← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 93

Sashe 8

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya nufi kofar fita daga falon da sauri har yana kokarin tuntube. Anty Ummi kam da kallon mamaki ta bishi da shi har ya fice. Cikin a hanzarce ya shiga motarsa yai mata key, horn biyu mai gadi ya bude masa gate ya hau titi da gudu. Cikin yan mintuna ya isa ZAINUDDEN SPECIAL HOSPITAL, yana aje motarsa ya nufi Emergency da sauri, Nurses dake Emergency din sai gaisheshi suke amman be amsa ba, dakunan ya soma bi daya bayan daya yana dubawa har ya kai karshe be ganta ba, layin yan hadari ya nufi ya soma duba gadajen dama dana hagu, sai daf da zai kai karshen dakin ya hangota kwance saman gadon an daura mata drip fuskarta da bandeji da kuma kafafunta.
Tsaye yai yana kallonta ya kasa karasawa inda take, tsigar jikinsa sai tashi take. Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya iya daga kafasar kamar marar lacca ya karasa kusa da gadonta, kallo daya yai ma fuskarta tausayinta ya kamashi yanayin yadda take numfashi kawai ya isa ya fahimtar da shi mawuyacin halin da take ciki.
Yasha ganin hadari kala kala ya sha yin tiyata ko ya duba marasa lafiyar da ido baya iya daukar ganin ciwon, amman be taba cin karo da wacce ta bashi tausayi sosai kamar Hafsat ba, duk wani shiga da fitar numfashinta aunashi yake da nasa, yana jina jin zafin ciwon dake jikinsa kamar a jikinsa yake. Hannu ya kai ya taba jikinta, sai yaji temperature dinta very high. File din dake saman drawer ya dauka yana dubawa, sai ga wasu nurses uku mata sun iso gurin gabansu sai faduwa yake, a zatonsu wani abun ne akai a kuskure ko kuma ba daidai ba, domin sun san halin Zain matukar suka saba wata doka ko suka yi wani abu ba daidai ba, zai iya korarsu.

“Waya dubata?”

Daya daga cikinsu mai sanye da karamin hijab half sunna ta amsa masa.

“Doctor Shukura, tace za a kara mata jini...”

“Ban tambayi ki”

“Sorry Sir”

Ta fada da sauri.

“Ina wadanda suka kawo ta?”

“Ba musan inda suke ba Sir, amman na fada musu a kawo jinin sai suka ce wai wanda ya kawota yaje gurin meeting ya dawo, su kuma ba yan'uwanta ba ne”

“A canja mata gado a kaita Mr Zain rooms”

“Yes Sir”

Yana fadar hakan ya juyo ya dawo gurin da nurses masu kula da gurin suke ya shiga can ciki ya dauko syringe tare da safar hannu da wata karamar robar dake daura drip, yana fitowa dakin nurses din na kawo gurin sun turota a gado. Tsayar da su hai ya saka safar ya daure dantsenta ya saka saka mata allura ya zuki jininta, Sannan ya cire sirinjin, Nurse din dake bayansa ta mika masa kada ta danne gurin sannan ya kwance robar da tsinin allurar ya jefar a kwandon shara.

Da sauri suka wuce da ita, shi kuma ya nufi gurin gwajin jinin, in few minute aka gwada jinin aka bashi result kasancewar shi ya zo da kansa, yayi mamakin ganin jinin ya zo daya da nasa, be wani bata lokaci ba. Gaje gurin dibar jini aka dibi nasa leda biyu. Sannan ya dawo office dinsa ya bude freezer ya dauki madara da maltina ya shanye, sannan ya sake fitowa ya kama Ward din dakin Mr Zain, dakunan da aka tana da saboda masu hannu da shuni, tun daga yanayin gurin ma ya isa ya fahimtar da mutum haka, dakuna ne masu yawa aka jera kowanne da numbersa.
Wayarsa ya fiddo daga aljihu ya nemo number Shukura, bugu biyu ta dauka.

“Tambaya min Farida wane daki ta kai yarinyar”

“Okay”

Bayan an seconds ta amsa masa da

“Mr Zain Room 37”

Kashe wayar yai ya kara gaban dakunan dake kusa dasu yana duba numbers din dakunan har ya isa 37, hannu ya kai ya murda kofar ta bude, daya daga cikin Nurses din da suka kawota tana tsaye a kanta tana duba file dinta. Tana ganin Zain tasha jinin jikinta.

“Zaki iya tafiya”

Cikin sauri ta fice daga dakin, sai ya karasa inda Hafsat mutsu mutsu amman idonta a rufe tana son yin kuka. Zaunawa yai gefen gadon yana kallon fuskarta, har a yanzu tausayinta yake ji duk kuwa da kasancewar yasan ba a hayyacinta take ba. Yanayinta sai ya masa kamar na Haleema lokacin da bata da lafiya, hannu ya kai zai shafa fegen fuskarta sai kuma ya gimke hannun ya sosa lips dinsa. Wayarsa ce tai ringing kamar daman jiran kiran yake sai yai saurin daga tare da karawa a kunne ba tare da ua duba mai kiran ba.

“Assalamu alaikum”

Jin muryar Hajiya Hadiza uwargidan Mai Martaba kuma uwa a garesu yasa shi natsuwa sosai, tare da amsa sallamar.

“Wa'alaikissalam Hajiya”

“Zain Mai Martaba yana son magana da kai, magana ce mai muhimmanci, sai dai ina son duk abunda zai fada maka ka kasance mai biyayya agareshi”

“Magana tana da nauyi ne sosai?”

“Idan ka zo zaka ji”

Daga haka ta kashe wayar, yasan idan har magana bata da muhimmanci ba zata kira tace yai ma Mai Martaba biyayyah ba, daman ta kanyi kokarin dorashi a hanya a duk lokacin da ta fahimci ana son hadashi da Mai Martaba ko Dada, domin ita kadaice take masa son gaskiya a cikin matan sarki.

_Ibrahim ka zo anjima kadan ka sakawa patient din dake Mr Zain ward room 37 ka saka mata jini, Mai Martaba yana nema yanzu_

Sakon daya aikawa abokinsa kenan na karta kwana, sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin, zuciyarsa cike da sake sake.

FARHAT POV.

Rayuwa tana zuwa ma ko wane bawa da abunda aka rubuta zai same shi ne, alkalamin kaddara baya barin kowa kuma baya manta kowa balle kuma har ya tsallake ka ya fada kan wani, iyakar abunda aka rubuta zai samu bawa a dole zai sameshi, ba mahana balle kuma matari.
Ranar yau ta zame ma Farhat bakar rana, domin ta zo mata da abubuwan daban daban wadanda suke dara a rayuwar ko wane bawa. A yau bakin labari ya sameta na yaudarar da Auwal yai mata mutumen data shirya bada ranta a gareshi, wanda ta sadaukar masa da soyayyarta ta mallaka masa komai nata, a yau ya rumtse ido ya zabi kasancewa da wata wace ba ita ba, ya zabi wata a matsayin abokiyar rayuwarsa ta har abada.
A yau Anty Rukaiya ta koreta mace data rike tamkar mahaifiyarta, macen da mijinta tsaya kai da fata wajen inganta rayuwarta, ya mayarda ita mutum ya bata ilmi ya wayar da ita, mace da take yi ma kallon uwa kuma uba a gurinta,
A yau tai tafiyar da take hangen kanta kamar a mafarki, taya zata yarda ita dai din ce ta hadu da masu satar mutane domin biyan kudin fansa? A yau ita ce a zaune cikin kasurgun daji da babu kowa a gaban da yamma sai itace da ciyayi, a yau taji abunda mutane da aka dauke aka rabasu da danginsu suke ji, a yau ta fuskancin wulakancin da ake yi ma mutanen da aka yi garkuwa da su, idan zasu je fitsar namiji ake sakawa ya rakasu da bindigarsa, a gabansa suke komai, a yau ta ga matan da barayi suke takawa su keta musu haddi, a inda suke zaune babu fitila kuma babu abun rufa balle matashin kai, a zaune wasu suke kwana wasu kuma su kwanta hannayensu da kafafunsu a daure kamar dabbobi, idan suka yi kuskure kadan sai su zanesu da bulala, a yau din dai da aka kawota an kashe mutane uku a gabanta mutane da ba a biya kudin karbarsu ba.

Da babura suka hauro da su cikin dajin bayan sun karbe komai masu, sai suka zabi wadanda suke ganin zasu iya samun wani dukiya a gurin iyayensu suka tafi dasu ciki har da Farhat, ranar yau ta zame ma Farhat bakar rana, daren kuma ya zame mata bakin dare.

“Keee... ”

Daya daga cikinsu ya tsaka mata tsawa, a firgice ta kalleshi, zuciyarta na mugun bugawa kamar zata fito fili.

*HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

8⃣

HAMEEDA POV.

Kamar kullum yau ma gaban window take tsaye tana kallon harabar gidan da kuma masu kai da kawo a harabar.
  A zahiri harabar gidan take kallo, amman a badini, hankalinta yana wani gurin ne daban, dalilin da ya sanya Zain ya juya mata baya take nema, irin rayuwar da suka yi a gidan take tunawa, ta yi marmarin irin kulawar da yake bata a baya, tana kaunar zaunawa da suke suna fira da juna.
  Amman komai da canja mata? Mutumen da a duniya yafi kowa tsanar ganin hawayenta a yau shine yake kwadaituwa da saka ta kuka, mutumen dake kokarin yaye mata damuwarta a yau shine damuwarta take sashi farinciki.
  Ta kasa yarda da komai, yau gobe burinta ya kasa ciki, ta kasa samun natsuwar aure kamar yadda ko wace mace take samun natsuwa a gidan mijinta, saboda ta hana kanta haihuwa, a yanzu kuma tada fito tana jiransa sai ya dauki kiyayya ya dora mata? Har gobe ganin take Anty Ummi ce ta shiga tsakaninta da shi, domin a da ba haka yake mata ba, gani take kamar itace ta saka ya auri Yayarta a maimakonta, bayan kuma ita tafi dacewa da shi, ta kasa yarda cewa Zain baya sonta.
  Juyowa tai tana fuskarta cikin dakinta, but still jikinta na jingine da ginin gurin, a hankali ta sauke numfashi.

“Wannan ce kadai damar da nake da ita a rayuwata, itace kawai hanyar da zan iya gusar da kiyayyata a zuciyar Zain, ina son mu koma kamar baya, ina kwadayin ka zama abokin rayuwata na har a bada Zain”

Ta furta a hankali sannan ta tako cike da kasaita ta karaso gaban kujerarta dake gefen godonta, har zata zauna sai kuma tai tsaye tana ta tunani.
  Yadda zata gyara alakarta da Zain take tunani, a ganinta har gobe Zain yana kaunarta kawai dai an shiga tsakaninsu ne.
   Kwankwasa kofar dakin akai, hakan yasa ta dago kai ta kalli kofar, bayan wasu yan seconds Abida ta turo kofar dakin ta shigo bakinta kumshe da sallama, kanta a kasa karasawa tai gaban Hameeda ta risina.

“Allah ya taimakeki Mai Martaba yana nemanki”

Kallon rashin fahimta da mamaki tai mata.
Chapter 8 · 0% Book details