant?"
"A nan matsalar take.

Ya ce min shi ka
ai ne mai rhesus negative blood group a gidan.

Dalilin da yasa ya
i sanar da kowa kenan."
"Wannan ai ba dalili bane.

Ya ma aka yi shi ka
ai yake da negative?

Wane blood group ne?"
Yaya Kubra tayi maganar cikin hawayen da bata san ya sauko ba.

Ita da ta zo da niyyar jin ko kidney stone ko wani infection.

Bata zata abin ya kai haka ba.

Kamal, Happiness
insu da ciwon
oda wadda take gab da daina aiki gaba
aya.

Kukan da ita Mubina tayi a lokacin da ta hanga taga kamar mafita ta
arewa masoyinta, shi yayarsa take yi.

Abin da yake faruwa babba ne.
oda ba abar sayarwa bace.

Sannan ko a cikin gidan su mutum ba fa kowa ne zai iya yarda a cire tasa a bawa wani ba.

Duk da tana da ya
inin da wuya aje da maganar gida ba a sami kaso fiye da saba'in a shirye da su bayar ba.

A ina za su sami
oda?

A dangi?...abin da kamar wuya.

Sannan zancen cigiya ma bai taso ba.

Hukumomin tsaro da na lafiya basu yarda wani ya saka ku
i ya sayi wani
angare na jiki ba.

Faruwar haka zai sa mutane su dinga sayar da organs
insu da zarar sun shiga matsala da ma abubuwa daban daban marasa da
i da za su iya biyo baya.

"Ki kwantar da hankalinki mu yi magana doctor."
A gigice Yaya Kubra ta ce "ta ina hankalina zai kwanta?

Iyayenmu duka na tabbata jininsu positive ne.

A ina ya sami negative don Allah?"
Bayanin wannan ru
ani Mubina tayi mata kamar ba likita ba don hankalinta na neman gushewa.

Da gaske likitoci kamar kowa in lalura ta waji nasu ce su ma ba sa ji, basa gani.

Group
in jini daban kamar yadda ta sani guda hu
u.

A, B, AB da O.

Sannan yana
auke da wani sinadari da ake kira rhesus.

Idan akwai sai wannan blood group
in ya zama positive (+), idan kuma babu sai ace negative (-).

Abin mamakin shi ne da group
in jinin da rhesus
in duka a wajen iyaye ake gada.

Uwa za ta iya zama A+, uba kuma O-, sai su haifi
a O+.

Ya gaji group a wajen uba, rhesus a wajen uwa.

Wannan shi ne normal.

To a case
in Kamal an wayi gari shi ka
ai ne yake
auke da jini rhesus negative.

Wannan yana nufin
aya daga cikin iyayensa yana
auke da alamun rhesus negative
in a
oye.

Tunda kowanne abu na jikin
an Adam ana samu daga uwa da uba a tare, wanda yafi
arfi ya nuna kansa (domimant gene).
ayan kuma ya zama a
oye (recessive gene).

To wannan
oyayyen zai iya bayyana a jikin
an da za su haifa a matsayin mai
arfi.

A ta
aice dai
aya daga cikin iyayen Alhaji ko Hajiya suna
auke da rhesus negative gene. (Batul ba likita bace.

Wannan bayani na samu shi ne bisa bincike da nayi.

Idan yaci
aro da
a'idar likitanci don Allah ayi min uzuri.

Littafin fiction ne dama.)
"Allah Sarki Kamal.

Nagode Doctor.

In sha Allah zan yi cigiya a family
in Hajiya.

Don da ace daga
angaren Alhaji ne tabbas Kamal ba zai kasance shi ka
ai ne mai wannan blood group
in ba."
"Cigiya kuma?

Doctor Kubra please ki duba abin a matsayin likita.

Anya ya kamata ki fara bin dangi kina neman mai bashi
oda?"
"Zuba ido zan yi ciwo ya cinye shi?

Me yasa ki ka fa
a min in ba don haka ba?"
"Saboda mu nemi mafita amma ba da garaje ba.

Cigiya zata iya zama laifi a shari'ance.

Musamman idan mai bayarwar ya nemi a biya shi."
Duk ta inda Yaya Kubra ta
ullo sai Mubina tayi mata nuni da illar hakan.

Iyayensa ya kamata su sani.

Shi kuma Kamal ya
i amincewa saboda a ganinsa tayar musu da hankali zai yi.

Ga ciwo, ga ku
i amma babu mai iya taimakawa.

Damuwar da za su shiga sai ta ninka ciwon nasa.

"Da na sani Taj na fa
awa." Mubina ta ce da taga Yaya Kubra ta manta da dokokin aikin nasu.

Yadda zai sami lafiya kawai take nema.

"Rufa mana asiri.

Gara kowa yaji akan Taj.

Ina miki rantsuwa da sai yafi Kamal jinya.

Those two are like one soul in two bodies."
yar Mubina ta sami kan Yaya Kubra.

Sun tsayar da magana akan cewa za ta zo ranar next appointnent
insa.

Daga nan sai su san abin yi kuma.

Yadda Mami ta so ko ana muzuru ana shaho haka Alh.

Mukhtar maigidanta kuma uba ga Salwa yake yi.

Ta zauna ta kalallame shi da
arya da gaskiya aka son da Salwa take yiwa Taj.

"Mu ne da alhakin sama mata farincikinta.

Idan ba haka ba Allah muna gab da rasata."
"Ni uban mace ki ke so in kira tsohon mijinki in ro
i ya sa
ansa auren
ata?
Chapter 57 · 0% Book details