← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 97

Sashe 33

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuma Hamdi gani take tsabar mugunta ce ma za ta sa ya cigaba da ingiza mata uba akan hanyar da babansa ya kore shi a kanta.

An yi Kamun Sajida ranar laraba cikin farinciki da taron dangi.

Hamdi tuni ta ajiye wani Taj ana ta sha'ani.

Wannan karon ko ciwon kai bata ce tana yi ba saboda tsananin farinciki.

Sajida ta sami wanda take so kuma yake sonta ba tare da ya ta
a goranta mata ba.

Damuwar su Yaya da tsoron
an matansu ba za su auro ba ta kau.

Komai nasu na rufin asiri sun yi domin fitar da juna kai kunya.

Alhamis aka yi sisters' a wani event centre.

Ranar dai har rawa Hamdi tayi tunda taron mata ne.

Sai da Anti Labiba ma ta janyeta saboda ko gajiya bata yi.

Ana canja ki
a take komawa.

"Wannan ko ke ce amaryar sai haka."
Wata
ar uwarsu ta kare mata "barta tayi.

Ranar nata auren ai ba yi za ta yi."
Ana can ana shagalin biki wasu motoci biyu masu kyau su ka yi parking a
ofar gidan Abba.

A tsaye yake da Kamal da Taj.

Kamal ne ya zo bashi tashi gudunmawar wadda ta kasance ta kayan abinci.

Sa
anin ta Taj da ya bashi ku
i.

Yana ta cewa sun yi yawa da almajirai na kaiwa cikin gidan wa
annan motoci su ka tsaya.
ar Ficika ne ya fara fitowa daga motar gaban yana murnar ganin Abba a
ofar gida.
annan mutanen ne su ka zo nemanka nace musu ai ka tashi daga wurin.

To sai..." ya juya ya nuna wani Alhaji da ya nufosu yana takawa kamar baya so "wannan Alhajin ya nemi in kawo shi wurinka.

Har za mu je restoran
in sai na tuna
azu ka ce min kana gida."
Abba ya yi murmushi "ai da ka sa wani ya rako shi ma."
"Yaran nawa duk basu san nan
in ba."
Abba ya mi
awa mutumin hannu domin su gaisa sai ya
aga nasa.

Kallon wula
anci kawai yake yiwa Abban.

Shi da ragowar mazan da su ka firfito daga motocin har su biyar.

"Kai ne Habibu Simagade?"
Abba ya
an murmusa "a da kenan." Ya kuma mi
a hannun mutumin bai kar
a ba dai.

"Ni ne uban Safwan mahaifi."
Mamaki ya bayyana a fuskar Abba.

Tabbas ga kama nan.

To amma ba wani abu bane tunda da ana neman aure kawunnansa ne su ka zo.

"Allah Sarki.

Bari nasa ayi shimfi
a a ciki."
"Barshi.

Zuwa nayi na fa
a maka cewa idan ka kuskura aka
aura aurensa da
arka gobe sai na
aure duka mutanen gidan nan."
"Alhaji me ya faru?" Abba ya ce da fargaba.

Taj da Kamal ma hankalinsu tashi ya yi.

"Meye ma bai faru ba?

Ya fa
a min yana son wata yarinya nasa aka bincika aka ce ubanta
an daudu ne.

A ranar na soke maganar.

Shi ne ya ha
a kai da wan uwarsa aka zo aka nemi aure da komai a bayan idona.

Suna ta
oye
oye basu san na sani ba.

Dama bari nayi sai goben in ci muku mutumci duka a wajen
aurin auren.

Sai yayansa ya shiga maganar" ya nuna babban
ansa "shi yasa na zo yau.

In kun je an
aura za ku ga abin da zai faru.

Zuriata tafi
arfin ha
a jini da irinku.
ata gari, lalatattun mutane"
Banda Innalillahi babu abinda Abba ke fa
ar Ficika kuwa ihu ya saka kamar mace yana ta jan jallabiyarsa sama yana tumamin wai sun shiga uku.

Baban Safwan ya kalle shi cikin takaici da ba
incikin anyi asarar namiji.

Ha
uri Abba ya fara bashi ya dakatar da shi.

Kamal da Taj su ka saka baki ya ce babu ruwansu.

Ba su yi aune ba Abba ya dire gwiwoyinsa a
asa zai fara ro
o mutumin ya juya abinsa bayan ya yi tsaki.

"Alhaji ka yiwa Allah kada ka hana auren nan."
Da sauri Taj ya kama hannunsa zai
aga shi amma ya
i mi
ewa.

"Abba don Allah ka tashi."
"Idan auren nan bai yiwu ba gaba
aya gidana laifina za su gani.

Sajida bata ta
a saurayi ba sai akan shi.

Sun saka rai Taj, kowa ya saka rai.

Duniya za ta zage ni.

Duniya za ta min dariya.."
Babu wani tunani ko hangen nesa Taj ya ce masa "Abba indai ka amince za ka bani Hamdiyya, in sha Allahu gobe za ka aurar da
"Taj?" Kamal ya kira shi gabansa na fa
uwa.

"Ina son ta Abba.

Saboda ita na zo gareka."
Abba Habibu rasa bakin magana ya yi.

Ido kawai ya zubawa Taj har motar baban Safwan ta bar layinsu bai sani ba.

RAYUWA DA GI
I 16
Batul Mamman
_Ya Rabbi.

Ya Zhuljalal wal Ikhram.

Allah
anmu sun koma makaranta.

Ka duba mana su da dukkan abokan mu'amalarsu da sauran
an bayinKa.

Ya Allah Ka tsare su daga dukkan sharri.

Ka kare su daga zamewa kowa sharri.

Allah Kada a kai
ararsu, kada su kai
arar wani.

Ka basu ilimi mai albarka da amfani.

Kasa aci moriyar abin da ake nema na boko da addini.

Ya Sami'ud du'a Ka fimu sanin mawuyacin halin da
asarmu take ciki.

Ka horewa iyaye abin da za su ciyar da iyalansu daga halali.

Ka makantar damu akan haram.

Duk uzurin da zai taso Ya Allahu kada Ka sa mu ro
i kowa.

Ka bu
a mana.

Ka albarkaci nema da samun mu.

Ya Rabbi Ka kawo mana sau
i da sassaucin rayuwa.

Ka azurtamu daga taskarKa wadda bata da iyaka.

Amin_
Kallon da Abba ya yiwa Taj na tsantsar
auna da girmamawa ne bayan ya gama mamaki.

Ya mi
e tsaye ya kama hannun daman Taj da hannayensa biyu.

"A duniya bayan iyayena da matata da kuma
an uwana da ba su guje ni ba da kuma
alilan cikin abokai, kai ne mutum na farko da jini bai ha
amu ba amma kullum burinka ka sanya farinciki a rayuwata."
Kamal samun kansa ya yi da girgiza kai saboda tsoron kada ya amince da
anyen aikin da Taj ya
allo.

"Abba..."
Kallonsa Abban ya yi yana murmushin danne ciwon dake cin zuciyarsa.

"Kada ka damu Kamal.

Ba zan ta
a zama butulu gareku ba.

Na san duka abin da kake gudu.

In sha Allahu ni Habibu ba zan bari son zuciya yasa na zama mai
ara nesanta uba da
ansa ba."
Daga Taj har Kamal ba
aramin tausayi ya basu ba.

Taj ya rufe ido ya ce,
"Abba, Alhaji ya da
e da zare hannunsa a kaina.

Auren Hamdi ba zai ..."
Kamal ya katse shi da hanzari "wallahi zai
ara girman fushinsa a kanka.

Haba Happy, ba ka tunanin su Inna ne?" Ya mayar da idanunsa ga Abba "ni zan auri Sajidan in sha Allahu.

Laifin ba zai tattare akan Taj ba."
Abba jinjina zumuncin
an uwan yayi.

Kuma bai bar zancen a cikinsa ba ya fa
a musu.

"Lallai Yaya Hayatu ya iya haihuwa.

Ko sha
an da su ka fito ciki guda ba lallai su yi zumunci irin naku ba.

Amma ku tafi gida, nagode.

Zan bawa Sajida ha
uri.

Na san za ta yi min uzuri."
"Sai dai idan ni ne baka son bawa
arka.

Ba auren taimako zan yi ba.

Allah na fi shekara ina sonta."
"Har a yaushe ka santa?" Kamal ya tambaye shi don bai yarda da zancensa ba ko ka
"Duka wannan bai taso ba.

Ku je gida.

Nagode"
Abba zai shige gida
ar Ficika ya kamo shi da sauri.

Duk sun manta dashi.

Kwarwar da yake da ihu ma ba sa ji saboda mahimmancin abin da su ke tattaunawa.

"Simagade....au Habibu ashe baka da hankali?

Ya Allah zai kawo maka agaji a lokaci irin wannan ka nemi ka watsa mana
asa a ido.

Ina mai tabbatar maka da cewa Sajida kai za ta
orawa alhakin rabata da farincikinta.

Daga nan kuma bamu san halin da za ta shiga ba.

Ni a tawa shawarar kawai ka bari su aure su duka."
"A'a Balarabe.

Baka san komai akan yaran nan ba.

Son zuciya a yanzu ita ce
iyayya mafi girma da zan nuna a madadin kyautatawar da su ke min."
ofar gidansa ya
arasa da sauri don
irjinsa zafi yake.

Sai dai ko rabin jikinsa bai samu shigewa ba ya fa
i a wurin.
ar Ficika aka sake samun abin yi.

Ya
ora hannu a ka zai cigaba da ihu, Kamal ya daka masa tsawa.

"Kada ka kuskura ka sake tara mana jama'a.

Yi sallama ciki ka yi min magana da Yaya."
"To, to" ya amsa kamar ba
an cikinsa bane ya yi masa tsawar.

Yadda mata ke ru
ewa a irin wannan yanayin, haka nasa hankalin ya gushe.

Da Kamal ya juyo bai ga Taj ba.

Ya fara tunanin ko cikin gidan ya shige, don yanzu komai aka ce ya yi ba zai yi mamaki ba.

Ya lura yana da taurin kai irin na Alhajinsu, sai dai kuma shi Taj ya ha
a da
anyen kai kamar wani
an ta kife.

Idan ya san abu daidai ne to kawai damn the consequences.

Horn
in mota yaji daidai
ofar gidan.

Ya le
a Taj ya fito a lokacin.

"Mu kai shi asibiti."
"Ai ka bari a fa
awa Yaya ko?"
Bai ma yi wannan tunanin ba.

Amma da yake ya san mahimmancin yin hakan sai ya gya
a kai.

Salatin Yaya su ka ji su ka koma cikin soron.

"Damuwa ce Yaya.

Kada ki
aga hankalinki musamman tunda da mutane a ciki.

Za mu kai shi asibiti."
aga shi su ka yi Kamal ya
arasa dashi motar.

Taj kuma ya tsaya sakamakon maganar da Yaya ta fara yi.
ar Ficika kuma ya ce..."
Taj ya gallawa
ar Ficikan harara shi kuwa bawan Allah ya girgiza kai da sauri.

"Wallahi ban fa
a mata komai ba."
"Me ku ke
oye min?" Ta tambaya hankalinta a tashe.

Dama bata ga abin da zai
aga masa hankali ya fa
i ba.

Bayan bikin nan shi ne babban farinciki da cikar burinsu.

Gani su ka zasu
ata lokaci sai kawai Taj ya ce
ar Ficika ya fa
a mata in sun tafi.
Chapter 33 · 0% Book details