← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 93

Sashe 9

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kin san dalilin kiran?”

“Ban san komai akai ba ya shugabata”

Yawun bakinta ta hade, ta soma takawa a hankali har ta isa gaban wardrobe dinta ta bude ta dauko mayafi ya rufe kanta sannan ta nufi kofar fita, zuciyarta na zillon rigan kafafunta. A iya saninta Mai Martaba baya fada a yanzu, kuma idan har wani hukunci zai yanke ko wata magana data shafi iyalinsa a falonsa na cikin gida yake zartarda komai. Kai tsaye part dinsa ta nufa tana kai hannu ta bude kofar falon farko sai gabanta ya soma faduwa.

“Assalamu Alaikum”

Tayi sallamar ne tana kokarin danne zuciyarta, yan matan Mai Martaba ne suka amsa mata, wato Sisters din Zain, cikin falon ta tana karewa duk wanda yakr cikin falon kallo kasa kasa, Hajiya Hadiza ce a kujerar dake kusa da ta Mai Martaba, sai Hajiya Maryam na binta, da Hajiya Zarah dukansu Matan Mai Martaba ne, Dada  Yalwa na zaune a kujerar data saba zama a duk lokacin da irin hakan ya samu.
  Tun da ta zauna bata sake dago kai ta kalli kowa ba, wannan dabi'ar na daya daga cikin dabi'un da Mai Martaba yake so, yana cikin dabi'un da ake yabon Hameeda da su har ake ganin tafi duka yaran sarkin kunya.
  Gyara muryar Mai Martaba yai, wannan yasa hankalin kowa ya koma kansa kenan, ciki har da Zain da zuciyarsa take can asibiti.

“Zain...”

Mai Martaba ya kira sunansa, a natse ya dago ya kalli Mai Martaba.

“Mi Hameeda tai maka?”

Kallon Hameeda yai yaga kanta kasa, sai ya kalli Dada Yalwa kamin ya maida dubansa gurin Mai Martaba.

“Allah ya taimaki Mai Martaba, bata min komai ba”

Dada Yalwa ta tari numfashinsa.

“Bata maka komai ba, zaka ce ta daina shiga sasshen ka? Ta daina bi inda zata ganka? Kace ka tsaneta? Ba wannan dalilin yasa tace zata bar gidan ba, saboda kana nuna mata banbance da sauran kannenka, kuma ba kowa ba ne sai wannan Ummi ita take zigashi a komai, har cewa yai ba zai kara kaunar Hameeda ba a rayuwarsa”

Tunda ta fara maganar babu wanda ya saka mata baki sai da ta kai aya, babu wanda ya isa ya karyatata ko da kuwa karya take fadi babu kuma wanda ya isa ya fada ta fada, shi kansa Mai Martaba natsuwa yai yana sauraren Mahaifiyarsa. Bayan wasu yan dakiku ya sake gyaran murya a karo na biyu ya ce

“Zain Hameeda da Ikram duka kanenka ne, a gurina duka daya kuke, Hameeda tsatson mu ce wannan kadai ya isa yasa ka girmamata, zan iya wakiltarta a komai na tsaya mata, kai ban tsaya maka ba, kai da ita duk a daki daya kuka taso wannan kadai ia isa ya yansa ka ganin kimarta, tafi kowa cancantar girmamawa a gurinka, kai ne Babba Zain be kamata ace wasu dabi'un marasa kyau suna tasowa daga gareka ba.
  Komai na rayuwar duniya dan hakuri ne, idan har tai maka laifine sai ka sameta ku tattaunawa, idan kuma abun ya gagara sai ka samu Hajiya ko daya daga cikin uwayenka sai ka fada musu komai”

Yayi shiru na wani lokacin, sannan ya cigaba.

“Ko kadan bana son naji wata rigima ko rashin jituwa na tasowa tsakanin iyalaina, zuciyata tana sosuwa idan daya daga cikinku ya aikata wani abu marar dadi, idan laifi tai maka ka yafe mata kuma ku shirya tsakaninku bana son jin wani abu ya shiga tsakaninku daga yau”

Tsit falon yai kamar ba kowa, zuwa can Hameeda ta dago fuskarta da hawaye shabe shabe.

“Ka gafarce ni Mai Martaba, da nasan idan na fadawa Dada abunda Zain ya fada min zai zata fada maka ne da ban fada ba, Allah shine shaidata bana son abunda zai daga maka hankali a yanzu kuma na maka alkawari ba zaka sake jin wata yasassshiyar magana a tsakaninmu ba”

Ta juyo ta kalli Zain da sai a lokacin ta lura da inda yake zaune.

“Ka gafarta min Yarima, idan akwai abunda nai maka cikin rashin sani ko da gangace, ka taimaki ne ka rika fada min abunda nake maka da yake bata maka tai zan kiyaye, kuma na maka alkawari zan kasance mai biyaya a gareka har a bada”

Ta karasa tana hade hannayenta hawaye na mata zuba kamar gaske. Kallonta Mai Martaba yai zuciyarsa cike da kaunarta, tarbiyarta da tsantsan da kanta da biyayarta suna burgeshi, tafi kowa gudun zuciyarsa a Masarautar. Zain kam be yi mamaki ba daman yasan yadda take narkewa a duk lokacin da irin hakan ta samu, ko a tsakaninta da Haleema ne sai Mai Martaba ya dora laifin akan Haleema ya ba Hameeda gaskiya.

“Wata matsala ba zata sake tasowa daga gareni ba Insha-Allah”

Ya fada yana maida kallonsa gurin Hajiya Hadiza dake gyada masa kai. Mai Martaba ya daga kai yana kallon sauran yan matan.

“Na taraku ne gaba daya, saboda kar bayan wannan kuma wata maganar ta sake tasowa, kar abunda ya faru tsakanin Zain da Hameeda yasa ku rainata ko kui mata wani kallo dabe dace ba”

“Insha-Allah zamu kasance masu biyayyah a gareka, kuma babu wani banbance da muke nunawa dukanmu, kanmu hade yake kuma za mu cigaba da kasancewa haka insha-Allah”

Cewar Ikram on behalf of them, kasancewar ita ce Babba a cikin yan matan da suke cikin gidan a yanzu. Da hannu yai musu alama sai duk suka tashi tsaye ban da Matansa, bayan sisters dinsa sun fice Zain ya tashi tsaye da zimmar fice daga falon, sai kuma ya koma ya zauna sakamakon kallon da Mai yai masa.
Natsuwa yai sosai dan yasan akwai sauran magana. A natse Hajiya Maryam ta fara magana, cike da isa daman haka take masa a gaban a duk lokacin da zatai masa magana.

“Abu na biyu da yasa muka kiraka Zain zancen aurenka ne, wasa wasa muka kusan shiga shekara ta hudu da rasuwar Haleema amman shiru baka sake maganar aure ba”

Ya dan dago kadan ya kalleta ya maida kansa.

“Har yanzu ban samu wacce nake so ba ne shiyasa”

“Har yaushe zaka ga wacce kake so, ai kin san halin Zain ko ta farko ai sai da aka matsa masa sannan yai, ni abunda na ga yafi dacewa kawai a hada shi da Hameeda”

Da sauri ya Zain ya dago ya kalli Hajiya Zara wacce itace take maganar a yanzu.

‘Hameeda..?’

Ya maimaita a ransa, sai kuma ya kalli Hajiya Hadiza kai ta gyarda masa a hankali ta yadda shi kadai zai iya fahimtar abunda take nufi. Sai ya maida kansa kasa zuciyarsa na mugun bugawa da karfi.
Hajiya Hadiza ta gyara zamanta tana magana a sanyaye.

“Ba haka ya kamata kui masa ba idan har aure kuke son yai sai ku bashi damar nemo matar da yake so, idan har be samo ba zaku iya bashi duk wacce kuke ganin ta dace da shi, ita kanta Hameeda baku sani ba ko tana da wanda take so”

“Yaushe zai zabo wacce yake so din, kun fi kowa sanin Zain, kuma tabbas yana son Hameeda ita kuma tana son shi ni na sani, Hameeda ita tafi kowa dacewa da ta maye gurbin Haleema”

Wannan karon Dada Yalwa ce take maganar cike da bacin rai.

“Da gangan nasa aka cire hotunan Haleema dan nasan idan ba haka akai masa ba, ba gyaruwa zai yi ba, kuma shi a halin yanzu ai be san wacce yake so ba, mace da matarsa ta mutu ba kamar sabon haihuwa ne komai sai an masa”

Hajiya Hadiza ta ce

“Kuma Hameeda tafi kowa dacewa da shi, saboda halin hakuri da Allah yai mata, da kuma kawaice zata iya jure duk wani abun da zai mata ta zauna da shi lafiya kalau, tunda suna son junansu”

Shi dai be ce komai ba duk da zuciyarsa na cike da abubuwa, yasan ba son gaskiya suke masa kamar Hajiya Hadiza ba, su kullum a cikin neman laifinsa suke, dukan abunda zai kawo rashin jutuwa tsakanisa da Mai Martaba faranta musu rai yake.

“Shi fa namiji ba a masa auren dole auren dole ma kuma na daya ba na biyu ba, haba abun ai ya zama wani kala, yanzu an daina wannan abun, mai zai hana Mai Martaba ya bashi damar da lokaci na zaben wacce yake so idan har be samo ba sai a yanke masa duk hukunci da ake so”

Dada Yalwa ta tsire baki tana kallon Hajiya Hadiza cike da tsanar dan ita a ganinta bata son Zain ne kuma tana mata katsalandan a abunda ya shafi Zain, bayan kuma ita tana ganin tafi kowa dacewa da ta yanke masa duk hukunci da take ganin ya dace da shi domin tafi kowa son farincikisa.

“Ke dai Allah be rabaki da shisshigi akan maganar Zain ya ba, ana ga gabas kina yamma sai kace baki san halin Zain ba, wani irin a bashi lokaci, shekara uku be ga wacce yake so ba sai cikin kankanen lokaci”

Ta karasa da jan tsaki. Mai Martaba ya gyara zamansa bayan ya gama sauraren abunda yake fita daga bakinsu, ya san halin matansa ya kuma san irin zaman da ko waccensu take yi da Zain, hakan yasa a duk lokacin da zai yanke hukunci abunda ya shafi gidansa ko kuma Zain ya kan saurari abunda zai fito faga garesu.

“Zain kana da wace kake so ko ta kwanta maka?”

Kamar daga sama Zain yaji tambayar Mai Martaba, sai ya rasa ta inda zai amsa masa, kar yace babu suce zasu hada shi da Hameeda idan kuma ya ce akwai wa zai gabatar?

“Mai Martaba a yanzu kam babu wacce nake so sai dai a bani damar zan nemo ko da a nan gidan ne”

Maganarsa tai Mai Martaba dadi, daman baya son yanke masa hukuncin abunda baya so, haka ma Hajiya Hadiza, Hajiya Maryam da Dada Yalwa kam sun dauka Hameeda yake nufi ko kuma sauran yan matan da ake riko a gidan jin ya sako maganar gida a ciki.

“Zaka iya tafiya Zain, Allah yai zaba maka abunda yafi zama alheri a rayuwarka”

Cewar Mai Martaba yana kallonsa.

“A tashi lafiya, Allah ya kara maka lafiya”
Chapter 9 · 0% Book details