Sashe 34
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya kalleta zuciyarsa cike da so da kuma kaunar matarsa, sai ta mike tsaye tana murmushi ta nufi dakinsa dan aje kayan da ke hannunta.
Bayan ya gama wankan ya zo falo suka ci abinci a tare, a yammacin ranar ta lahadi be labarta mata komai ba sai Lagos da abunda ke cikin Lagos, wani abun ya bata mamaki wani ya bata dariya a haka dai ta yi shawa'ar wata rana idan zai sake zuwa wani worship din zata bishi ta ga Lagos da kanta.
Bayan sallah isha'i tana zaune daki a gaban madubi tana daura dankwalin atamfa ya shigo rike da wani dan karami abu mai kamar akwati fuskarsa dauke da murmushi kamar kullum, a gefen gado ya zauna yana kallonta itama sai ta kalleshi ta dauke ido. Hannunta ya kamo ta danka mata wani awarwaron azurfa mai dauki da sunanta wato Maman Hafsat. Tsalle ta yi ta dire tana ihu da murna.
"Habib Ina ka samo?"
"Na musamman ne ni nasa aka kera min shi a can Lagos din, kin san kin fada min idan Allah ya baki ya mace zaki saka mata Hafsat shiyasa na ce ya rubuta Maman Hafsat a jiki"
"Na gode sosai Allah ya saka da alheri"
"Amin, wannan kuma na yar mu ne Hafsat... "
Ya karasa yana mika mata karamin na yara mai dauke da suna Hafsat. Karba tayi sai dai bata murna kamar yadda take a karban na farkon, shafa awarwaron ta yi idonta cike da kwalla.
"Kin fara ko?"
Ta share hawayen da suka zubo mata.
"Kawai ina tunanin lokacin da zamu samu yar ne har mu saka mata awarwaron"
"Kina tunanin Namiji zamu samu?"
"Ina tunanin zuwan haihuwar ne Habib"
Sauka ya yi daga inda yake ya gurfana kasan kuiwoyinsa ya dora hannayensa saman cinyarta.
"Rufaida, komai fa na Allah ne, sau nawa zan fada miki ki daina saka kanki a irin wannan damuwar, kin san matsalar ba daga ni ba ne, kuma ba daga ke ba ne, kawai akwai lokacin da Allah ya diba mana ne wanda dole sai mun cin ma adadin kamin mu samu haihuwar, kuma na miki alkwari ba zan sawa dan kowa wannan sunan da kike so ba sai yarki"
"Idan kuma Allah ya kaddara ba da ni zaka haihu ba fa?"
"Kai Subhanallah Rufaida ana baki kina roko, wannan wace irin magana ce haka, yau ma daga dawowata bata min rai zaki yi?"
"Ka yi hakuri Habib nasan haihuwa na Allah ne, amman abun yana damuna yadda yan'uwanka suke dora laifin a kaina yana damuna, kai kuma kaki ka yi musu abunda suke so, ni kake jawa kiyayyar ko jiya sai da Hajiya ta zo gidan nan tana rokona akan na barka ka yi aure, bata hana na mallakeka ba amman na barka ka yi aure tana son ganin jikokinta"
"Itama ta yarda kin mallake ni kenan?"
"Mi zai sa ba zata yarda ba? Dan me zata baka umarni kara aure kaki karawa? Kai kanka na tabbatar kana son ganin jininka Habib"
Ta sauka kasa daga saman kujerar tana rokonsa hawaye na kwaranya a idanuwanta.
"Na hada ka da girman Allah Habib na rokeka dan Allah dan Manzonsa, ka kara aure dan Allah ka yi aure kamar yadda Hajiya da yan'uwanka suke so, kai kanka kana son ganin jininka Habib, kuma idan kayi aure zaka wanke ni daga zargin da yan'uwanka suke min na cewar na mallakeka, wata kila ma ka samu haihuwa kamar yadda suke so"
Mikewa ya yi tsaye ba tare da yace da ita komai ba ya fice ya bar mata dakin tana aikin kuka. Har ga Allah bata son mijinta ya kara aure, domin babu mace da take zaman lafiya da mijinta tana son shi yana sonta, ta so ya auro wata ko da kuwa yan uwansa suna sonta ne balle basa sonta, amman a yanzu ya zame mata cilas ta rokeshi ya yi auren saboda farincikin mahaifiyarsa ganin cewar shi kadai ta haifa kuma tana son ganin jikokinta.
Ko wane gidan aure yana irin nashi kalubale da ma'aura suke samu kansu a cikin, wata ta kan zo da sauki wata kuma mai tsanani, wata akan samu mafita awarware wata kuma ta dauwama har a abada! Rayuwar auren Rufaida da Habib rayuwa ce mai kyau kuma abar burgewa ga kowa, irin yadda suke nunawa junansu so da kulawa kai kace a kwai daya suka fito, basa da matsala ta ko'ina, Habib baya son bacin ran Rufaida da ka bata mata rai kara ka bata masa kamar yadda itama take kokarin gujewa duk wani abu da tasan zai sosa nasa rai, hakan yasa mutane suke zargin cewa ta mallakeshi baya yi komai sai abunda ta ce, basu da matsala ta ko ina face rashin haihuwa da Allah ya jarrabi Rufaida da ita kamar yadda yake jarrabar wasu daga cikin bayinsa. Rashin samun haihuwa ita kadaice matsalar dake damun Rufaida da Habib, babu irin neman maganin da basu yi ba na gida da na asibiti, babu ranar da basa addu'a dare da rana akan Allah ya basu haihuwa, dukan asibitin da suka je ana fada musu cewar Habib bashi da wata matsala balle kuma Rufaida da mahaifarta take lafiya kalau kawai dai lokacin haihuwar ne beyi ba, wanda Allah ya riga ya rubuta adadin lokacin da hakan zai kasance, wanda bayi da yawa basu gane hakan ba, ciki kuwa har da yan'uwan Habiba da kuma mahaifiyarsa, sun kasa yarda cewar Rufaida bata da wata matsala, suna tunanin Habib yana fadar hakan ne kawai domin ya kareta, wasa wasa kiyayya ta fara shiga tsakamin Rufaida da yan'uwan Habib da kuma mahaifiyarsa, ganin an kwashe sharakara goma sha daya Rufaida bata taba batan wata ba balle bari (miscarriage), har ta kai Rufaida bata son shiga cikin yan'uwan Habib ko kuma ta kusanci Mahaifiyarsa saboda kori da habaici da ake mata.
Mahaifiyar Habib ta yi iya hakuri da daga kafa wa Rufaida wanda take tunanin ya kamata ace Rufaida ta gano hakan da kanta amman kasa ganowa har sai da ta fito fili ta nuna mata tana son danta ya kara aure, da gangan Habib ya buga kafa da kasa ya ce shi ba zai kara aure ba, a tunaninsa idan har ya kara aure be kyautawa Rufaida ba, kuma zata shiga damuwa. Aka kida aka raya aka daka Habib ya tsaya kai da fata akan ba zai kara aure ba wai shi ya yarda daga Allah ne, wata kila lokacin haihuwar ne be yi ba. Lokuta da dama Mahaifiyar Habib takan sa Rufaida a gaba tana rokonta data bar danta ya yi aure saboda ya samu jikoki tana son ganin jikokinta saboda shi kadai ta haifa.
Tun Rufaida na dauko abun wani iri har ta fahimce cewa Hajiya Larai wato mahaifiyar Habib ta yarda da zugar mutane da ke cewa ta mallake Habib baya ganin kowa sai ita kuma baya yin komai sai ta ce ayi.
Wannan matsalar ce ta saka Rufaida a damuwa, ita da kanta ta zo tana neman ya kara aure amman ya ki wai shi bashi da ra'ayin kara mata biyu, idan ta matsa masa har kaurawace abincinta da shimfidarta yake amman hakan be dame ta ba, ita dai burinta ya kara auren kamar yadda mahaifiyarsa take so.
*** *** ***
Bayan ta gama kukan ta mike tsaye ta bi bayansa, a falo ta zame shi zaune saman cushion ya hada kai da guiwa ya noce kansa kana gani kasan damuwa ce tayi masa yawa.
"Kana da son kanka Habib abunda yake faranta maka rai kawai kake, ko da kuwa hakan zai bakanta maka rai ne, kana kokarin ganin ka faranta min ko da kai naka ran zai bace sabo...."
"Saboda na san hakan zai dawo min da bakincikina i zuwa farinciki, dukan abunda zai faranta miki rai shi zai faranta min rai, miyasa Hajiya ba zata fahimci cewar rashin haihuwar mu daga Allah ba ne?"
Ya karasa mata tare da dagowa ya kalleta.
"Miyasa kai ba zaka fahimci halin da Hajiya take ciki ka kara auren ba?"
"Na fada miki bana da ra'ayin mata biyu"
"To ka saki ni ka auro wata...!"
Ba shiri ya tashi tsaye da sauri yana kallonta tare da mamakin kalamin da ya fito daga bakin matarsa, duk irin so da Rufaida take masa yau har ta iya bude baki ta ce ya saketa ya auro wata?
"Da bakinki kike cewa na sakeki na auro wata? Kin san abunda kike fada kuwa?"
Ta gyada masa kai hawaye na zuba a idonta.
"Na sani, matukar hakan zan faranta ran mahaifiyarka da yan'uwanka da kuma kai kanka na yarda ka sakeni ka auro wata, kai kanka kana son haihuwa Habib ina karantar damuwar a fuskarka, ina ganin shaukin da ke fuskarka a duk lokacin da idanuwanka suka sauka akan yara, ina jin addu'o'in da kake yi cikin dare Habib, wata kila ni Allah be yi zan haihu da kai ba, miyasa ba zaka auri wacce zata haifa maka yaya ba?"
Ta taso ya nufota yana fadin.
"Ke kadai zaki haifa min Hafsat Rufaida..."
Hannu ta daga masa tun kan ya karaso.
"Karka sake shagaltarda ni da kalamanka, kar zuciyarka ta sake yaudaraka ka saba umarnin mahaifiyarka, ina jiye maka tsoron fushinta Habib ina jiye maka tsoron rana da zata fusata tayi mummunan furuci akanka Habib, ka ji tsoron Allah mahaifiyarka ita ta dauki cikinka tun kana kwana daya har ka kai wata tara ta haife ta raineka har ka girma ka hadu da ni na aureka, shin idan ban zame mata silar farinciki ba taya kai zaka zame mata silar bakinciki? Kai ma zaka zo dan da ka haifa ya tsabawa umarninka? Iyaye suna da muhimmanci Habib Annabimu sai da ya kira uwa sau uku sannan ya kira uba, ina son ka sani fushin Allah yana tare da fushin uwaye, kuma yardarsu tana tare da yardar Allah ina tsoron kar wata kai ma danka yai maka haka Habib-"
Tunda ta fara maganar yake kallon hawayen da ke zuba a idonta har ta kai aya, yasan gaskiya take fada masa amman shi kuma ya rasa yadda zai fahimtar da Hajiya da ita kanta Rufaidar yadda ya yarda da abunda Allah ya rubuta zai same shi.