← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 97

Sashe 25

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ne ya yi al
awarin ba zai yi aure ba sai Alhaji ya yafe masa."
Zancen ya fara shigarta.

Kamal ya zama kamar wani lauya wurin jujjuya zance.

A
arshe dai ya samu da kanta ta hango illar auren Taj a yanayin rashin jituwa da uba.

"Abin da za ayi ko Kamalu, ni zan sa a kira min Hayatun muyi magana.

Na san ko babu komai idan yaji daga gareni zai girmama zancen.

Ba zai wula
anta min jika ba."
Tamkar ya sanya ihu haka yaji a wannan lokacin.

Ashe duk
atun da yake ita wani angle
in daban take kallo.

Mi
ewa Taj ya yi ya fice ya barshi yana ta kame kame.

Falo ya koma inda ya yi sa'a babu kowa.

Yana zama Kamal ya fito yana ta waigen baya.

"This woman is too smart Happy.

Kana ganin ta toshe duk wata hanyar da zan
ullo don a kwantar da zancen nan."
Murmushi Taj ya yi "ka
an ma ka gani.

Shi yasa na so fa
a mata gaskiya.

Kai kuma ka hana."
"Haba Happy, wani abin ai sai da siyasa.

Kara wani abu ce"
Kai Taj ya ri
e kawai.

Kwanakin nan gajiya da damuwa suna yawan sanya masa ciwon kai.

Tunda ya sami kan Abba abin ya ragu.

Amma fa daga lokacin da su ka saka ranar zuwa Abujan shikenan bashi da wata walwala.

"Kan ne dai?" Kamal ya yi tambayar da kulawa yana dafa shi.

"Wallahi kuwa."
"Ka daina damuwa.

Ba a yiwa namiji auren dole fa" Kamal
in ya yi murmushi.

"Happiness bana son takura ne.

Sannan bana son ungratefulness.
inta tamkar ban godewa kyautatawarsu bane."
"Don ka taimaki mutum kuma bai kamata ka
ora masa nauyin da zai takura shi ba.

Ni shawarata kawai tunda Hajjon ta
an fahimta ka cigaba da jan
afa.

Kuna fara magana a fito mata as unromantic as possible.

Kada ka sanya mata false hope.

In anyi sa'a ta gudu da kanta."
Sai a lokacin Taj yaji sanyi a ransa.

Ya mi
awa Kamal hannu.

"Happiness nawa ni ka
ai.

Yadda ka ce hakan za ayi.

Thanks bro"
Hamdi bata ta
a shiga motar haya a Abuja ba ita ka
ai.

Ko yawon da su ka dinga fita da Anti Labiba farkon zuwanta, yawanci mijin Antin ke kai su.

Ko kuma Anti Labiban ta kira bold ko uber.

Hankalinta kwance yake tunda akwai idon garin.

Yau da take ita ka
ai ne dai duniyar tayi mata zafi.

Na farko dai direban motar a
oyasinta zai yi biyunta.

Ga jiki da bai
uya ba.

Sannan babu tantama ba bahaushe bane.

Inda zasu je kuma bata sani ba.

Anti Labiba dai ta ce mata zasu bi ta titin hanyar Central Mosque
in da su ka ta
a zuwa.

To gashi an fi minti shabiyar a titi amma babu masallaci babu alamunsa.

Banda hawa da sauka akan wasu gadoji da ko wu
a aka
ora mata ba za ta gane ko
aya ba, babu abin da yake yi.

Ga gudu da ta lura yana yi kamar wal
iya.

Hanjin cikinta su ka sami wuri su ka cure wuri guda.

Zuciyarta tana harbawa kamar za ta fito waje.

Sai kuma bisa rashin sa'a aka kira shi da wata wayar ba wadda take gabansa tana nuna hanya ba.

Ya sanya earpiece a kunne
aya yana magana da yaren da bata ji.

'Passenger' da kuma 'get ready, I will be there soon' ka
ai ta iya tantancewa.

Habawa, duk wani labari da ta ta
a ji game da satar mutane sai da ya dawo mata.

Jikinta ya dinga rawa.

A hankali ta kama shesshe
ar kuka don bata so yaji.

Ta fiddo wayar da Anti Labiba ta bata da za ta taho ta tura mata message.
(Anti zai sayar dani a hanya ban san inda muke ba amma titin yayi kama da bayan gari)
Ta rubuta a jere ko wa
afi babu tsakanin rubutun.

Gashi tana zama a motar ya danna lock ta gaba.

Gilasai duk an
agesu an sakar mata AC.

Anti Labiba na kashingi
e a falo message
in ya shigo.

Ta tashi zaune a gigice.

Ta dinga kiran Hamdi wayar ta
i shiga.

Cikin matsanancin tsoro ta kira nambar Anisa da su ka yi magana
azu.

Abinci ta shiryo a tray ta fito dashi wayar ta shigo.

Bata
auka ba sai da ta ajiye tray
in a gabansu Taj.

Ta
auki wayar daga kan tray
"Dama yanzu nake shirin nemanki.

Naga bata iso ba har yanzu."
Anti Labiba ta
ora hannu a ka "bata zo ba?

Sun kusa minti arba'in da biyar da barin gida fa."
Anisa da bata da saurin fushi tayi musu uzuri da cewa "maybe hold up ne.

Kin san yamma tayi.

An fara dawowa daga office."
"Uhmm uhmm dai.

Bari na turo miki message
in da tayi min yanzu.

Zan nemi maigidan na sanar dashi."
Zama Anisa tayi don ta gama kawo komai falon.

Ta sha kwalliya sosai tayi kyau.

Ta bu
e abincin tana tambayar Taj me za ta zuba masa wayar Anti Labiba ta sake shigowa.

Tambayarta tayi taga text
in ta ce yanzu za ta duba.

Ai tana karantawa ta kama salati.

"Me ya faru?" Taj ya zare wayar a hannunta don jikinta rawa yake yi.

"Anti!

Anti!!" Shi ne sunan da take kira hankali a tashe.

Antin ta fito da mayafi a hannu don kiran ya tsorata ta.

Taj da Kamal su ma duka babu mai nutsuwa.

"Wai yarinyar da na bawa aikin snacks ce ta taho tun
azu amma kinga bata ido ba."
Anti ta ja tsaki "haba Anisa.

Shi ne ki ke min wannan kiran mai firgitarwa?"
Wayarta ta soma lalube Taj ya mi
a mata bayan ya gama karantawa.

Ta dam
awa Antin.

Itama tana karantawa su ka kira Anti Labiba.

Kuka ma take a lokacin.

"Wayarta ko ta shiga bata
auka.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
"Ki ce ta turo numbar mutumin tunda dole akwai numbarsa akan app
in da zai yi magana da passenger."
Da gaggawa Anisa ta fa
i sa
on.

Anti Labiba ta tura musu.

Direba na tafiya ya fara jin sautin kuka na tashi ka
an ka
an.

Gabansa ya yanke ya fa
i da ya
an le
a ta madubi ya tabbata yarinyar da ya
auko ce take yi.

Dama ana cewa fa wasu fasinjojin ba da alkhairi suke zuwa ba.

Wasu ma sharri su ke
ullawa mutane.

Kaddai irinsu ya
auko yau?

"Madam, what is wrong?" Ya kwantar da murya ya tambayeta.

Ita kuma jin ya kirata sai kawai ta fashe da kuka sosai.

"Please take me home."
"We are almost at your destination.

Did something happen?"
Hamdi ta kalli titin.

Babu sawun mutane sosai.

Ita da zai sayar ko ya cirewa sassan jiki zai yiwa da
in baki?

"Zan sauka...drop me here."
Direba ya kalli wajen sai yaji fargaba ta dirar masa.

Bisa shawarar map
in bolt da yake bi an nuna akwai hazard akan hanyar da tafi saurin kai mutum inda zai je.

Hazard
in kuwa yana iya zama hatsari, lalacewar mota ko goslow
in da ya hargitsa titi.

Sai map
in ta za
ar masa wata hanyar daban.

Shi kuma baya son bi saboda nisanta sosai.

Kuskurensa shi ne da ya
auke hanya bai yi mata bayani ba.

Kukan da take a firgice ne ya tuna masa da hakan.

Ya soma bata ha
uri da rarrashi.

Amma fir Hamdi ta
i yin shiru.

Ita dole ya sauketa.

Shi kuma yana tsoron bu
e motar bai san me zai faru ba.

Mutane ma yanzu basu fiye bincike ba.

Wanda yafi rauni yana fa
in abu sai kawai a hau a zauna.

Suna haka Anisa ta kira shi.

Tambayarsa tayi game da fasinjar da ya
auko.

Cike da farinciki kuwa ya fa
a mata abin da yake faruwa.

"Let me talk to her."
Ai ko wayar
in yarda tayi ta kar
a.

Karshe sai speaker ya saka yadda za ta ji.

"Ki kwantar da hankalinki.

Ya ce hanya ce bata da kyau shi yasa ya canja wata.

Amma yanzu zai kawoki."
"Ni dai ki zo ki kar
i kayanki don Allah.

Daga nan in ya kuma tada mota Allah ihu zan masa.

Tun
azu fa muke yawo..." ta fashe da wani kukan.

Anisa ta rasa irin bayanin da za ta yi mata.

Sai kawai ta bawa Taj wayar.

"Naji kamar yarinya ce, please ka
an kwantar mata da hankali Yaya."
A tsiwace Hamdi ta ce "ni ba yarinya bace.

Na yafe ku
in.

Ku zo ku
auka ko na bar masa a mota."
Ita a wautarta in ta nuna bata tsoro
ila a ha
ura da cutar da ita.

Yadda take magana sai ya bawa Taj dariya.

Kai kana ji za ka san a mugun tsorace take.

Wayar ya kara a kunnensa.

"Big girl."
Anisa da Kamal harma da Anti su ka yi dariya.

Da ta amsa abinta.

"Na'am."
"Ni yayan Anisa ne.

Yanzu zan sa direban ya turo min location
in ku.

Sai na zo na kai ki gida.

Haka ya yi?"
"Eh, amma don Allah minti nawa?

Kaga fitsari ya matseni."
aga kai ya yi sai yaga duk sun yi alamun tausayawa gareta.

"Zan yi sauri in sha Allah."
Cikin mintuna ka
an kuwa direban ya tura masa da location ta whatsapp
in Anisa.

Su ka shiga motar Kamal su uku.

Kamal
in ke tu
awa.

Anisa tana baya.

Lokaci zuwa lokaci kuma Hamdi sai tayi flashing da wayar direban.

Ta ma manta ko bashi bata yi ba.

Sai ya rabu da ita tunda ta daina kukan.

"Kun kusa?"
"Saura ka
an."
Anisa ta kira Anti Labiba ta ce mata za su kawo Hamdi gida.

"Don Allah ku yi ha
uri.

Ba
uwa ce a garin."
"Ban ji haushi ba.

Ni tsorona ma firgitar da tayi kada ya zauna mata a rai." Cewar Anisa.

Wasa wasa sun yi minti shabiyar kafin su isa.

Unguwannin ne da tazara a tsakaninsu.

Motar na doso su Hamdi ta kama handle za ta bu
e.

Shi ma direban duk ya
agu.

Yana ganin sun yi parking a bayansu ya cire lock.

Babu takalmi haka ta jeho
afafunta waje ta fito.
Chapter 25 · 0% Book details