← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 93

Sashe 93

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

“Hijab Dada ne wanda take yawan sakawa idan zata yi sallah, akwai kur'anenta da carbi a ciki, sai kuma hotonta da namu lokacin da muke kanana, maybe zai rika tuna miki da ita”

Hannu biyu ta saka ta karba sai ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Idanuwan Zain kuma suka cika da hawaye, daukar sauran ledodin Hafsat tai ta aje mata gaban, sannan ta rika hannun mijinta ba tare da kunyar komai ba suka fito daga gurin.
The following day suka koma Paris, har lokacin Zain baya cikin dadin rai da natsuwa, duk kuwa da yawan kiran waya da Mai Martaba yake nasa da kuma Anty Ummi suna bashi hakuri akan rashinta. Tun daga lokacin Zain be sake wani farinciki ba domin mutuwarta ta suna masa da mutuwar Haleema da Farhat da kuma mahaifiyarsa, sai dai yana kokarin boyewa gudun kar ya shiga hakkin Hafsat. But when he truly findout tana da ciki sai ya nemi duka damuwarsa da bakincikin ya rasa, hankalinsa da tunaninsa sai ya koma kanta da kuma rainon cikinta. Abunka da kwararen likita har numfashinta kula yake da shi idan ya canja.

Cikin so da kauna ta raini cikinta, bata kusa da iyayenta da kuma yan'uwan twins amman kusan kullum sai sun yi waya da ita, ta bangaren yan'uwan Zain ma haka, wani lokacin har kunya take a yadda suke tambayar idan taji wani abun. In a day idan baya gida wuni take da waya makkale a kunnenta especially lokacin da cikin ya tsufa sai yai ta jin kamar idan baya jinta a waya ko a kusa da shi wani abun zai iya samuwarta ne.
Sosai ta so ya maida ita gida ta haihu amman ya ki wai can ba za'a kula da ita kamar yadda shi yake yi ba, and if wani abun ya sameta ko dan cikinta ba zai iya yafewa kansa ba. Hajiya Hadiza da Momy ma sai da suka masa magana akan ya dawo da ita Naija ta haihu sai yai musu karyar wai idan ta samu canjin iskar da take shaka cikinta zai iya samun matsala, ba dan sun aminta ba da zancensa suka kyaleta ba sai dan ganin yafi son tana kusa da shi din.

Ranar da zata haihu bakin har kunne sabar raki, abu ya kai ga ma'iya 😂, you know abroad yadda suke barin mazaje aure su shiga dakin haihuwa tare da matan su, yana kusa da ita holding her hand duk wani motsi da take da numfashi yana ji kuma yana kallonta, haihuwa is not easy sai duk tausayinta ya kama shi, tana jin kamar abun ya dawo gareshi maybe shi zai daure da duk zafin da zaiji. She spend few hours tana nakuda kamin ta haiho masa twins. Namiji da mace, a take ya daga waya ya fada musu daman tun tana nakudar ya fada musu cewar tana asibiti. Daga Masarautar Rishim har Kaduna Family house dinsu sai aka rushe da murna da farinciki.
Cikin Koshin lafiya ta haifi yaranta, sai dai ba su barta ta koma gida ba dai tai bachi ta huta suka bata kulawar data dace, basa wankan ruwan zafi irin namu na hausawa, magani kawai suka bata, a gida kuma Doc Zain na kokarin ganin ta ci abu mai kyau wanda ya dace. Hajiya Hadiza ce da wasu kanensa biyu dawacce zata kula da jarirai aka zo dasu paris.
Ranar suna Namijin ya ci sunan Mai Martaba aka masa alkunya da Amir, macen kuma aka saka mata Sa'adatu wato sunan Dada, aka mai ta alkunya da Amira. Yan'uwa da ke naija sun yi sunansu su kan akan an yanka ragon kawai amman babu wani taron sunan saboda na kamar nan ba ne, abokansa yan naija ne akwai suka kawo matansu wasu kuma suka zo.
Sai da Hajiya Hadiza tai sati biyu sannan ta koma Hajiya Zara ta zo ita ma tai two weeks ta koma, ko bayan arba'in sai da Hafsat tai wata biyu a can sannan ya yarda suka ta fo naija. Babu wanda baya farincikin da ganinsu ga twins dinsu kyawawa masu kama da su, wannan karon kin yarda tai ta bishi su koma a dole shi kadai ya koma, sai duk ya ji dabam, he really miss his wife and his twins. Shi da kansa ya nemi aje musu aikinsu ba dan sun so ba, ya hada komai na su ya baro kasar.
Daya dawo sai ya kara gyara asibitinsa mai zaman kansa wacce Ibrahim ke kula da ita ya koma kan aikinsa. Hakan ya fi komai yi ma Mai Martaba dadi fa kuma hafsat ko ba komai tana kusa da gida duk abunda akai zata samu zuwa kuma zata ji. Twins na da shekara biyu da rabi ta sake samu ciki ta haifi wasu twins amman wannan karon duk maza, sai Zain ya saka musu Muhammad da Ahmad, a cikinta na uku na namiji ta sake haihuwa wato Mahmud, bayan shi ta haifi Namra ( Haleema) da Aisha (Farhat) sai dai da dai daya ta haifesu ba kamar twins dinta na farko da kuma na biyu ba.

Dukan wata kulawa da ko fa kauna Hafsat tana samu daga gurin mijinta ,har take jin kamar ta fi ko wace mace sa'ar abokin rayuwa, ga yan'uwansa kamar su hadeta ita da yayanta, dukam wani abu daya faru a baya ya zame mata kamar tarihi, ta wani bangare kuma ya zame mata darasin rayuwa, wanda za a ciri mai amfani a ciki a watsar da sauran. Daga ita har shi Rayuwata ta zo musu da abunda ba su zata ba, gashi a yanzu tana zaune da matar da yafi kauna fiye da ko wacce, yana tare da iyalinsa kamar kowane mai aure kuma yana farinciki a gidansa, abunda be taba sawa rai ba. Yana yawaita godiya ga Ubangijinsa ta hanyar sallah azumi da kuma dakata, lokaci zuwa lokaci Al-hamdulillah shine akwai abunda yake fito a bakinsa....

Kamar yadda nima yake fitowa a bakin AL-HAMDULILLAH TSUMMA AL-HAMDULILLAH TSUMMA AL-HAMDULILLAH.
Godiya ta tabbata ga Ubangijin Khadija, wanda ya halliceta tun babu ita ya rayata har ta kawo yanzu, kuma ya bata ikon rubuta HAFSATU MANGA, ya amince mata ta gamashi cikin jindadi da koshin lafiya. Al-hamdulillah Allah na gode maka.
Tsira da aminci su kara tabbata ga Mijin Khadijatu (A. S) kuma angon Khadija (AS) wato Annabi Muhammad (S. A. W).

Allah ina tawassali da sunayenka tsarkaka, ka yafe min inda nai kuskure ko tuntuben halshe, Allah ka sanya rubutuna ya zama mai amfanin ga al'ummar Annabinka, kuma ya zame min sanadin tsira.

Godiya ta Musamman a gareku masoya na masoyan kwarai masoyan gaskiya, masu son na har cikin ransu wato members din Hafsatu manga Paid grp, baki yayi kadan ya gode muku, na irin goyon baya da kuka bani. Na gode na gode na gode sosai Allah ya bar zumunci mai dorewa har aljanna.

Ummu Faisak
Asma'u Badamasi
Hajiya Zainab Kano (Mama)
Maman Hafiz (Maman Candy)
And Zubaida Malam
You people are like family to me, ku kuke fara goyan min baya a dukan abunda zan yi ko ya shafe ni. Allah ya bar zumunci da so da kauna.

Jinjina a gareki Mom Iman I'm in love with your comments every day. And all members of HAFSATU MANGA COMMENT GRP.
Daga karshe ina neman yafiyar wanda na batawa cikin rashin sani ko ganganci, ina rokon addu'ar a duk lokacin da sakon mutuwata ya riskeku 🙏 i will surely miss you guys 💔😭 but don't worry ana tare we have each other numbers.

Best regards 🌹😍♥️
Khadeeja Candy♥️🖤

Stay bless.😍
One heart♥️
One love♥️
Chapter 93 · 0% Book details