Sashe 36
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A karkashin wani ice suka aje ta, a gurin ta zauna tana ta rusa kuka, duk wanda ya wuce sai ya tsaya ya mata magana amman bata iya cewa komai sai kuka take, a haka har Allah ya kawo wani dattijo, babu kalar tambayar da be mata ba, amman ta kasa ce masa komai sai kuka take shi ya rika hannunta ya tafi da ita gidansa, Matarsa Inna Ladi mace ce mai son mutane da kuma maraba da su, Inna ladi baiwa ce a gidan masarautar Kufawa hakan ya samo alsali ne tun daga kakarta kasancewa a wacan zamanin ana yayin sayen bayi masarautar kauyen Kufawa ta siyenta ita da kakanta, a haka aka haife iyayensu, har aka zo kansu kasancewar zamani a canja sai ya zama suna gidanjensu sai dai dukan wani aiki na gidan sarkin su suke yi su da duk bayin da aka siye tare kuma da yayansu, har yau har gobe idan Sarkin yaga dama zai iya daukar daya daga cikinsu ko yayasu ya bayar kyauta, sai dai walahar irin ta da da bauta d ake sha ya banbanta da na yanzu, daga gidanta take zuwa yin aiki a gidan Sarkin idan ta gama ta dawo tayi nata aikin, idan kuma bata samu zuwa ba sai ta tura yayanta.
Ita kanta Inna Ladi tana kallon Rufaida ta san daga birni take kuma ba lafiya take ba.
“Malam ina ka samo wannan matar?”
A take ya labarta mata komai, ta tausaya mata domin ta san duk yadda aka yi wannan sihiri ne ga kuma tsohon cikin da take dauke da shi. A gidan Rufaida ta cigaba da zama wani lokacin ta kan fita ta tafi yawonta sai da yamma ta dawo wani lokacin kuma sai ta zauna a gidan tai ta kuka, a haka ta kwashe shekara daya bata haihu ba, daga nan Malam Sani bawa da Inna Ladi suka dingi yi mata addu'a da rubutu tana sha, wasa wasa ta kara kwashe shekara uku sannan ta haihuwa, ranar da tai nakudu babu inda ba a jita ba, saboda kuka da ihun da take, wani abun mamaki tana haihuwar yarinyar sai ta karbeta daga hannun Inna Ladi tana kallonta jikinta har rawa yake.
“Hafsa Hafsa hafsa”
Shine kawai abunda take ta fada, wannan dalilin yasa suka sakawa yar da haifa Hafsat amman Inna Ladi tana kiranta da manga kasancewar sunan mahaifiyarta ne.
A hnnunsu Hafsatu manga ta girma duk wani abu da uwa take yi ma ya, Inna Ladi ce take yi ma Hafsatu manga, a haka har tai yi wayo.
Ta bangaren Habib babu irin neman da basu mata ba, su da yan'uwanta amman basu sameta ba, wannan damuwar ce ta zame masa silar ciwon zuciyar da yake tasar masa lokaci zuwa lokaci. A duk lokacin daya tuna da Rufaida sai yaji kamar ya hade zuciya ya mutu dan bakinciki, a haka har aka kwashe shekara tara zuwa goma a lokacin twins din Safiya suna da shekara 28, tun gama karatun lauyan da suke ko wacce ta kama aiki sun zama manyan lauyoyi har ta aurar da su. Hafsatu manga kuma na da shekara tara zuwa goma.
*** *** ***
Suna rayuwarsu cikin jindadi da walwala, wata rana kwatsan barayin shano suka kawo musu hari daman sun dade suna aiko sakon cewar zasu kawo musu hari, sun kashe mutane da yawa garin kadan ne suka samu tsira wadanda suka kai gudu da kafa har suka kai wani garin, sai bayan an kashe rabin garin aka aiko musu da sojoji, a nan wasu suka samu tsayawa a makarantar bokon dake garin, aka kawo musu taimako gaggawa.
Share your opinions.
[3/4, 3:37 PM] Mrs Zainab Jega: *HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_
Wattpad @KhadeejaCandy
2⃣6⃣
Cikin rashin jindadi Anty Ummi ta dawo gidan mahaifinta bayan tasa an tafi da Hafsatu manga, jikinta ya soma bata babu dadi zuciyarta na raya kamar wani abun zai faru, and Zain ba zaijidadi ba, yes ta san ba zai ji dadi ba amman bata da wata mafita bayan wannan.
A gidan ta wuni, tana ta jiran kiran daga mutumen amman shiru be kirata ba, hakan yasa trying numbersa sai taji ta kashe, sai da yamma ta koma gida, bayan taga jikin Abbansu da sauki sosai, sai dai har ta bar gidan mutumen be kirata ba, da tunani kala kala ta isa gida.
Bata yi mamakin ganin Zain a falonta zaune ba, sai dai fargaba da tsoro sun cika mata zuciya na yadda zata tunkareshi da maganar. Da murmushi ta kalleshi
“Ka kai yaushe kana jirana a nan?”
Ya kalli agogon hannunsa.
“Four hours, ina Mama”
Ya tambaya yana kallon kofa dan har yanzu be ga ta shigo ba, sai tai kamar bata ji shi ba, ta rumgume yayanta dake mata oyoyo.
“Anty tun dazu Uncle ke jiranki”
Aliyu ya fada, sai tai murmushin yake.
“Na gani ai...”
“Anty ina mama?”
Hankalinsa ya fara tashi daman tun dazu jikinsa ke bashi ba dadi.
“Kids kuje ciki zamuyi magana”
Bayan sun wace ta zauna a kujerar dake kusa da ta Zain.
“Gida naje guba Abbah, ciwonsa ya tashi”
Kallonta kawai yake be ce komai ba, be kuma nuna damuwa akan abunda ta fada ba, he care for her family amman a yanzu ba shi yake son ji ba, so he wouldn't talk har sai ta kai gabar da yake so.
“Daga nan na bada ita ga wanda zai kaita gida...”
Ta fada tana murza yatsun hannunta, nan ma be ce komai ba sai kallon yatsun hannunta yake, yana reading mind dinta.
“Da safe ne, tun da mutum ya tafi be kirani ba and na kirashi wayarsa kashe... Amman na san idan ya isa zai kirani”
Still shiru be ce komai ba.
“Zain ban yi hakan dan musgunawa daya daga cikinku ba, nayi hakan ne dan samawa kowa mafita, abunda kake yi kamar kana son Mama ne, which is wrong, and she's too young for that ni kuma ina tsoron abunda zai faru...”
Wani dukan hannun kujera yai wani irin fushi ya bayyana a fuskarsa.
“Saboda kina iya controlling dina ba shi ke nuna kina iya controlling din wasu ba, ba ki da ikon zabawa Mama abunda ya dace da ita saboda ke ba uwarta ba ce, kuma ba kowan kowa ba ce a rayuwarta, ilminki be amfaneki ba tunda baki san ciwon kowa ba sai na ki, saboda tana nan gidan ne ya baki damar yanke mata wannan hukuncin ko? Ba zaki taba iya yanke alakar dake tsakanina da ita ba, and for your words abun kunya ne ace baki iya shaidun kanenki da alheri ba, baki yi karya ba ina son Hafsat sai dai ba irin son ta zuciyarki ke ayyana miki ba, har gobe ba zaki taba son abunda zai faranta min ba Anty Ummi, saboda baki taba zama uwata ba....!”
Yana kaiwa nan ya tashi fuuu ya fice daga falon cikin wani irin bacin rai. Maganarsa ta daketa har kasan zuciyarta a take hawaye ya cika mata ido, sai tai saurin tashi ta daga kanta sama tana sauke numfashi.
HAMEEDA POV.
Safa da marwa kawai take acikin daki ita kadai, tana jinjina karfin hali da makirci irin na Farhat.
“Wai har ni yarinyar nan zata daurawa sarka ta siyar a gaban Mai Martaba, lallai Zain ya auro yar bariki kuma tantiyar shedaniya, amman zan koya mata darasi zan bude mata sabon babin da bata taba karatu ba, tana ji tana gani zaman gidan nan zai gagareta, tunda na iya kawarda yar'uwata Wallahi kowa zan iya kawarwa saboda bukatata...!”
Ta fada tana wani kashe ido, sai kuma ta karasa inda wayarta take ta dauka ta kira Abida, in few minutes Abida ta shigo dakin jikinta na rawa.
“Allah ya taimakeki na amsa kiranki”
Hameeda ta nufi jakarta ta dauka wani abu ta mikawa Abida.
“Jeki dakin Farhat ki saka mata wannan abun a karkashin katifarta”
Abida ta tsaya kallon abun cikin damuwa kamar ba zata karba ba.
“Karbi na ce, kuma ki tabbatar kinyi yadda na ce miki, sauran ki bari wani ya ganki”
“To ranki ya dade”
Ta karba ta tashi ta fice da sauri, kai tsaye Part din Farhat ta nufa tana ta tunanin abunda zata ce mata ta yadda zata barta ta shiga har cikin dakinta. A hankali tai knocked kofar falonta gabata sai faduwa yake, bata isa tacewa Hameeda ba zata yi ba, haka kuma bata isa tayi mata kuskure ba domin tasan abun kanta zai dawo. Tana tsaye a gurin har Farhat ta bude kofar sai ta tsaya tana kallonta ita kuma tai kasa da idonta tare da risinawa ta gaisheta.
“Allah ya taimakeki na ce ko kina bukatar wani aikin ne?”
“Bana bukata”
Taje zata maida kofar falon ta rufe Abida ta sake cewa.
“Gyaran falo da daki fa nasan ba a gyara ba, saboda naji Hajiya Maryam tana cewa ba za a baki kuyangi ba gudun abunda zaije ya dawo, duk abunda kike so zaki fada min sai nai miki”
“Idan akwai abunda ya zama dole na sanar miki zan sanar miki, amman gyaran gina ni zan yi abuna”
Tana gama fadar hakan ta rufe kofar. A dole Abida ta tashi ta bar kofar falon ta dawo dakin Hameeda.
“Ban samu sakawa ba, bata bar ni na shiga falon ba ma”
“Saboda me?”
“Tace bata bukatar komai ita zata yi da kanta”
Hameeda ta mika mata hannu ita kuma ta danka mata abun a hannunsa, bata jira komai ba ta dauki mayafinta ta rufe kanta ta fice daga dakin, kai tsaye ta nufi part din Zain. A bakin kofa ta tsaya ta sauke ajiyar zuciya ta daidaita fuskarta ta yadda zata nuna babu abunda ke damunta, ta dade a tsaye tana knocked sannan Farhat ta bude kofar.
“Lallai Antina, ke ba yar sarauta ba amman kin barni a tsaye ina ta knocked kamar wata baiwa”
Hameeda ta fada tana murmushi, Farhat ta bar jikin kofar dan ta bawa Hameeda damar karasowa cikin falon.
“A gurina darajarki tazara kadan ta bawa bayi, domin a yanzu ina sama da ke, ke da bayin dukanku a kasana kuke, so ko ba a kirani yar Sarki ba, za a kirani sarakuwar sarki domin dansa nake aure, kuma kin san ance matar Yarima ita ma gimbiya ce”