← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 93

Sashe 47

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Bana shakkar a ci amanata, kai ne dai bana son ka ci amanar wannan yarinyar, zan ninka maka abunda wadanda suka baka, har sai ninkin ya nimka sau dubu ka fada min da yarinyar nan take ko kuma ka nemo min ita”

“Da biyana akai na yi wannan aiki, kai ai tun kamin ya kaimu haka zan fada maka farashin da zaka biya na warware maka komai, miyasa ka kasa ganewa ne? Kusanci na da kai yafi kusancin wanda zai hadu da ni da rana tsaka ya nemi na tozartaka ko iyalanka ya biyani”

Zain ya katse kiran, tare da kunna motarsa yana fadin..

“Ba zan iya barin yarinyar nan a hannun mutane da bata sani ba, hankalina ba zai taba kwanciya ba”

Cikin yan mintuna ya isa gidan Ibrahim, sai kace ba shekaranjiya ya gama fushi da shi ba, bashi da wani amini bayan shi wannan dalilin yasa ko sun samu tsabani sukana shirya kansu domin ko wanne baya iya gi sai da dan'uwansa.
A harabar gidan ya tsaya ya kira Ibrahim a waya, ya sanar masa yana waje.

“To ka shigo mana gidan bakonka ne”

Yana sauke wayar ya fito cikin motar rike da rigar ya nufi kofar falon, knocked yai sannan ya tura ya shiga, a zaune ya samu Ibrahim Falmata na gefensa zaune sanye da Hijab tana gyara masa hannun rigarsa.

“Yanzu bayan ka kore budurwata mai zaka zo nai maka?”

Zain ya yi murmushi ya zauna saman kujera yana gaisawa da Falmata.

“Ango ina amarya”

“Tana lafiya ta ce a gaishe ki”

“Ina amsawa nima ina gaisheta, kuma a fada mata angonta ya kori Abokiyar zamana a gurin aiki ba mu jidadi ba, gashi kuma Abban Siyama yaki ya fada mana laifin da tai”

“To ai sa za ki yi ya aurota ya kawo cikin gida sai na san da gaske kina sonta”

Falmata tai dariya, tare da tashi tana fadin.

“Me kake ci na baka na zuba? Ba jimawa zai kawo min kanwata, Next week zan shigo na ga Amarya”

“Allah ya kai mu”

Sai ta shige daki sannan Ibrahim ya kalli rigar da ke hannun Zain ya kalleshi ya ce

“Kamar rigar Mama”

“Ita ce, Ibrahim ba zan boye maka ba, gaskiya na fara zarginka akan lamarin nan kai ma kana da sakaci, idan ma Hafsat ce sikar komai har da laifinka, tun farko sai da na ce karka sako yarinyar nan a ciki amman kace ka aminta da ita”

“No i trust her, kawai dai kasan mata wani lokacin ba a sirri da su, kuma wani zai iya bugun cikinta ya ji wani abu, amman abunda na sani ba zatai unkurin cutar da kai ko yarinyar nan ba, na san dai garin dumi taje ta fadawa wani ko kuma wani abun, wannan dalili yasa nima nake fushi da ita”

“Yanzu ni abunda na ke so, ka yi sanarwa ka zan saka naira millions uku ga duk wanda ya gano inda yarinyar take kuma ya kawo ta gurinka, kai zaka saka sanarwa kuma number za a bada”

Ibrahim ya tsaya kallonsa yana mamakin lamarin Zain.
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 34

Kamin ya isa cid din duk ya bi ya matsu, a hanyarsa ne ya kira Anty Ummi ya sanar mata duk da yasan Dcp zai kirata, sai ta sanar masa tana ma gurin.
A harabar gurin ya faka motarsa ya fita ya shiga cikin office din. Anty Ummi da Alhaji Masa'ud na zaune a kujera daya, Yayinda Alhaji Salisu yake zaune a kujerar daje facing din ta Dcp, a dayar kujerar ya zauna ya zaune wacce ke gaban teburin Dcp. Bayan sun zauna Dcp ya shigo yana rike da hannun Hafsatu manga, mutanen da suka ce sune iyayenta suna biye da shi.
Fuskarka ta jike shakaf da hawaye har idonta ya kumbura. Kin daga kai tai ta kalli kowa har Dcp ya zaunar da ita saman wata kujerar. Sai da ya gaisa da su sannan ya kalli Hafsatu manga ya ce

“A jiya Zain yake fada mana cewar Hafsatu manga tana gurin wani Dsp dake kaduna, so na buga na bincike Dsp din yace aiki aka kawo masa ita ya fadwa kanwarsa ita kuma tana ganin hotonta sai ta gane taa fadawa Zain shi kuma ya sanar da ni, bana son muja abun da nisa ne shiyasa ban zafafa bincike ba, kamar yadda Alhaji Salisu ya bukaci a kashe maganar”

“Amman aikinku ne Dcp, ya kamata ku yi bincike ko dan tabbatar da gaskiyar lamari”

Cewar Zain. Sai Alhaji Salisu wato mahaifin Anty Ummi ya daga masa hannu.

“A kashe maganar kawai zai fi, ka damka yarinya ga iyayenta, hankalin kowa ya kwanta”

Ya karasa yana kallon Dcp. Sai Zain ya ce

“Amman ka tabbatar iyayenta?”

Dcp yayi dariya.

“Zain ke nan, ga yarinyar nan zata tabbatar maka da bakinta”

Ya kalli Hafsatu manga.

“Ke daga kanki ki kalli can, wacece waccan matar....?”

Ta daga kanta a maimakon ta kalli matar sai ta kalli Zain tana ta hawaye kamar an bude fanfo, ji take kamar ta fada masa gaskiya amman tana tuna maganar da Dcp yai mata cewar zai fasa kanta da bindiga matukar ta fadi gaskiya, ko yanzu ma da zasu shigo sai da ya jaddada mata.

“Mama... Wacece wacan?”

Ya kira sunanta a hankali sannan ya nuna mata matar. Sai a lokacin ta kalli matar, sai kuma tai shiru kamar ba zata ce komai ba.

“Ma... Ma... Ma... Ma.. ”

“Wacan fa?”

“Baaba.. Baba... Baba...”

Zain ya ji babu dadi, yasan duk yadda aka yi ba iyayenta na gaskiya ba ne.

“Kin tabbata? Kin san kin fada min cewar mamaki mahaukaciya ce, kuma baki san inda Babanki yake ba, kin tuna?”

Sai kawai ta fashe da kuka.

“You see wadannan ba real parents dinta ba ne ya kamata kui arresting dinsu”

Anty Ummi ta kira sunansa, ganin yadda yake tada jijiyon wuya, bata son ya nuna kulawarsa a kan yarinyar a gaban mahaifinta.

“Zain dan Allah”

Kallonta yai kamar zai yi magana sai kuma ya tashi ya fice daga office din. Su Anty Ummi kam basu bar asibitin ba sai da aka bawa fulanin Hafsatu manga, aka kashe case din sannan suka dawo gida.
Cikin bacin rai Zain ya shigo office, yadda ya banki kofar office din ma ya isa ya karantar da kai haka, telephone dinsa ya dauka ya kira Ibrahim. Ba bata lokaci sai gashi ya shigo office din hankalinsa a tashe dan ya fahimci hali da abokinsa yake ciki.

“Yarinyar ta san komai Ibrahim, da ita aka hada kai a cuci mama, wadancan banzaye mutanen ba iyayenta ba ne, na karanci hakan a idonta, kuka take sosai magana take son tai min amman ta kasa saboda tsoro”

Ibrahim ya dafashi.

“Ni ban gane kan maganar ka ba, zauna please”

Ya zaunar fa shi, sai Zain yasa hannu biyu ya rufe fuskarsa, yana sauke numfashi a hankali, kokarin daidaita fushinsa yake, kokarin bawa zuciyarsa hakuri yake.
Dagowa yai ya kalli Ibrahim yana ware yatsun hannunsa yana hadewa.

“Ka rubuta mata takardar sallama, kuma ka fada mata idan wani abu ya samu yarinyar nan sai na rufeta, ko kuma nasa ai mata mugun wulakanci”

“No no no Zain listen, babu hannun Hafsat a cikin matsalar nan, kawai tana kokarin taimako ne”

“Wane irin taimako saboda tana budurwarka ai ba zaka ga laifinta ba, ka koreta karta sake shigo min asibiti da sunan aiki, idan kuma kai ba zaka iya ba ni zan iya zuwa nai mata wulakanci”

“Zain duk kabi ka rikice akan yarinyar da baka san inda ta fito ba, sanadin yarinyar aka kama Anty Ummi yanzu kuma muna cikin wannan case din, wannan wane irin abu ne?”

“Ibrahim fita ka bar min office dina”

“Zain.... ”

“Just go please, and make sure you fired her”

Ibrahim yafi kowa sanin halinsa idan yai fushi baya jin rarrashi kuma baya saurarawa kowa. Dan haka ya fice shima cikin zafin rai.
Zain be bar office din ba sai dare, ko da ya isa gida baya iya tantance halin da yake ciki, iyakar abunda ya sani yana jin jikinsa kamar marar lafiya, a bakin kofar falonsa ya tsaya ya kira Dcp a waya, sai da tai ringing kamar zata katse sannan ya dauka.

“Yariman yarimawa”

“Dcp ina yarinyar nan take?”

“Na bada ita ga iyayenta yanzu haka sun kama hanyar Nijar, daman ta fada min ita kawai suke jira zasu koma gida”

“Kai baka ga alamar ba iyeyenta ba ne na gaskiya? Miyasa ba kai bincike ba?”

“Binciken mai ko?”

Wani dogon tsaki Zain yaja ya jingina da kansa da kofar. Tun can farko be santa ba, daga lokacin data shigo rayuwarsa natsuwa da kwanciyar hankali suka barsa, he live a lokacin da be san da wanzuwarta a dogon kasa ba, yanzun ma zai iya rayuwa ko babu ita, even if ba iyayenta na gaskiya ba ne, zai runtse ido ya kyale komai domin samawa kansa salama.

“Good bye...”

Ya furta ciki murya marar dadi, idonsa na rikewa zuwa ja, saboda bacin rai da damuwa. A hankali ya tura kofar falon ya shiga, kukan Farhat ne ya fara masa marhaba da zuwa, daga kitchen take amman kuka take ta rairawa iya karfinta. Kai tsaye ya nufi kitchen din da fuskar nan tasa babu annuri. Zaune ya sameta ta rike kafa tana ta kuka sosai, ya risina yana duba kafar.

“Minene?”

“Ciwo take kamar zata cire”

“Ai kinsan tana ciwo kika taso kika zo kitchen mi kika zo yi”

“Na yi miya tuwon zan yi”
Chapter 47 · 0% Book details