Sashe 1
Rayuwa Da Gibi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Table Normal
No List
RAYUWA DA GI
Batul Mamman
Bismillahir Rahmanir Rahim
_In loving memory of Aisha Aminu Balbalo (mai lalurar numfashi da take sayen cylinder
in oxygen wadda aka fi sani da Carofee).
Allah Ya ji
anta Ya gafarta mata.
Amin_
Wanki take a tsakar gida tana sauraron hirar mahaifiyarta da
anwarta Zee.
Ba ta saka musu baki saboda tun ainihinta ba mai son hayaniya bace.
Sai murmushi kawai idan sun yi abin dariya.
"Wannan wankin naki zai sami shanya kuwa Hamdi?"
Sararin samaniyar da Yaya ta kalla ita da Zee su ka zuba wa ido.
Ga dai rana ana gani tana haska ko ina.
Amma idan mutum ya mi
ar da ganinsa zai yi tozali da ba
in hadarin da yake ta gangami daga nesa.
Tunanin ta
aita wankin ta soma yi yadda wanda ta gama za su sami wuri akan
ofofin
akunan gidan su ka ji sallamar wasu mata.
Da farinciki Yaya ta tashi daga kan tabarmar da take zaune ta nufi zaure tana cangala
afarta ta hagu wadda shan inna (polio) ya cinye.
Da alama ba
in da aka kwana aka wuni ana zancen zuwansu ne su ka
araso.
"Maraba lale da Altine."
Shewar Yaya da ba
uwar su ka ji daga zauren da taje ta taro su kafin su dawo tsakar gidan hannun da ba
uwar a kafa
arta.
"Oh ni jikar mutum hu
u.
Ashe rai kan ga rai Jinjin?
Ya bayan rabuwa?" Matar ta jero mata tambayoyi su na daga tsaye.
"Sai alkhairi.
Rayuwar nan sai godiyar Allah." Su ka sake rungumar juna su na dariya.
an matan da ba
uwar tasu mai suna Altine ta zo dasu da kuma Hamdi da Zee sai su ka tsaya kallon abin al'ajabi.
Labaran da su ke ji game da juna ashe gaskiya ne don ga zahiri sun gani.
Iyayen nasu sun yi zumunci sosai kafin a haifesu lokacin suna zaman Agege a Lagos.
Abubuwa da dama sun faru wa
anda su ka yi sanadiyar dawowar su Jinjin garin haihuwarsu Kano.
arancin hanyoyin sadarwa da fa
i tashin yau da gobe ya dakusar da wannan zumunta ta makwabtakar gidan haya
aya.
Shekara bakwai kenan da dawowar su Altine Kano su ma amma basu ta
a ha
uwa ba sai da Allah Ya ha
a mazansu da wani da ya san duk su biyun.
A wurinsa su ka sami labari harma da lambobin wayar juna.
Altine kakkaurar mata ce mai fara'a kamar gonar auduga.
Mijinta Maje mahauci ne yana sana'arsa ta fawa.
Da yake kakanninsu
aya duk su na da billensu na gadon sana'ar a kuncinsu.
Akwai ta da kazar kazar don in tana abu sai ka rantse wannan jikin ba nata bane.
Da wannan yanayin nata ta ja Jinjin a jiki duk da farkon zuwanta saboda yanayin mijinta da lalurarta bata sakewa da kowa.
A gidan nasu na iyali goma sha biyu
an ka zo na zo aka taso ta a gaba da tsokana.
Don ma maigidan nata ba
yalle bane.
Bakinsa ka
ai ya ishe su
watar kai.
Idan ya fita ne dai ko ban
aki ta fito zagawa an dinga dariyar tafiyarta kenan.
Sai da Altine ta gama lura da ita ta gane tsoron
an gidan da su ke duk hausawa take yi.
Sai ta zame mata baki harma da hannuwa.
Don idan abin bawa hammata iska ya kama dukan tsiya take yiwa mace la'ada waje.
an Altine
aya lokacin ita kuma Jinjin da ciki su ka rabu.
"Ina Baballe kuwa?" Cewar Yaya cikin yanayi na kewa.
Da jinda
i Altine wadda
anta su ke kira Iyaa (kamar yadda Yarbawa su ke jan sunan) ta bata amsa.
"Ya tafi bautar
asa Binuwe (Benue)"
"Allah Sarki.
Shekara kwana.
Yaron da na tafi na bari yana tatata"
Dariya su ka yi farinciki da jinda
insu ba zai kwatantu ba.
Duk wannan abin da su ke yi Hamdi da babbar cikin
an matan Iyaa kallon gane juna su ke yi.
Ganewa mai cike da tsoro da fargaba a
angaren kowacce bisa dalilai daban daban.
Kamar iyayen sun sani kuwa su ka za
i wannan lokacin wurin gabatarwa juna
an nasu.
"Kina nufin da cikin Hamdi ku ka taho?"
"A'a, yayarsu dai Sajida.
Tsiranta da Hamdi ma ya kai shekara biyar.
Bata nan ne.
Ta tafi Abuja gidan
ar yayata da ta haihu."
Iyaa ta murmusa "Allah Sarki" ta nuna babbar
ar "Sajidan ce sakuwar Ummi kenan, don baku jima da tafiya ba na haifeta."
Yayinda Yaya take da
a hu
u, Sajida, Hamdiyya, Zinatu (Zee) da Halifa, na Altine uku ne.
Baballe, Ummi da Siyama.
Sai da su ka nutsu da gaishe gaishen Yaya ta aiki Zee.
"Maza jeki gidan Lami ki ce ta baki lemukan da na bata ajiya." Ta yiwa Iyaa bayanin sace musu transformer da aka yi kusan wata uku babu wuta sannan ta fuskanci Hamdi "ke kuma ki je wajen babanku ki fa
a masa Altinen Maje ta iso."
Iyaa ta sanar da ita ai babansu Ummi na sauke su a
ofar gidan ya yi waya da maigidan nata.
"Ina jin ya kwatanta masa wurin sana'ar tasa don ya ce can zai je sai su taho tare."
Cigaba da hirarsu su ka yi wanda hakan ya bawa Ummi damar yiwa Hamdi inkiya da su tashi tana son magana da ita.
Ita kuwa sai ta
auke kai kamar bata gani ba.
Hakan ya tunzura Ummi matu
a sai kawai ta mi
e tsaye ta ce tana son shiga ban
aki.
Hamdi na jin haka ta san kwanan zancen.
Cikin
akinsu ta gayyato ta ba don ta so ba.
Duk da gidansu mai tsakar gida ne amma kowanne
aki da ban
akinsa a ciki.
Wannan tsarin babansu ne da ya ce baya so ace komai dare, ruwa ko iska sai an fito tsakar gida idan za a zaga.
Shigarsu
akin ke da wuya Ummi ta juyo fuskarta a murtuke.
"Zan fa
awa Iyaa makarantarmu
aya amma kada ki kuskura
ayin baki yasa ki fa
awa kowa sirrin rayuwata a makaranta"
"To" ta iya cewa don hankalinta a tashe yake.
Yau ruwa ya
arewa
an kada.
Sirrin
oye zai fito fili.
Rai a
ace Ummi ta bangaji kwalarta yadda ta saba cin zalin
an mutane a makaranta.
"Bar ganin nan gidanku ne kin dai san an kusa komawa makaranta.
Kin kuma san ko ni wace ce ba sai an fa
a miki ba."
Ficewa kawai Hamdi tayi daga
akin wani abu na hawa da sauka a
irjinta.
Barazanar Ummi ba ita bace damuwarta kamar yadda zuwanta gidan yake nufin tonuwar asirinta.
Gudun rana irin wannan da wata
ar makarantarsu za ta zo gidansu yasa ta za
i makarantar kwana.
A can
in ma bata da
warar
awa ko
aya.
Tsakaninta da kowa mutumcin gaisuwa ne da kuma taimakon da take yi musu na
arin haske akan karatu.
Allah Ya yi mata baiwar
aukar darasi da zarar an koyar.
Bata ta
a tsallake matakin ukun farko ba tun shigarta.
Sau biyu makaranta na neman iyayenta domin a karramata a gabansu tana da
ilewa.
Na farko ta ce mahaifinta ya yi tafiya.
Na biyu kuma ta ce yana kwance tun kafin ta taho ya yi hatsari ya karye.
Da taga alamun za a bishi gida gayyatar Yaya ta nuna ai maman ke jinyarsa.
Malamin ajinsu da kansa ya gane akwai abin da take
oyewa sai ya sanar da hukuma kada a matsa mata.
Sun riga sun saba ganin abubuwa marasa da
i game da dangin
alibai.
Tunda dai ba karatu aka hanata ba sannan duk dawowa daga hutu da ku
in makarantarta take zuwa ya ce a
yaleta kawai.
Daga lokacin sai dai idan an yi taron ta taho da kyautarta gida.
Bata tsoron duniya ta ga lalurar Yaya amma mahaifinta da shi ya
orawa kansa bata son ana ala
anta su a waje.
Sau tari ita da
an uwanta su kan zauna su kwashewa wanda ya ha
a auren mamansu da mutum irin mahaifinsu duk kirkinsa albarka.
Fitowarta tayi daidai da dawowar Zee.
Ta ajiye ledar hannunta ta tafi
auko tray za ta
ora musu.
Sai ga Ummi ta fito ta dubi Hamdi tana murmushi kamar gaske.
"Don Allah ba ke ce Hamdiyya Habib ta Rumfa Hostel ba?"
Murmushin dole Hamdi tayi ganin iyayen nasu sun dawo da hankali garesu.
"Ni ce.
Kema kamar na gane ki."
"Ummi ce, Ummi Maje.
A 'F class' nake shi yasa ba lallai ki sanni ba."
Iyaa ta hau murmushi wanda kuma da wuri ya koma shan kunu da ta gane me hakan yake nufi.
"Kin dai ji kunya wallahi.
Karatu kamar cin
wan makauniya.
anwar bayanki ma ajinku
aya?"
Ta gyara zama ta yiwa Yaya
arin bayanin asalin da
anci irin na Ummi wanda ya janyo ake ta yi mata repeating.
Wannan shekarar ma don an riga an saka ranarta ne babansu ya ro
i alfarma aka kaita aji shida saboda ta gama a aurar da ita.
Basu san rashin
ari ba shi ka
ai ne matsalarta ba kamar yadda Hamdi ta sani.
Idan kana neman irin
aliban nan da ko bayan shekara ashirin in ka tambayi abokan karatunsu game dasu sai dai su bi su da 'Allah Ya isa' ko ka ji ana cewa 'a dai yi shiru' idan mutum ya riga ya mutu to Ummi Maje ce.
Bully ce lamba
aya!
Lokaci guda rana ta
auke, hadarin ya sake duhu ga iska mai
arfi tana ka
awa.
Babu shiri hirar ta koma cikin falo.
Zee ta
arasa shanya wa Hamdi kayanta ita kuma ta shiga kitchen ta ha
a salad bisa umarnin Yaya.
Abu
aya hakan yake nufi.
Abbansu yana tafe da abinci kuma tabbas a yau Ummi za ta sami makamin cutar da ita.
A baya ko kallo basu ishi juna ba tunda duk jarabar mutum dole ya ha
ura indai Hamdi ce.
Bata shiga sabgar kowa balle a kai ga yin fa
a da ita.
Tsananin fa
uwar gaban da taji lokacin da aka yi sallama daga zauren gidan yasa ta shar
e hannu wurin yankan albasa.
Yayyafin da aka soma bai hana kowa jin sallamar mace ba.