← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 97

Sashe 26

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayafin da ta yafa akan riga da siket
in jikinta ya rufe rabin fuskata.

Wayar Anti Labiban ma bata
auka ba ta fito da sauri.

Mayafin da ta gyara ne ya bayyana fuskarta sosai.

Taj yana fitowa su ka ha
a ido.

Zuciyarsa sai da tayi wani irin abu saboda ganin abin da bai ta
a zato ba.

"Hamdi?" Ya furta a can
asan ma
oshi shiyasa babu wanda yaji.

Ita kuwa bata ma gane me ta kalla ba.

Burinta dai ya cika ta fita daga motar mutumin.

Kamal ya
arasa wurin direban ya bashi ha
uri tare da cewa
anwarsu ce.

Shi ma ya bada ha
urin rashin yi mata bayani wanda ya janyo wannan ru
anin.

"Ga kayanta" ya ce da yaga suna shirin tafiya.

Kwalaye ne madaidaita guda biyu.
aya doughnut.
ayan kuma meatpie da samosa.

Sai kuma ledar youghurt wanda Hauwa ce da kanta tayi.

Anisa ce ta kula Hamdi bata da takalmi da ta zauna a baya.

Za ta fita ta
auko mata sai Taj ya ce ta zauna.

Shi ya
auko harda wayar yana ta mamakin wannan coincidence.

Ashe tana Abuja.

Shi yasa baya ganinta a gidansu.

Murmushi kawai ya dinga yi har su ka soma tafiya.

Hanyar gidan da ba ganewa za ta yi ba shi ma Anti Labiba ce ta turo kwatance.

Anisa ta ce ta gane.

Idan sun isa unguwar za ta kira sai ta kwatanta gidan.

"Shhh" Hamdi ta fara yi da baki saboda fitsarin da ya gama matsarta.

Tun a na farko Taj ya ji.

Hankalinsa gaba
aya yana bayan motar.

"Step on it Kamal (
ara sauri)" ya ce a hankali don kada taji kunya.

Kamar a kunnen Anisa ya fa
a sai cewa tayi "eh kuwa.

A matse take sosai" tana kallonta.

Ko a jikin Hamdi.

Burinta kawai a isa gida.
afafunta sun kasa zama waje guda.

Komawa gidan tayi mata nisa saboda uzurinta.

Finally bayan ta gama gumi su ka shiga estate
in su Anti Labiba.

A guje ta fita da Kamal ya tsaya.

Ta sake barin takalma da wayar da dama Taj bai mi
a mata ba.

Anisa ta bita cikin gidan su kuma suna waje.

Anti Labiba da yara sun taso da murnarsu ta wuce su ta shige ban
aki.

Bata ma kula harda maigidan ba sai da ta gama ta fito.

"Washhh Allah na." Ta furta da ta dawo hayyacinta.

Sai kuma ta rungume Antin tana kuka.

"Mene ne na kuka kuma?

Ba gashi kin dawo ba."
Ta kalli maigidan da su ke kira Uncle.

"Na zata ba zan sake ganinku ba."
"Ke dai anyi matsoraciya." Cewar Anti Labiba tana dariya.

"Ko nice fa zan tsorata.

Bata san wuri ba kuma an bi hanya daban." Anisa ta kare mata.

Murmushi ta yiwa Anisan gami da bata ha
urin rashin cika al
awarin kai kaya.

"Wa yake ta kaya baiwar Allah?

Ai tunda dai kin dawo gida nima bu
atata ta biya."
Kiran sallar magrib aka fara Anisan ta ce tare su ke da yayyenta.

Uncle da kansa ya fita ya kira su cikin falo domin su yi sallah bayan an kai musu ruwa sun yi alwala a waje.

Suna idarwa Anisa ta ce za su tafi.

Anti Labiba dake kitchen tana ha
a zo
o ta hana.

Sai da ta ha
a komai ta kawo ta nemi Hamdi a falon ta rasa.

Maigidanta ta tambaya ina take ya ce ai tun shigowar su sallah bai ganta ba.
aki Anti Labiba ta bita.

Ta sameta zaune a bakin gado da zumbulelen hijabinta.

"Ki zo ki sake yi musu godiya za su tafi."
"Anti rawar fitsari fa na dinga yi a motar.

Ni dai wallahi ba za ni ba."
"Harda saurin rantsuwa?"
"Baki ganni bane" ta fa
i tana takaicin abin da tayi.

Falon ta dawo bata san Hamdin na bayanta ba.

A bayan labule ta ma
ale ta
an le
o da kanta.

Hira Uncle yake da su Taj inda a nan su ka gane su
in duka
an Kano ne.

Ya nemi su dinga zumunci domin an zama
aya.

Ta bayan labulen ta sake ha
a ido da Taj domin yaga tsayuwarta tun farko.

Baki ta bu
e don da wannan kallon ta gane shi.

Zuciyarta ma bata manta ba saboda irin harbawar da tayi da sauri.

Ta sanya hannu ta rufe bakinta.

Za ta gudu taji muryarsa da ta gane tun a wayarsu ta
azu.

"Kamal bani key na
auko mata takalma da wayarta."
Anti Labiba ta waiga ta hango shatinta a labulen.

"Zo ki je ki kar
o mana.

Ko sai ya biyoki dasu kuma?"
Sumi-sumi ta fito kai a
asa.

Kamal ya tsaya bawa Uncle numbar wayarsa.

Ita kuma Anisa santin zo
o take tana kuma wasa da yaran gidan.

Da fa
uwar gaba ta isa bakin motar.

Taj ya bu
e ya
auko mata takalman da wayar.

Maimakon ya mi
a mata sai ya jingina da motar yana kallonta.

"Kin gane ni yanzu ko?"
Murmushi tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta.

"Ashe nan ki ka gudu shi yasa ban ganki ba."
Kallonsa tayi a fakaice "nema na kake yi?"
"Na san inda zan same ki Hamdi.

Kawai ganinki ne ban yi ba a wajen."
Shi mai maganar da ita da ake yiwa duk jikinsu tamkar anyi musu duka.

Zu
atansu ke aikin wucin gadi na tsananin murnar sake ha
uwar bazata irin wannan.

"Ina?

Makaranta?"
"A gida."
Daina
oye fuskarta tayi.

Ta kalle shi da mamaki.

Muryoyin su Anisa yaji sai ya bata kayanta.

"Sai mun ha
u a Kano.

Take care."
Motar ya shiga amma bai rufe ba har su ka iso.

Hamdi ta sake yi musu godiya sannan su ka shiga mota su ka tafi.

Daren ranar mutumin da bata san sunansa ba ne ya cika mata zuciya da tunani.

Bata da wani aiki sai murmushin da bata san lokacin da yake zuwa ba.
angaren Taj kuma suna yin sallar isha ya ce bacci zai yi.

Abincin da Anisa ta dafa Kamal ne kawai ya ci.

Shi kuma ya sanya snacks
in Hamdi a gaba.

A take ya yanke shawarar sanyata a
angaren snacks
in restaurant
in shi wanda Kamal ya yiwa suna da HAPPY TAJ.

Kuma ba shi ka
ai ba.

Kowa ya ci sai yaba da
in kayan.

Wayar da su ka dinga magana
azu ya kira sai yaji muryar direban motar.

Ba yadda ya iya.

Godiya kawai ya sake yi masa ya katse kiran.

Kenan ba da wayarta su ke magana ba?

Yayi guntun tsaki.

Babu matsala tunda samunta ba zai yi masa wahala ba.

Zuciyarsa wasai ya kwanta.

Tun asuba Taj ya fa
awa Kamal cewa a yau za su koma Kano.

Zai yi magana da Anisa kafin su tafi.

Ba musu ya amince " gara haka don zamanmu ma zai iya sanyawa ayi tunanin wata soyayya ku ke bugawa fa."
Da yake da wurwuri ta tashi ta ha
a musu breakfast.

Shi ya taimaka masa wurin samun ganinta da wuri.

Ta zauna a falo ta sunkuyar da kai
asa.

Gaba
aya sai ya dinga jin babu da
i.

Hajjo taje kawai ta sanya mata rai.

"Anisa."
"Na'am Yaya."
"Kinji ha
in da Hajjo take son yi mana ko?" Kai ta gya
a da murmushinta.

"Bani da abin cewa game da karamcin gidan nan naku sai godiya.

Anyi min komai a lokacin da na rasa soyayyar mahaifina."
Ta dube shi da tausayawa "kayi ha
uri.

Komai zai daidaita in sha Allah."
"Haka nake fata.

Amma saboda halin da nake ciki Anisa bana son yin aure yanzu."
A razane ta dube shi.

Gabanta na fa
uwa kada ya ce baya sonta.

A ransa hakan yake son fa
a ko don ta bawa wasu dama.

Amma yana gudun me zai je ya dawo.

"Ina son lokacin aurena Alhaji ya halarta ba don anyi masa dole ba.

Idan na sami
a in kai masa ya yi hu
uba yadda yake yiwa
an uwana.

Ya kuma sanyawa abin da na samu suna." Yaja numfashi "hakan ba zai samu ba yanzu saboda bai ha
ura ba."
"Kana nufin na nemi wani kenan?"
Ta tambaye shi da sanyin jikin da ya sanya masa tausayinta.

"Ina nufin mu bi komai a sannu sannan mu nemi za
in Allah.

Bana son in yi miki al
awarin da ba zan iya cikawa ba."
Murmushi tayi ga
walla ta taru a idanunta "na fahimceka, zan kuma cigaba da yi maka addu'a."
"Nagode" yaji zuciyarsa maimakon ta rage nauyi
arawa tayi.

Reaction
in Anisa na sau
in kai ya kwa
a masa lamari.

Shawarar Kamal ta biyu zai bi.

Ba zai yarda ya nuna mata kulawar da za ta saka rai da samunsa ba.

Amma abin da kamar wuya domin Hajjo ba za ta sakar masa mara ya sha iska ba.

Shi ya san da wannan.

Sati guda ya
ara a Kano ya tattara ya tafi.

Ayyuka ne har biyu su ka taso masa na bukuwan manya wanda suka
i yarda su nemi wani chef
in duk da baya nan.

Sun tsara abubuwa da dama da Abba kafin tafiyar tasa.

"Ka cigaba da training
in yaranka kafin na dawo.

Idan sun yi passing test
ina zan yi retaining
insu."
Abba ya ce "shagon fa?"
"Ku cigaba da girkinku kafin a
arasa wancan."
Gidan Abba Habibu kowa ya yi farinciki da cigaban da ya samu.

Wurin yanzu yafi na da komai da komai.

Hamdi ce ka
ai da labari yaje mata ba kunya ta ce ko waye Taj
innan bai burgeta ba.

Idan taimako zai yi ai da ya samarwa Abba wata sana'ar.

Kuma da yake a idanunta wani matashin
an daudun take gani, sai taji duk ta tsane shi tun kafin su ha
u.

Haka kawai ya zo ya yi amfani da halin rashin da suke fama dashi wanda ya hanata shiga jami'a ya sake dulmiya mata uba.

Har ta dawo Kano bayan wata uku da ko sau
aya bawan Allahn nan da ya gama da zuciyarta bai nemeta ba.

Tun tana damuwa don ta sa rai za ta sake ji daga gare shi har ta ha
ura.

Sana'ar snacks ta kama ka'in da na'in wadda kuma Allah Ya sanyawa albarka.

A
an tsukin wajejensu tayi suna.
Chapter 26 · 0% Book details