← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 93

Sashe 62

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kanki zaki fallasawa sirri Hameeda ba ni ba, ba yarinyar da kika siyar tana hannuna ba? Ki saurari hukuncinki gurin Mai Martaba”

Yana fadar hakan ya kashe wayar. Sai tai saurin tashi tsaye. Mi yake nufi? Tona mata asiri zai yi? Lallai kuwa Mai Martaba zai fi yarda da shi fiye da ita. Safa da marya ta fara yi a cikin dakin, tana ta tunanin manufar maganarsa da kuma samawa kanta mafita.

Sai da yaje ya gaishe da Mai Martaba tare da Hafsatu manga, ya nunawa Mai Martaba ita sannan suka dora da zancen garin, a nan yake sanar da Mai Martaba akwai maganar da ya kamata su yi amman ba yanzu ba sai nan da kwana biyu idan ya natsu. Mai Martaba yayi farinciki da kyautar da Masarautar Damagaram tai ma dansa, yaji dadi sosai ko ba komai yasan sun karrama shi. Daga gurin Mai Martaba ya shiga gurin su Hajiya Hadiza da Hajiya Maryam da Hajiya Zarah ya nuna musu ita kuma ya gaishesu sannan ya fito.
A mota yai waya da Ibrahim ya fada masa komai da yadda abubuwan suka faru, har ma da zancen visa da zai nema musu zuwa kasar india, har da bashi Hafsatu manga suka yi magana sannan ya karbi wayar ya kashe, yana parking harabar gidan sakon Anty Ummi na shigowa wayarsa.

_Gobe ne birthday Farhat ya kamata ka yi surprise dinta_

Kashe motar yai ya bude ya fita sannan ya zagayo ya budewa Hafsatu manga, sai ta rike masa hannu gangan kamar ance za a kwaceta. Wata haddaiyar bakar mota ya gani mai tsada da direba ciki, an faka ta kusa da kofar falon Anty Ummi. Zai ta ya zagayo sannan ya shiga cikin falo, tufafin jiya ne na fulani a jikin Hafsatu manga, wannan dalilin ne yasa ya shi kara son zuwa da ita gurin Anty Ummi dan a duba mata kayan Amal kamin ya shiga gari anjima ya siyo mata.

Har suka shiga cikin falon Hafsatu manga na rike da hannunsa, a dayan bangare na falon ya nufa ya zauna ganin Anty Ummi da bako. Ganin hakan yasa Anty Ummi kiransa.

“Zain baka ga Ya Habib ba ne?”

Zain ya taso jin Anty Ummi ta ambaci Yaya sai ya karaso gurin ya zauna a dayar kujerar Hafsatu manga na rike da hannunsa.

“Ai ban sanshi ba”

“Yayana ne, wanda ke Kaduna be cika zuwa ba sai idan wani abun ya taso shiyasa baka sanshi ba, yanzu ma saboda rashin lafiyar Abbah ne da be samu damar zuwa ba a lokacin yana Dubai, shine yanzu ya zo”

“Allah sarki”

Zai ya fada tare da mika masa hannu suka gaisa, idon mutumen suna kan Hafsatu manga wani irin kallo yake mata kamar bana lafiya ba, ita kallonsa take tana kokarin tuna inda ta taba ganin fuskarsa, shine mutumen da takardunsa suka fadi ta dauko masa, yanzu ka tuna sai tai masa murmushi, a maimakon ya mayar mata da murmushi sai akwai yai fuskar tausayi da tashin hankali yai kiranta da kai, sai ta saki Zain ta tashi taje. Sai ya kama hannunta yana duba awarwaron dake hannunta yana duba awarwaron yai saurin kallonta yana mata wani irin rikonta daya firgitata.

“Ina kika samu wannan Awarwaron?”

Da karfi ta fisge jikinta ta juya da gudu ta koma gurin Zain kamar zata shige jikinsa.

“Wallahi nawa ne ba satowa nai ba, Mamana ta bani shi”

Ya mike tsaye da sauri zaije ya kamata hankalinsa ya tashi sosai.

“Ina mahaifiyarki take”

Zain ne ya tashi tsaye ya shiga tsakani yana tare mutumen.

“Dakata Malam”

Sai mutumen ya kalleshi kamar zai ce wani abu sai kuma ya koma ya zauna ya dafe kansa, sai ga hawaye sun sauko masa. Hafsatu manga ta kalli Zain kamar zata yi kuka.

“Zat tashi mu tafi ni bana son wannan gidan”

Haka Zain ya biye mata ya tashi tsaye rike da hannunta sai Anty Ummi ta dakatarda shi.....
[3/20, 3:05 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 44

Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un. Kawai yake maimatawa yana dafe da kansa.

“Ya Habib lafiya”

Anty Ummi ta sake tambaya a karo na biyu, sai ya dago kansa ya kalli Hafsatu manga, fuskar mahaifiyarta ce ya gani shimfide a fuskarta, ya maida dubansa gurin awarwaron hannun da take kokarin boyewa a zatonta za a ce tayi masa sata ne. Sai kuma ya kalli Zain.

“Waye mahaifin yarinyar nan?”

“Nine yata ce”

Zain ya fada kai tsaye.

“Ka tabbatar da yarka ce malam?”

Ya fada muryarsa na rawa alamar kuka na gab da kubuce masa daman tuni hawaye sun fara sauko masa.

“Ba yarsa ba ce Yaya tsintarta muka yi...”

Cewar Anty Ummi, Zain yayi kamar ya dakatar da ita amman bata tsaya ta saurareshi ba, sai da ta fayyacewa Ya Habib komai. Faduwa yai kasan gwuiyoyinsa yana hawaye kamar ba gobe, wasu na bin wasu ya kasa cewa komai. _Mahaifiyarta mahaukaciya ce_ abunda Anty Ummi ta fada masa yana ta masa yawo a cikin kai, ya kasa yarda ya gasgata cewar yarsa ce ba shi wani tabbaci akan hakan, sai dai kuma yana jin akasin haka wato na yarda cewar yarsa ce saboda abun hannun dake hannunta mai dauke da sunanta wanda yasa aka mata ita da mahaifiyar shekaru da dama da suka wuce, gashi kuma ance mahaifiyarta mahaukaciya ce zai iya yiyuwa mahaukaciyarce tunda ta bar gida ba tare da kowa ya sani ba. Kai ya sake dagawa ya kalli Hafsatu manga wacce ke buyo bayan Zain, fuskarta sak daya take da ta mahaifiyarta.

“Babu tantama wannan yata ce....!”

Ya fada cikin wani irin murya hawayen nata bin fuskarsa. Anty Ummi ta kalleshi ta kalli Hafsatu manga baki sake fuskarta dauke da tsantsar mamaki.

“Ya wannan yarinyar kauye ce daga kauye ta fito”

“Waye mahaifinta?”

Ya tambaya yana tada kai ya kalli Anty Ummi wacce tai yi maganar. Anty Ummi tayi shiru kamar mai tunanin abunda zata ce.

“Ni bani da Baba ban san babana ba, sai mamata kuma mahaukaciya ce, dan haka kai ba babana ba ne”

Hafsatu manga ta fada tana turo baki har lokacin tana bayan Zain rike da rigarsa gani take irin na baya za a mata wato Anty Ummi tana son bada ita ne kawai ga wani kamar yadda tai mata a baya. Murmushi mutumen yai yaja wani dogon numfashi ya aje.

“Ni ne mahaifinki, Indai Rufaida ce ta haifeki to nine Habib mahaifinki, ina siya miki wannan awarwaron tun baki zo duniya ba ke mahaifiyarki, uwarta ta bar gidana da cikinta ta shekara hudu da cikin bata haihu ba, kuma har yau bamu san inda take ba”

Ya karasa yana fashewa da kuka tare da nunawa Anty Ummi Hafsatu manga, jikin Anty Ummi ne ya soma yin sanyi tabbas ta tuna lokacin da aka ce Uwar gidansa tana da ciki bayan shafe shekaru bata haihu ba, ta kuma san lokacin da take dauke da cikin na tsawon shekaru, hawaye ne ya zubo mata, sai ta kalli Hafsatu manga tabbas fuskar Rufaida ce a fuskarta ba zata taba manta kamanin matar babban yayanta ba.

“Innalillahi Wa'inna Illahirraji'un”

Ta furta tana rufe baki. Zain ya tabe baki yana zuba hannayensa a aljihu.

“Ban yi tunanin idan na zo da ita zaki sake mata wani abun ba, shiyasa ban kawowa kaina komai akan tahowarta gidan nan ba, na san duka wannan tsarinki ne, ba anan zata zauna ba, dan haka ki rushe duk wani tsari da kika yi akanta”

Anty Ummi ta hawaye ta kalleshi cikin muryar kuka ta ce

“Ban shirya wannan ba Zain, ban san zaka zo da ita ba, Yaya ma be san da ita ba, kuma ba karamin mutun ba ne da za a ce an biyashi yai wannan abun, shin baka gani ne? Taya zai zubar da hawayensa akan karamar yarinya kamar wannan indai bashi da alaka da ita?”

“Nima ban sani ba, iyakar abunda na sani duk wanda yai unkurin cutarda Mama zan iya cutar da shi nima, bani da tabbaci gaskiyarki akanta saboda kin taba unkurin hallakata, so ni duk ban yarda da wannan plan din na ki ba, idan har ita ce miyasa baki taba labarin ba? Miyasa lokacin da kika ganta baki gane ba?”

“Saboda Mahaifiyarta ba nan take ba, ba kawowa raina cewar ita ce ba, saboda ban zata za ta iya zuwa har nan garin Gusau ba”

“Oh sai Yanzu daya ganta da rana tsaka ya ce yarsa ce sai kika tuno? Haka kawai mutum zai ga yarinya yace yarsa ce ni na yarda”

“Miye ribata idan yai maka karya?”

Mutumen ya tambaya cikin muryar kuka. Zain ya daga kafunsa.

“Ban sani ba”

Hannun Hafsatu manga ya rika wacce ta fara hawaye zasu fita daga cikin falon sai mutumen ya kirashi.

“Tsaya mana, fada min inda mahaifiyar yarinyar nan take ina son ganinta”

“Ban sani inda take ba, itama kuma bata san inda take ba, and wannan ba zai na baka yar mutane ba so wannan plan din be yi ba”

Ya karasa yana kallon Anty Ummi which means his last sentence is for her.

“Ko da anyi gwaji?”

“Wani abun kika taka idan munje gwajin ne?”

“Kana magana kamar ba da ni ba Zain, Wallahi har ga Allah ban tsara komai ba akan wannan abun ba, ban san komai akai ba”

“Idan ke baki tsara ba, maybe wani ya tsara someone like Hameeda Auwal ko kuma wani can daba mai wata manufar daban”

Mutumen ya share hawayen idonsa ya tashi tsaye.

“Zan nemo mahaifiyar yarinyar nan duk inda take, ko dan tabbatar da zargina, sannan ina hadaka da girma Allah ka bani damar gwajin DNA test dan tabbatar da hakan”

“Miyasa tun farko baka nemi mahaifiyar ba, sai yanzu da ka gannin da ita zaka ce wani yarka ce?”

“Ban san dalilin daya hana ni nemanta ba, tunda ta tafi babu wanda ya taba nemanta bamu sake neman ta, amman kullum da ita nake kwana na ke tashi tunaninta ne silar ciwona, amman yanzu zan nemeta koda hakan na nufin ajalina ne, dole na dawo da Raifaida indai tana duniyar nan”

Ya furta yana ware hannayensa hawaye na sauka a idonsa.

“Shekara nawa rabonka da ita?”
Chapter 62 · 0% Book details