← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 97

Sashe 80

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mijinta na zaune wa ya aike ku?" Mama tayi musu tsawa.

Sai kuma ta kalli Taj "tashi kaje mana."
"Ina?" Ya tambaya don bai san kan gidan ba yanzu.

"Tana
akin Inna" cewar Firdaus.

Tashi ya yi kafin yana waige "wanne ne?"
Yayinda wasu ke nuna masa, masu hankali wannan tambayar fami tayi musu.

Inna mai yawan kawaici sai gata ta du
ar da kai tana share hawaye.

Ace
an halak bai san
akin mahaifiyarsa ba a gidan ubansa!

Tabbas wannan abu akwai ciwo.

Yana ganin halin da su ka shiga ya yi saurin barin wajen domin baya son ayi
a kwance uwa kwance.

Murnar kowa za ta koma kuka.

Abin da ba zai so ba.

Tafiyarsa kuwa tsokanar
an uwansa ta janyo masa.

Aka yi ta masa dariyar sha
iyanci.

Hakan sai ya hana koke koken da iyayensu su ka fara.

Hamdi ta fi minti goma sha biyar tana son fitowa amma tana kunyar mutan gidan.

Na farko bata san lokacin da kowa ya fita ba saboda bacci.....'bacci a
akin uwar miji don abin kunya' shi ne abin da ta fara fa
awa kanta da ta farka.

A saman kayanta na jiya kuma taga an ajiye sabuwar doguwar riga an cireta daga leda amma da tag.

Da ta
aga wani irin
amshi ne mai da
a ruhi yake tashi a jikinta.

Babu makawa turara ta aka yi.

Ga wata
aramar ledar an saka sabon brush.

Ta san ita aka ajiyewa.

Ban
aki ta shiga tayi wanka a gurguje ta fito.

Bata son kowa ya shigo ya ganta.

Musamman Inna.

Gaban dressing mirror ta zo ta tsaya ta shafa man da Innar ta nuna mata jiya.

Daga nan bata sake ta
a komai ba ta saka rigarta mai kyau ta yafa
aramin mayafin ta fita falon
akin.

Nan ma babu kowa shi ne ta dinga zuwa
ofar fita tana dawowa.
ofar taji anyi tayi saurin gyara zama a zatonta Inna ce.

Sallamar da ya yi ce ta sake tada mata hankali.

Idan wani ya shigo ya gan su a
akin fa?

Idan Inna....

"Baki amsa min sallama ba kin tsaya kina yaba Salman Khan daga sama har
asa." Taj ya fa
a yana zama a kan kujerar da take.

Da sauri ta tashi tsaye tana kallon
ofa ta ce "Ni ba kai nake kallo ba" da
ar tsiwarta saboda ba wai ta manta abin da ya yi bane jiya.

"As if..." sai kuma ya koma kallon falon yana inhaling
amshinsa kafin ya mi
e tsaye "Wanne ne
akin baccin Inna?"
Da hannu Hamdi ta nuna masa.

Yadda ya dinga tafiya ne ya ta
a mata zuciya.

Ta bi bayansa har ciki.

Nan kam har lumshe idanu ya dinga yi saboda yadda
amshin
akin yake nutsar masa da zuciya.

Irin
amshin da ya dace da Innarsa.

Mai sanyi, da
i da kuma kama waje ya zauna a ran wanda ya sha
e shi.

Juyawa tayi za ta fita ta bashi wuri sai kawai taji ya janyota ya rungume ta baya.

Du
ar da kansa ya yi daidai kunnenta.

Wani nau'in
amshin ya sha
a mai da
i.

A ransa ya
udurta neman sunan mai sayarwa a wajen Inna don ba za a bar matarsa da gidansa a baya ba.

" Yau ma arzi
inki na ci aka ce na shigo
akin Inna kamar yadda Alhaji ya barni na shigo gidan nan domin ki.

I owe yoy big time Hamdi.

Thank you."
Tausayinsa taji kamar daren jiya ta ce "Na taya ka murna Happy."
"Kin dai taya mu." Ya juyo da ita suna fuskantar juna.

"A'a fa.

Ni dama tun farkon zuwana Alhaji bai koreni ba."
"Sai ni uban
an taurin kai ko?"
"Ni dai ban fa
a ba" tayi murmushi.

"Kin ayyana a ranki na sani." Ya kama hannuwanta yana murmushi.

"Ka dai tsargu kawai saboda baka da gaskiya"
Janta ya yi wajen gadon "Zo mu
ana gadon Inna."
"Ni kaza?" Hamdi ta ce a firgice "kada ka janyo min abin fa
a har jikoki mana."
Zillewa tayi ta fita daga
akin ya bita falo kafin ta fita.
uri ya bata akan maganganum Alhaji ga Abba jiya.

"Abin da nayi jiya har yasa ki fushi was for you Hamdi.

Na san baki ji da
i ba amma ina so muyi clearing issue
in kafin anjima."
Da ya san amsar da za ta fito daga bakinta da bai tayar da wannan maganar ba.

Kallonsa tayi.

Kallo mai tarin ma'anoni.

A wajenta kuwa da manufa
aya tayi shi...(na san abin da nake yi).

"Uba uba ne Ya Taj.

Nagode da baka barni na yiwa Alhaji rashin kunya ba da yanzu ina nadama don ba tarbiyar gidanmu bace.

Amma ina so ka sani cewa WALLAHI ba zan ta
a sakin jiki a gidanka ba sai Alhaji ya
auki Abbana da darajar da Allah Ya bashi."
"Me kike nufi?" Taj ya tambayeta da yaji komai nasa ya fara kwancewa.

"Aurena kayi ba sadaka aka baka ba.

Allah Ya sani ba zan iya
auke kai ina gani ana yiwa mutum mafi girman daraja a wurina irin haka ba.

Sai in ga kamar nima na yarda bai kai a girmama shi ba."
"Amma ni wane irin girma ne bana bashi?"
Abin da bata son farawa don kar ta kasa dainawa ne ya zubo.

Hawaye.

Hankalin Taj ya sake tashi.

Ya matso ta matsa baya.

"Ba da kai nake ba.

Ba kuma fa
a nake da Alhaji ba.

Amma kai ma ka san irin matsayin da ya bashi daga maganarsa ta jiya.

Kana gani ko zuwana nan ba shawartarsa ya yi ba duk da dai an
aura aure.

Ko don ya ta
a yin daudanci ne?"
A lokacin ya gane Hamdi bata da labarin ainihin abin da yake tsakanin iyayensu maza.

Bata san sanayyarsu ta wuce ta zaman unguwa
aya ba.

Akwai sauran rina a kaba kenan.

Amma da ta bu
ofa ce ta kawo
arshen zancen.

Sam bata nuna musu taji maganganunsu na baya bayan nan kuma ta fahimci inda suka dosa ba.

Fa
an hana Hamdin fitowa tayi masa.

"Abinci za ta ci a mayar da ita gida."
Wayar Alhaji ce ta tayar da Ahmad daga baccin da ya koma.

Kamar yadda dalilai daban daban su ka hana yawancin mutan gidansu bacci, shi ma haka Salwa tayi sanadin wargaza nasa zaman lafiyar da ta gayyato Anti Zabba'u gidansa.

Ana kiran assalatu da ya tafi masallaci su ka tattara za su bar gidan ko tsinke basu gyara ba daga
arna da almubazzarancin da su ka yi da daddare.

Suka ta
ofa su ka ji a gar
ame.

Ya sanya kwa
o ta waje da zai fita.

Anti Zabba'u ta dinga ruwan ashariya tana cewa tafi
arfin Ahmad ya wula
anta ta.

"Mu gyara gidan nan kawai kafin ya dawo.

Ni bana son rigima." Wata a cikin
an matan ta ce.

Rai a
ace Anti Zabba'u ta ce "An fa
a miki saboda shara ya rufemu?

Nuna isa ne kawai da cin mutumci irin na uwarsa."
"Duk da haka gara mu gyara.

Zan fi son mu fita salin alin kafin ya fahimci halin da waccan mara kunyar take ciki."
Da wannan maganar su ka du
ufa.

Gyaran dai sai a hankali amma dai yafi babu.

Duk abin da su ke yi kuwa Anti Zahra tana jinsu tayi zamanta a
aki.

Mami ma taji komai tana cike da takaicin ba za ta iya
aukar mataki ba.

Da ya dawo don kansa ya ce su bar aikin saboda yadda su ka tasarma damalmala gidan.

Ruwan mopping wannan klin aka zuba masa kuma ba a bari ya narke ba aka matse mop
in sama sama aka soma ya
awa a
asa.

"Ga gidanka nan za mu fita amma wallahi Ahmad bashi kaci.

Wannan wula
ancin sai kayi nadamarsa."
"Boka ne fa ki ke ta
ama dashi.

Ni kuma da wanda ya busawa bokayen rai na dogara.

Ki ajiye makaman kawai ayi zumunci Fisabilillahi."
wafa tayi.

Ranta yana tafarfasa.

Mutumin da ta bawa ku
inta kuma aiki bai ci sai ya yi nadama shi ma.

Sun zo fita Ahmad ya ce "ina Salwa?"
Kamar jira suke kuwa yana magana su ka fice gaba
aya a gurguje.

Bai tsaya tambayarsu ko lafiya ba ya shiga
akin ya ganta a zaune a kan kafet da kumburarriyar fuska tana kuka.

"Tunda bugun fanke ka
ai su ka yi miki ki taso ki gyara gidan nan yanzu yanzu."
"Yaya baka ganin fuskata ne?" Ta sauke mayafinta yadda zai gani da kyau.

"Allah Ya
ara.

Maza ki fito ki gyara gidan.

Amma ki fara duba ko Mami tana bu
atar wani abu."
Kwanciyarsa kenan Alhaji ya kira.

Dama ya tsorata saboda yayi wuri mutum ya amsa waya.

Hankalinsa sai ya nemi barinsa bayan ya fa
a masa me Salwa tayi da kuma babban abin wato ciwon Kamal.

Muryarsa kuma rawa take yi sosai.

"Ban fa
awa kowa ba sai kai.

Ina bu
atar ka zo mu yi shawara Ahmad.

Zan iya rasa Kamal a kowacce da
"Kayi ha
uri.

In sha Allahu zamu sami mafita.

Gani nan zuwa."
"Ka taho da Salwa."
RAYUWA DA GI
I 31
BATUL MAMMAN
YA HAKIMU gwanin Sarkin
"Salwa kuma Alhaji?

Wani abu tayi?"
Ahmad ya yi tambayar ne saboda a tunaninsa ciwon Kamal ka
ai ya isa ya gigita Alhaji.

Me zai sa ya tuna da Salwa har ya nemi a taho da ita a lokaci mai mahimmanci irin wannan?

Gwiwa a sage ya tambaye shi "Laifi tayi ko?"
"Kai dai ka taho min da ita."
Yana bashi wannan amsar ya gane ko ma mene ne ba abin wasa bane tunda lalura mai girma kamar ciwon
odar Kamal bai hana shi nemanta ba.

A kitchen ya same ta da himilin kwanuka kamar a gidan ake taron biki.

Ko tausayi bata bashi ba don taurin kai da kafiya gami da son zuciyarta ne ya jawo mata.

Abu guda ne dai.

Ya sanyawa ransa sai ya bi kadin dukan da aka yi mata a cikin gidansa.

Su Habitti ba a ci bulus ba.

Mu
ullin mota ya
auka ya ce da Zahra kiransa ake yi a gida game da bikin Taj ya fice.

Da ya kira Salwa su tafi ba
aramin rawar jiki ta dinga yi ba.
Chapter 80 · 0% Book details