← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 93

Sashe 78

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mai Martaba ya kalleta a hankali.

“Dukan abunda kike ji Ikram ba ki kai ni ba, amman Wallahi na rantse miki da Allah da yau ke ko Hajiya ko Zain wani zai kashe rai, to sai nasa kotu ta zarartar masa da hukuncin abunda ya aikata, itama wasu rayukan ta kashe kuma ba dan ba a son su ba, dokar Allah ce duka wanda ya kashe rai a kasheshi, domin rai be fi rai ba, itama kanta idan ba hukuncin aka yanke mata ba ba zata taba samun natsuwa da kwanciyar hankali ba, yana daya daga cikin dalilin daya sa ta fadi gaskiya ba tare da an matseta ba”

“Amman Mai Martaba za a iya biyan diya...”

Ikram na rufe baki sai ga Dada Yalwa ta turo kofar falon ta shigo, duk cirko cirko suka yi a zatonsu zata gane abunda ya faru ne, musamman Ikram da ke aikin sharar kwalla. Gurin da ta saba zama ta nufa ta zauna tana fadin.

“Yanzu Zain ya kirani wai ya raka Hameeda airport zata tafi Kaduna gurin Alhaji Aminu (Yayan mahaifiyarta), wai ta bada shaidar da ake bukata shine ta koma can har a gama, ya ce wai idan ta fada min ba zan yarda ba shine tace kar a fada min zata kirani idan ta isa, kuma nata kira wayarta na kasa samu”

Ta fada fuskarta na nuna tashin hankalin da ke zuciyarta,yanayin yadda tai yi maganar zaka fahimci cewar sam bata yarda da abunda Zain ya fada mata ba. Ikram ce take gyaran muryar tai karaf ta ce

“Dukanmu nan mun san da tafiyarta Dada, daman tace kar a fada miki ne saboda ba zaki barta ba, ita kuma ta gaji da zama gidan nan wai tafi son ta tafi sai idan an gama shari'ar gaba daya sannan zata dawo, tun shekaranjiya ta fadawa Mai Martaba maganar tafiyar”

Dada ta kalli Mai Martaba da idanunwata na tsofi dake nuna tana daf da yin kuka.

“Ki kwantar da hankalinki Hajiya, ni kaina na fi son tai nisa da nan har sai komai ya lafa, domin bana jindadin rashin jituwar da suke samu da Zain”

Mai Martaba ya fada mata.

“Allah yasa gaskiya kuke fada min, daga zuwa bada shaida sai kuma ace ta tafi kaduna, ko dai wani abun ne?”

“Babu komai Hajiya, idan ta isa ai zata kiraki ko kuma ke ki kirata domin tabbtarwa”

“To Allah ya kaita lafiya”

Ta tashi cikin rashin kuzari ta fice daga falon ba dan ta gamsu cewar hakan ne dalilin zuwanta Kaduna ba, zuciyarta na raya mata ba hakan ne gaskiyar ba akwai dai abunda suke boye mata.

*** *** ***

Ya sauke wayar daidai lokacin da Ibrahim yai parking a harabar gidan. A hankali Zain yaja numfashi ya sauke tare da kai hannu zai bude motar.

“Are you happy now?”

“No”

“Sad?”

Ibrahim ya tambaya.

“No, idan na yi farincikin Mama ta fito, Hameeda tana gidan yari, Dada Yalwa fa? Akwai shakuwa sosai a tsakaninsu, kuma ba zata taba yarda ba ni da laifi ba, wannan abun ma zai iya sanadiyar mutuwarta”

“Amman Hameeda ta cancanci dukan wani hali da zata shigo, ni wallahi na yi farinciki da ta fadi gaskiya tun shari'ar bata je nisa ba, kuma bata wahalar da kowa ba, da ace gaskiya bata bayyana ba, da Hameeda zata tai ta kashe maka mata ne har illa Mashallahu”

“Yeah she deserve it amman bana son ganin mutuwar Dada, i won't forgive myself, tunda ta kashe yar'uwarta zata iya kashe kowa ma, amman ina jin da an gama shari'ar nan zan bar kasar nan zan koma paris na zauna”

“Hakan ma zai fi, amman ban ce ka zauna kai kadai ba, you should engage yourself with something kar kaje kai ta tunani wani abun ya faru da kai, ka yi applying a cikin hospital dinsu na san zasu dauke ka tun da kana da takardu masu kyau, ka zauna a can ko da na shekara hudu me ko biyar”

“Hudu biyar? No sai dai yadda hali yai, bana son zama kasarnan kwata kwata kuma ko na dawo ba zan zauna a nan ba”

Yana gama fadar hakan ya bude motar ya fita.
[4/1, 1:53 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *54*

Daga kotun suka nufi gidan Alhaji Salisu wato mahaifinshi, a nan suka ci suka sha shi da wani kanen Rufaida dan sauran tuni suka kama hanyar komawa Kaduna.
A nan ma Hafsat ta ga gata ba a barinta ta zauna ita kadai saman kafafun wani ko wata daga cikin kanen Alhaji Habib, ta sha hotuna a wayar kanenta sai yabon mahaifiyarta suke dan yanzu ne suke kara tabbatar da kamar da ke tsakaninsu. Da yamma ya kama hanyar Kaduna tare da Barrister Hassana da Hafsat wace ke ta kuka wai ita ba zata je ba sai anje da Zat tana ganin kamar wani abu za su mata.

Da magariba suka sauka Kaduna, daga airport din Barrister Hassana ta nufi Asibiti gurin mahaifiyarta, Alhaji Habib da Hafsat manga kuma suka nufo gida, Jamil kuma ya nufi gidansu wato family house din su Rufaida, cike da farinciki Alhaji Habib ya shigo gidansa tare da Hafsatu manga yana jin kamar a mafarki ne, yau ga shi ya yar da yai shakara da shekaru yana memanta, gudan jininsa yar Rufaida yar da ya kwallafawa rai tun kamin ta zo duniyar ma. Direbansa na farki mai gadin ya zo da gudu tana daga masa hannu alamar gaisuwa.

“Barka da zuwa Alhaji”

“Yauwa Barka Sulaiman, mun same ku lafiya”

“Lafiya kalau, Alhaji ka yi baki tun dazu suke suna jiranka”

“Su waye?”

Ya tambaya yana kokarin fitowa daga cikin motar.

“Wallahi ban sansu ba, amman dai suna tare da wata mata marar lafiya, da suka zo sunce nan ne gidan Alhaji Habib Salisu na ce musu ce shine suka ce ga matar da kake nema am samu”

“Wacece ina suke?”

Ta tambaya da karfi.

“Suna Bq a can na sauke su”

Sulaiman be ma gama rufe baki ba, Alhaji Habib ya saki hannun Hafsatu manga ya nufi BQ din, kamin ya isa har da hadawa da dan gudu, a balcony ya same su zaune maza uku daya daga cikinsu dattijo ne, suna ganinsa suka tashi tsaye domin kallon daya zaka masa kasan cewar shine mai gidan, tun daga yanayin shigarsa da kuma siffarsa wacce ke kara fito da ainahin zatinsa.

“Alhaji ina wuni”

Duk suka hada baki gurin gaisheshi shi kuma ya amsa cikin yanayin da ke nuna ya kagu ya ga matar da suka zo da ita.

“Lafiya kalau, ina matar yake?”

“Tana can daki”

Da sauri ya hau barandar ya shiga daya daga cikin dakunan da ya hango bude. Rufaida ce kwance kamar mai bachi sai dai shigowarsa yasa ta tashi zaune da sauri tana masa kallon tsoro. Idonsa ne ya cika da kwalla, sai ya fara takawa a hankali yana dosar inda take dakakkar shaddar dake jikinsa na amsa ko wane motsi nasa. Hannunsa ya daga ya nunata kamar zai fadi sunanta sai kuma ya kasa bakinsa sai rawa yake, hannu ta daga sama ta dora saman kai ta fasa ihu sai yai saurin komawa baya yana kallonta hawaye na zuba a idonsa. Hafsat ce ta shigo tare da Sulaiman Mai gadin gidan.

“Mama”

Hafsatu manga ta fada, ta nufi inda take da sauri, ita ma tana ganinta ta bar ihun ta ware hannayenta ta rumgume tana ta shafa irin abun nan na rashin hankali tana duba lafiyar yarta. Hafsatu manga kam rawa kawai take tana kara rumgumeta kamkam.

“Mama da baki nan aka kaini gurin yan sanda aka kama ni wai na kashe wata ni kuma ban kashe ta ba, mama kin san wannan Zat din ko to shine ya karbo ni daga gurinsa, shi yana da kirki yana dafa min indo, kuma ya fada min ke kika aiko wadannan mutane nan wai kina nan tafe ke ma, ashe da gaske ne ko? Kuma mama wai wacan Babana ne?”

Ta nuna Alhaji Habib da ke aikin zubar da hawaye har yanzu, ita dai Rufaida bata komai sai juye juye kai alamar bata cikin hayyacinta, daman can Hafsatu manga tasan ba magana take ba, idan har tai magana sai idan tana jin yunwa ko kuma zata kira Hafsatu manga shine kawai take bude baki tai magana.

“Mama su Inna Ladi sun mutu ko? Ko suna nan? Aa basa nan an kashe su ma, amman Mama ke ina kika tafi? Wani guri kika boye ko? Na sani ai”

Ta fada tana dariya. Alhaji Habib kam kallonsu kawai yake cike da tausayawa, matarsa ta fita daga haayyacinta ta koma kamar ba ita ba, har wata hurhurar wahala tai. Ya dade a haka sannan ya nufi inda take ita kuma ta fara masa ihu, sai Hafsatu manga ta tashi tsaye tana tareta.

“Aa karka zo mamata tsoron mutane take”
Chapter 78 · 0% Book details