← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 97

Sashe 77

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai yanzu yake nadamar
auron bakinsa.

Sunan Happy yake kira a zuci domin shi ne zai iya bashi shawarar yadda za su fasa
wan a gida.

Shirun da ya yi ya sanya Mubina yin gyaran murya.

"Bari na baka wuri ka shirya."
Da sanyin jiki ya yi mata magana kafin ta fita.

"Kada ki tafi Mubina.

Bana son zama ni
aya don Allah.

Not when you just told me I don't have much time left."
Tsayuwa tayi amma bata ce komai ba har ya mayar da rigarsa ya sanar da ita.

Ta juya a hankali ta dube shi.

Idanunsa sun ka
a sun yi ja sosai.

Sai wata
walla da take barazanar wanke masa fuska.

Koma mata
an yaro ya yi mai jiran rarrashin uwa.

Komai nata da ya danganci juriya a take ya
wace.

Jikinta ya kama rawa a yayinda ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai.

"Yaya za ka yi da ha
ina da ka
auka Kamal?"
Idanunsa ko bu
ewa da kyau basa yi ya
aga kai ya kalleta.

"Me nayi miki kuma?"
"Ka san baka da burin rayuwar duniya me yasa ka bari na kamu da son ka?

Me yasa kake azabtar dani ta hanyar nuna min kanka a yanayin ciwo amma ka
i bani ha
in kan nema maka magani?"
"Ashe kina sona..." Kamal ya tattaro
arfin hali yayi murmushi gami da komawa ya kwanta "kinga har naji
arfi a jikina.

Bari na huta sai na tafi."
Wani irin kallo Mubina tayi masa "ka san
arfe nawa kuwa?

Ko ka manta za a sake allurar
arfe shida na asuba?"
"Kada ki damu zan dawo in sha Allahu."
Mamaki ya bata.

Ta zata gaskiyar da ta fa
a masa mai ban tsoro za ta sa ya soma tunani da yin abin da ya dace.

Rai a
ace ta ce
"You are simply unbelievable!

Me za ka je yi a gidan bayan dare ya raba?

Kai da ka zo a sume ne kake zancen zuwa gida."
Ya za ayi ya manta?

Dama dauriya ya dinga yi a wajen dinner
in.

Taj na fita da Hamdi ya kirata.

Lokacin ta kusa gida ma tunda ita ma taje dinar.

A asibiti su ka ha
u sai dai kafin ta iso ya suma a mota.

Wurin parking ta dinga dubawa har ta gano motarsa tasa aka
auko shi.

"Zan fa dawo da gaske.

So nake in sanar da Alhaji lalurata.

Ko ba haka kike so ba?"
"Kada ma ka fa
a mana.

Ni ina ruwana?

Na daina damuwa."
Kamal ya yi murmushi "to wallahi ki canja taku don soyayya babu nunawa juna damuwa bata da armashi.

It won't even last."
walla ta goge da
asan mayafinta ta harare shi "kai
in lasting zaka yi balle soyayyarka?"
"Ahhhh, abu na Allah...ki ka san ta inda sau
i zai zo min?

In warke muyi aure.

Duk shekara na raka ki labour room
in can naku na sama."
Ba lokacin wasa bane amma sai da Happiness ya sanyata murmushi sannan su ka fito daga
akin.

Alhaji bai yi mamaki ba da bincike ya nuna banda jinin Taj da ya hau babu wani abu da likitan ya iya gani da zai zama silar ciwon kai mai tsanani irin wanda yake fama dashi.

Ya duba ido da kunne har ma ha
oransa domin ciwonsu kan jawo ciwon kai amma duk
alau suke.

Kuma ya ce yana bacci.

"To ko stress
in biki ne?" Likitan ya tambaya da damuwa.
ewa tsaye Alhaji yayi "kada ka damu doctor.

Kawai ka rubuta masa pain reliever mu tafi." Idan sihiri ne ba a asibiti za a gani ba.

Rubutawar ya yi su ka fito.

Taj yana mai
ara jin mamakin mahaifin nasa.

Yadda yake abubuwa kai ka ce babu abin da ya ta
a faruwa a tsakaninsu.

Kowa tasowa yayi da ganinsu banda Hamdi.

Da farko tana ganin
ofar ta bu
e ta tashi da sauri.

Tana ha
a ido da Alhaji sai ta koma ta zauna ta kama kallon gefe.

Kama kanta tayi don kada ya fa
i abin da zai sake damunta.

Taj
in ma
in kallonsa tayi wanda Alhaji ya karanci yadda hakan ya dame shi.

Da alama kasancewarsa a wajen ce kawai ta hana shi
arasawa gareta.

Ita ma kuma dauriya ce da taimakon fushin da tayi tun a hanya ya hanata ko da satar kallonsa.

Murmushi Alhaji ya yi ba tare da ya sani ba.

Wannan yarinya anyi rigimammiya.

Wato ita nan maganarsa ce har yanzu ba ta ha
ura ba.

'To ai shikenan.

Na san maganinku daga ke har Taj
in.'
"Abba zo ka kaisu gida sai ka taho da motar Taj
in."
Zumbur ta mi
e tayi gaba.

Taj ya auna yaga idan ya bari ta fita fa akwai matsala a gaba.

Kai ya
an sunkuyar ya
i kallon Alhaji da Abba ya ce,
"Ina zuwa Alhaji."
"Ina za ka je?"
Hamdi da ta kusa
ofa kuma taji maganganun da suke yi sai ta tsaya cak.

Kuka kawai take son yi.

Wato umarnin kada ya bita aka bashi yanzu kuma.

Bata juya ba ta sake
aga
afa ita ma Alhajin ya tsayar da ita.

"Kema ina za ki je a daren nan kike
arin fita ke ka
ai?"
"Tafiya za mu yi Alhaji.

Dare ya raba sosai." Abba Habibu ne ya bashi amsa.

"Ai na san daren ya yi shi yasa nace Abba ya kai ku gida kai da wanda ya tu
o motar."
Ba shiri Hamdi ta juyo.

Taj ma dai Alhajin yake kallo.

"Ku kuma ku wuce mu tafi gida."
"Mu su wa?" Taj ya yi tambayar a gaggauce.

"Kai da matarka mana.

Ko kana tunanin a daren nan zan bari ka tafi gidan Ahmad ka tashe su?" A zahiri kuwa baya son yaje ne ya sake ha
uwa da Salwa ta
ulla wani abin.

Bai ga abin da zai sa ya bar Taj ya kwana nesa da gida ba yau
innan.

Furucinsa Halliru mai tu
o mota ne ka
ai bai bawa mamaki ba tunda bai san komai ba.

Fuskokinsu su duka abin dariya don dai ma Alhajin yana gudun raini a gaba da ya dara.

Idanun Hamdi
ara girma suka yi.

Na Abbanta kuwa da Taj sun yi micimici kamar ya ce zai yanka wani.

Taj baya son saka rai a banza sai cewa ya yi "ban taho da mu
ullan gidan ba."
"Naku gidan ba da gayyar mata ku ke shigarsa ba?" Alhaji ya ce yana tafiya har ya wuce Hamdi ya fita.

Bata iya tafiya ba sai da Taj ya
arasa inda take ya ri
o hannunta.

Suna zuwa bakin
ofa ta
wace hannun ta fito.

Abba Habibu dai ya shiga duhu dole ya nemi
arin haske.

"Alhaji ina za su je ne?"
"Gidana." Ya amsa kai tsaye.

Hankalin Hamdi sai yanzu ya yi asalin tashi.

Ta dubi Abbanta tana girgiza kai kamar
zata cire shi.

"Bishir mu
ullin motar yana wajenka ko?"
Nuna masa mu
ullin ya yi shi kuma kai tsaye ya yi gaba ko jiran wani ya yi magana bai tsaya yi ba.

Ya sakar musu bomb ya barsu da haya
"Abba don Allah ba za ni ba" cewar Hamdi harda hawaye.

Taj kuwa kai ya girgiza masa cike da murna "Abba ku tafi sai da safe."
"A yi haka?"
"Abba kana ji fa Alhaji da kansa ya ce in zo gida na kwana ba ro
a nayi ba." Ya kalli Hamdi, kallo na girmamawa "albarkacinki naci.

Wallahi albarkacin aurenki ne.

Nagode Hamdi."
Shi ma Abba sai lokacin ya fahimta sosai.

Ya ri
e hannuwan Taj su ka yiwa juna murmushi na farinciki.

"In sha Allah daga yau waccan magana sai dai a tarihi kuma.

Allah Ya cigaba da toshe dukkan
araka."
"Amin Abba.

Nagode.

Nagode" Ya amsa da murmushi.

"Ni fa ba zan..."
"Bi mijinki ku tafi Hamdi.

Sai da safe." Abba ya katseta da sauri.

Yana gama magana yabi bayan su Halliru.

Aka barta da Taj.

Hannunta ya kamo kada su yiwa Alhaji laifin barinsa jira.

Suna zuwa su ka samu ya shiga gaba.

Su biyun su ka zauna a baya.

Motar tayi tsit.

Alhaji ne ka
ai yake jin wani irin farinciki na kasancewa tare da Taj a wannan yanayin.

Ribas Bishir ya yi idanun Alhaji su ka sake sauka akan motar Kamal.

Da sauri ya ce da Bishir ya tsaya.

Bai yi musu magana ba ya fita ya koma cikin asibitin.

Shaf ya manta yaga motar lokacin shigarsu.

To me yake yi a ciki basu gan shi a reception ba sannan bai neme su ba?

Mota kuma tasa ce babu tantama.

Yana shiga ciki ya nufi wajen Receptionist
in sai ga Kamal da Mubina suna fitowa daga koridon inda Emergency room yake.

"Kamal?"
Hantar cikin Kamal sai da ta ka
a da ya tabbatar Alhaji yake gani.

Ya yiwa Mubina kallon tuhuma sai tayi saurin girgiza kai.

"Baka da lafiya ne?" Alhaji ya tambaye shi.

"A'a.

Dawo da ita nayi daga wajen dinner."
A tsanake Alhaji ya kallesu sannan ya ce "Me ka zauna yi to?

Naga motarka tun zuwanmu kusan awa guda da ta wuce."
Kamal ya rasa
aryar da zai gilla sai Mubina ce ta
wato shi saboda yadda taga ya gama ru
ewa.

"Emergency case na samu Baba.

Sai yanzu na fito."
"Allah Ya bada lafiya.

Amma duk da haka da shi sai ya tafi gida tunda dare ya yi."
uri Kamal ya bashi.

Yana shirin tambayar waye babu lafiya Alhaji ya sake yi masa tambaya.

"Me ma ya zaunar da kai?

Ko akwai ala
a a tsakaninku da ban sani ba?"
an daga aikin Alhaji kenan.

Fa
in magana kai tsaye ba tare da
oye
oye ba.

Mubina ji tayi kamar
asa ta bu
eta shige ciki.

Kamal kuma da yake neman mafaka tuni ya cafke wannan damar ya nuna hakan ne.

Tsaf Alhaji ya ha
e rai kuwa.

"To ni bana son irin haka?

Idan kana neman mace sanar dani ya kamata ka fara yi saboda nayi magana da manyan ta.

Amma haka kawai ka
auko
ar mutane ka zauna a wajen aikinta da talatainin dare irin wannan ai bai yi ba."
"Ayi ha
uri Alhaji."
"Kema da ki ka biyo shi baki kyautawa kanki ba.
Chapter 77 · 0% Book details