← Book details Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 97

Sashe 50

Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da alama barkwancinsu Taj ba a
asa su ka
auka ba.

"Allah da gaske.

Shi yasa mu ka ce gara ta zo.

Kuma dai idan zuwan zamu yi Inna ba za ta bi mu ba.

Ai kin san wacce ce Inna a cikinmu ko?"
Yaya tayi murmushi "na gane."
Mama ma dariyar tayi "tunda anyi auren ya dace mu san juna ko yaya ne.

Ina fatan zuwan nata babu takura."
"Wace irin takura kuma ku da abar ikonku?

In Taj cewa yayi ta tafi kenan ai sai dai mu bita da addu'a."
Da girmamawa gami da mutuntawa su ka gama magana.

Taj zai
aukota bayan azahar.

Abba ya yi mamakin shigowa gida ya sami Yaya ta ta
are tana gogewa Hamdi jiki da ragowar dilkan Sajida.

"Allah
adiran ala mayyasha'u.

Khadijatul Kubra yau ke ce da wannan aikin?

Lallai Sajida rakiya tayo a gidan nan ga
ar so nan kin saka a gaba" ya kalli Zee dake gefe tana fifita garwashi "kema
ar rakiyar ce ko za ayi miki?"
Kunya ta kama Yaya ta tashi ta koma cikin falo.

Hamdi da Zee su ka yi ta dariya.

Da
yar Hamdi ta yarda ake yi mata.

Wai cikin mutane za ta je.

Bata son a rainata ta.

Zee ma nata kwa
in yana gefe.

Ita kuma sai yau Baballe zai zo.

Cinikin motoci ya kai shi Kwatano tun bayan auren.

Yaya ta ce gara a ga
an nata a yanayin da duk hassadar mutum sai dai ya kushe a zuci.

Sai gashi Abba na sakota a gaba ta gudu.

Falon ya bita "dawo ki cigaba da kankareta kada mijin ya zo a barshi jira."
"Kankara kuma don Allah kamar wata faso?" Ta fa
i tana
ar harararsa cikin wasa.
an da irin wannan abu ba ba
onsu bane su ka tattara su ka barsu a falon.

Zee ce ta
arasa mata ita kuma ta yiwa Zee
in.

"Wai amma gyaran jiki kamar za a kai mu yau?" Cewar Zee da su ka sanya turaren wuta cikin lullu
aton zani kowacce ta zauna akan kujera.

"Ke dai muyi kawai in ba kin shiryawa mitar Yaya ba.

In taji haushi sai ta hanamu zuwa gidan Ya Sajida gobe."
"Kin tambaya ma kuwa kamar yadda ta ce?

Ni fa na rasa ma me zan ce.

Haka kawai yanzu shige ds fice na sai in bin wani bayan a gidanmu nake" cewar Zee.

"Na ma manta da tambayar.

Zan dai gwada.

In na kasa in rubuta a text." Shawarar ta yiwa Zee.

Ita ma a text
in za ta rubuta.

Suna idar da sallar azahar Yaya ta umarci Hamdi da yin wanka ta shirya.

Jinkirin fita na
aya daga cikin abubuwan dake saurin kawo sa
ani tsakanin ma'aurata.

Ita dai nata to ne.

Tana kaffa kaffa don sun gama shirya irin dabdalar da za su yi gobe da Sajida.

Ga tanadin hira da neman shawara kowacce tana son ji daga babbar yaya.

Biyu da kwata Taj ya iso.
ememe Kamal ya
i rako shi.

Har cewa ya yi to wa zai shiga da ita gidan tunda shi a waje zai tsaya.

Kamal ya ce masa in sun iso ya kira shi.

Haka nan ya tafi yana mita.

Sai da Hamdi ta fito ya shiga shi masa albarka.

Yana zaune a falo yana zubawa Yaya santin kunun ayanta da duk sanda zai zo sai ya nema tayi sallama.

Ya juya a hankali su ka yi sa'ar ha
a ido.

Da ido kawai ake gani lallausar shaddar da ya saka wadda aka yiwa
inki irin na matasan zamani.

Ruwan toka ne kamar kullum an
aranta adon.

Very classy and elegant.

Bai saka hula ba sai gyaran fuska da ya yi.

Ita kuwa cikin
inkunansu na bikin Sajida ne ta saka guda da ya kamata su sa ranar
aurin aure.

Riga da siket ne mai adon ja da shu
i mara turowa ne a jiki sai ba
i.

Fuskarta yau ya fara ganinta da kwalliya irin wannan.

Light make up.

Komai cikin tsari babu hayaniya.

Tayi
aurinta a karkace ka
an ta
ora shu
in mayafi daga rabin
walin.

Hannuta da lallen biki ya fara tafiya ta sanyawa abin hannu a
aya.
ayan kuma agogo ne na silver.

"Gara ku tashi kada yamma ta same ku ko?" Yaya ta ce da taga kallon ya
arewa.

Taj ya ma manta inda yake da alama.

Ita kuma Hamdi sai juya awarwaro take.

Da ya fita ta fara binsa sai taji kamar ta zura da gudu.

Tsoro ya shigeta har zuciyata tana gudun famfala
i.

Bakin wata mota da duk rashin sanin motocinta ta san wannan ta kai duk inda ake so ta kai.

A idonta dai jeep ce tunda tana da tudu.

Fara
al da tambarin BMW a jiki.
e mata ya yi ta shiga sai ta daina ganin hasken rana sosai.

Gilasan masu duhu ta kalla ta
ara jin wannan tsoron.
amshin da
in da motar take fitarwa zai iya mantar da mutum a ina yake.

Taj na zama a mazaunin direba ta kama kanta.
an waigen
auyancin ya
are.

Ya tada motar ya kunna AC sannan ya fara ribas.
an tsaya."
Hamdi ta fa
i tana
ora hannu a
irji.

Burki ya taka da hanzari "Me ya same ki?"
Idanunta har sun tara
walla ta ce "Gabana ke fa
uwa wallahi."
"Saboda me?

Ha
uwa da
an gidanmu?"
Ta girgiza kai da dukkan gaskiyarta ta nuna shi.

Yana son honesty
inta.

Juya kan motar yayi domin su hau titi ya ce
"Kin dai san ko ina satar mutane ba zan saci jinin Abbana ba ko?"
Tana jinda
in yadda yake girmama mahaifinta sosai.

Amma da yake bakin baya shiru sai cewa tayi "na sani ko ka fara yau.

Ka zo da mota a rurrufe ba a gano ciki ta waje."
auye zan ce miki ko matsoraciya?

Amfanin wannan tint
in ga irinmu shi ne yanzu misali idan naji ya kamata..."
auke ido ya yi daga titi su ka kalli juna.

"Ya kamata me?"
"Will you let me kiss you idan mun dawo?

Ko yanzu in sami wurin parking?"
"Ya Taj???" Idanunta su ka firfito.

"Na'am.

Ashe kin san suna na.

Na zata Salman Khan za ki ce.

Har na tanadi wa
arsa da zan miki." Ya yi maganar yana dariya.

Bakin tsiwa ya mutu murus.

Ya
an kalleta yaga hannuwanta kawai take kallo.

Shi da ya tsammaci ta bashi amsa.

"Hamdi?

Yaya?

Zazza
in ne yau ma?"
"Uhmm" ta gya
a kai harda shafa wuya da goshi.

"Ki ce in tanadi maganin maleriya da thypoid ranar da za ki tare kawai."
"Allah da gaske nake.

Jikina babu
wari ma." Ta
aga hannu ta sake shi yaraf.

"Kinga mun kusa zuwa gidan.

Ki rufa min asiri yanzu don za ki ha
u da
an jarida masu tambayar tsiya.

Akwai
an bugun ciki ma wa
anda za ki iya fa
a musu duk hirar da muka yi yanzu ba tare da kin sani ba."
A tsorace ta ce "da gaske?"
"Da wasa" ya furta a hankali yana yi mata murmushi.

A bakin gate
in wani
aton gida taga sun tsaya.

Ya
aga waya ya kira Kamal ya ce masa sun iso.

Tsoron nan bai barta ba ta ce "ba za ka shiga ba?"
"Alhaji bai yi min izini ba." Ya amsa mata da murya mai rauni.

Tausayinsa ya mamaye zuciyarta har taji kamar tayi masa kuka.

"Kada ki
ata min kwalliyar nan tun kafin na biya ku
inta don Allah."
ba don kai nayi ba" ta ce da tsiwar nan.

"Mala'iku suna jin ki dai."
Da sauri ta ce "Astagfirullah."
Bata ankara ba ya yi abin da tun shigowarta motar yake muradin yi.

Hannunta mafi kusa dashi ya kama ya sar
e yatsun ya lan
washe su.

"Wa ki ka yiwa kwalliyar?

Suna ji dai kada ki manta."
Tsuke baki tayi tana jin yadda
umin hannunsa ke shigarta.

Ita kam ta shiga uku.

Wannan aure ta son ya
ore....Allah na tuba ta fa
i a zuci.

"Hamdi?" Ya
an matsa hannun.

"Kai na yiwa" murmushi ya soma yi ta
ara da cewa "amma dai Yaya ce ta tilasta min nayi."
"Allah Ya biya Ya mafificin alkhairi.

Now can I ki..."
Bata bari ya gama magana ba ta sanya hannu ta toshe masa baki.

"Kaga fa Ya Kamal ya fito." Ta kalli gate
in a firgice.

Dariya ta bashi ya cire hannun nata ya ri
e shi da
aya hannun.

"Idan ya
araso sai na ce ya tayani ro
onki.

Kinga fa a waje za ki barni for God knows how long."
Kamal har ya
araso.
wasa gilas ya yi ta
angaren Taj.

Shi kuma ya zuge gilas
asa.

"Happiness ta
i yi min sallama kamar bata san iyakata nan ba.

In ta shiga ciki sai sanda suka ga damar sako min ita."
Sunkuyar da kai tayi don har lokacin hannuwanta suna cikin nasa.

Tana ja yana sake ri
ewa.

Kamal dariya yayi kawai "Mrs Happy haka za mu yi dake?"
"Shi za ka za
"Da me kike tunani?

Ya za
eki a kaina?"
"Naga wai ni ce
arama" tayi kicin kicin da fuska.

A take Kamal ya canja she
"Happy bu
e mata.

In ka kaita gida sai ku yi sallamar a can."
"To wallahi tayi al
awari a gabanka" Taj ya sha kunu da ya yi maganar.

"Ki yi mu shiga kinji.

Su Umma ke su ke jira."
"Nayi." Ta fa
a don idanun
an uwan su biyu sun hanata sakat.

Sama Taj ya yi da gilas
in ya kai hannunta guda bakinsa ya sumbata.

Hamdi ta rasa inda za ta tsoma ranta don kunya.

"Gidanmu ba irin wanda ki ka saba bane Hamdi.

Duk inda ake da yawa komai is possible.

Don Allah idan an
ata miki rai ki fara fa
a min kafin su Abba.

Zan baki ha
uri a madadin ko waye.

Kin ji?"
Murmushi tayi har zuci.

Ta
an matsa hannunsa dake cikin nata sannan ta fita.

Kamal na bu
e gate da su ka shiga ciki taji wata murya da ta so ta gane tana yi masa magana.

"Ya Kamal basu iso bane?"
Hamdi ta bi inda ya kalla da ido.

Budurwa ta gani tayi kwalliya ta fitar hankali.

Tayi kyau tamkar wata amarya.
Chapter 50 · 0% Book details