← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 93

Sashe 25

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wato kunje kai da wacan bakar yar'uwar taka kun gada kai ko?”

“Ba wani hadin kai Dada kema kin san idan bana son abu babu wanda ya isa ya saka nai yi, ni naga yarinya nanu ina sonta shiyasa kuma nayi tunanin zaki goya min baya shiyasa na gabatar da ita a gareki”

Yana kaiwa nan ya tashi ya fice daga falon yana mai nuna bacin ransa a fili. Hameeda ta kalli Dada ta ce

“Miyasa ba zaki amince masa ba Dada?”

“Saboda ke nake son ya aura ba wata ba”

“Ba zan taba yafewa kaina ba Dada matukar baki bar Zain ya auri matar da yake so ba, bana son Zain a yanzu Dada, son da nake masa na yan'uwanta ne kawai, amman ba zan iya zama da mijin yayata ba, Saif nake so kuma na gabatar miki da shi dan me zaki mana dole? Dada idan Zain be auri yarinyar nan ba kika san halin da zai shiga? Ke da kanki kike kewa ke uwarmu ce a gidan nan miyasa ba zaki mana abunda zai faranta mana rai ba”

Ya karasa hawaye na sauko mata. Sai kuma ta tashi ta karasa gaban Dada ta kama hannunta ta rike.

“Indai har dan ni neni dan Allah ki barshi ya auri wacce yake so, in yaso bayan aure sai ki gabatar masa da ni nasan ko dan kunyar ba zai iya musa miki ba, amman idan kika hana shi yanzu ba zai taba amincewa ya aureni ba, ganin wata yace yana sonta ma ai nasara shi yake nuna cewar ya fara zama mutum kenan dan Allah Dada ki amince dan Allah”

“Idan har zan amince to sai dai ya hadaku ku biyu ya aureku...”

“Aa Dada ki Kyaleshi ya aureta, in yaso daga baya sai ki gabatar masa da ni, idan kika masa haka yanzu zai iya kin amincewa nima ba zan ji dadin zama da shi ba a yanzu”

Dada ta dauke kai ba dan ta gamsu ba.

*** *** ***

Daki daya suka kwana da Hafsat, da asuba Hafsat ta tasheta tai sallah sannan ta sake komawa bachi, bata tashi ba sai misalin goma na safe. Ta dade tana murza idonta kamin ta budesu kwarar biscuit daya ta gani an aje kusa da ita sai ta kai hannu ta dauka, a nan ta hango wani kasa tana kara dubawa sai ta hango an jera shi har kofar falo. Sauka tai saman gadon ta rika tsintar biscuits din da daidai har zuwa gurin kofa, hannu yasa ta kara bude kofar ta fito tana ta tsinta har ta kawo falo sam lura da kowa dake falonba har sai ta taji anyi gyara murya, sai tai saurin tashi tsaye zata waiga taga wanene sai kawai taji an dagata sama ana mata cakulkuli. Dariya take sosai har da kyalkyatawa kamar ba ita ba, da sauri Doc Hafsat ta fito daga Kitchen sanye da kayan bachi hannunta rike da knife tana kallonsu.

“Ikon Allah yau Mama kece kike kyakyatawa haka”

Auwal ya zaunar da ita saman kujera yana dariya.

“Bata dariya ne?”

“Tana yi amman bata kyakyatawa”

Yayi murmushi yana kallonta cike da sha'awa, har yanzu bata daina dariyar ba sai dai ta daina kyakyatawa, sai da ta gaji da dariyar sannan ta kalli Doc Hafsat ta hade hannayenta tana gaisheta. Auwal ya mika hannun ya riko hannunta yana kallon munduwar dake hannunta.

“Wai ya bincika iyayenta kuwa?”

“Bana tunanin yayi hakan, kuma iyayenta a kauye suke kauyen kuma an kori kowa in ba yanxu su ka koma ba”

“Ce miki yai daga kauye take? Look at this”

Doc Hafsat ta rika hannunta tana dubawa.

“I tot shi ya siya mata kamar zinari ko?”

“Azurfa dai sinari ake mai suna sai a manyan birane, amman wannan azurfa ce mai tsada, baby shi ya siya miki?”

Ya karasa yana tambayar Hafsatu manga, sai ta girgiza kai alamar a a.

“Babanki ya baki ko Mama?”

Ta gyada kai. Sai ya kalli Doc Hafsat ya ce

“I don't think ya fada miki gaskiya akan yarinyar nan, idan har da gaske yar gudun hijirace miyasa be kaita sansanin yan gudun hijira ba, ko kuma ya kai ta gidansu, ai fadar sarki mai maraba da baki ce ko yaushe, actually yarinyar nan batai kama da yan kauye ba Hafsat, dubi abun hannun na nata duk iyayen da suka sakawa karamar yarinya kamar wannan azurfa mai tsada kuma mai sunanta ya nuna iyayen masu kudi ne, kuma ba yan kauye ba, abu na biyu kyawon yarinyar nan ya wuce ace daga kauye Kufawa take dube ta da kyau ki gani ba tai kama da hausawa ba...”

Doc Hafsat ta kalleshi ta kalli Hafsatu manga.

“Me kake nufi?”

“I think satota yai”

Ba shiri Hafsat ta saki baki sai kuma tai saurin rufewa tana girgirza kai.

“No no Astagafurrullah, Doc Zain ba zai yi haka ba”

“Ko...? Let's see...”

Yasa hannayensa biyu ya rika kunnuwanta, yana kokarin tashi tsaye daga zaunen da yake a hannun cushion.

“Cute baby, bye bye”

Dariya tai amman ba mai sauti tana runtse ido.

“Idan Momy ta fito ki ce mata naje kai Zainab airport”

Kasa amsawa tai har ya wuce dan mamaki ya hana ta tace komai wani bangare na zuciyarta na son ya yarda wani bangaren kuma tana ganin kamar Zain ba zai iya haka ba, wayarta ce tai ringing, sai ta aje wukar saman center table ta nufi dakinta. Zain ne ya kirata ba karamin faduwa gabanta yai ba kamin ta dauka.

“Hello ina kwana?”

“Lafiya. Gani nan ganin Mama, ki sanarda iyayenki”

“Okay sai ka iso”

Tana aje wayar ta kwalama Hafsatu manga kira.

*** ***** ****

Sai ya shiga ya gaishe da Mai Martaba sannan ya fito daga cikin gidan gaba daya, a gaban wani katafaren Mall ya tsaya ya shiga ya zaba mata kala takwas masu kyau, dan be jin zata kai kwana takwas ma a gidan, sai kuma talkama, tsayawa yai yana kallon wasu talkami masu kyau dauka yai ya hada da wadanda cikin wani irin nishadi, har ga Allah yana jin son Hafsatu manga sosai yake jinta kamar yar da ya haifa, Allah ya sa masa son yara balle ita da take da shiga rai, and gata da sunan mahaifiyarsa sunan daya fi so fiye da ko wanne a duniya, yana da burin sakawa yarsa sunan idan Allah ya bashi, finally Hafsatu manga has it be ga dalili daya da zai hanata shiga ransa ba.

Sai da ya biya kudin sannan ya koma dayan bangaren ya siya mata chocolate da wano sweet Candy mai dadi.
A a mazaunin baya aka zuba masa kayansa sannan ya fito da wayarsa ya kira Doc Hafsat ya sanar mata da zuwansa sannan ya kama hanyar gidansu dake Millions quarters.
Sai dai yai horn mai gadin ya bude masa sannan ya kunna kai harabar gidan, wayarsa ya sake daukowa ya aikawa Hafsat da sakon isowarsa, ko minti biyu ba ayi ba sai ga Hafsatu manga ta fito daga cikin gidan da gudu ta doso inda motarsa take fake, an gyara mata kai an saka mata ribbon tufafin jiya ne a jikinta amman tayi kyau sosai sakamakon kwalliyar da aka mata. Bude mata yai ta shiga front seat ta zauna sannan ya mika hannunsa ya rika hannunta yana murmushi.

“Mama ya akayi?”

Ta ware hannayenta alamar bata sani ba, tana murmushin daya fitarda dimples dinta.

“An miki fada a nan ko an dakeki ko tsawa?”

Ta girgirza.

“Kina jindadin zama nan?”

Ta gyada kai.

“Good”

Ya mika hannunsa a seat din baya ya dauko ledar dake da chocolate ya bude daya ya mika mata, cike da murna ta karba jikinta har rawa yake ta kai a bakinta.

“Akwai dadi?”

Ta daga masa kai, sai ta gutsiri wanda ke cikin bakinta ta mika masa, a maimakon ya karba sai ya mika mata bakinsa ta saka masa, kamar ba shi Zain din dake kyamar cin abun hannun mutane ba, balle kuma na baki da yake da tabbacin idan ya ci sai ya yi hararwa.
Isowar Doc Hafsat ne yasa shi zuke gilashin motarsa ya gaisa da ita.

“Ga tufafi nan a shigar mata da su, and duk abunda take bukata ki fada min, tayi kuka?”

“Aa wani abun mamaki ma, yau tayi dariya har da kyalkyatawa lokacin da Auwal yake mata wasa”

Ya danyi jimmm kamin ya ce

“Wane Auwal?”

“Yayana ne”

“A nan gidan yake?”

“Ee amman ba nan yake aure ba”

A hankali ya sauke numfashi yana kallon Hafsatu manga, haka kawai sai yaji babu dadi, duk kuwa da kasancewar yana son farincikinta amman ya samu kansa da rashin jindadin hakan.

“Ku shiga ciki akwai inda zamu je yanzu”

Ya fada yanayinsa na canja. Fita Hafsatu manga tai rike da ledar tana masa bye bye, Doc kuma ta bude gidan baya ta dauki dayar ledar.
Sai da suka shige cikin gidan sannan ya kunna motarsa ya fice, duk jin yai kamar bashi da lafiya damuwa ta rufewa wacce be san daga ina takeba. Kamin ya isa gidan su Anty Ummi ya dauki wayarsa ya kira Ibrahim, yana labarta masa abunda ya faru tsakaninsa da Dada da kuma Hameeda.

“Amman ina tunanin akwai abunda Hameeda take hange”

“She change fiye da tunaninka, yanzu ba ta nawa take ba, damuwa ya mata yawa ma, har shaye-shaye take”

“Do you really think duk wannan gaskiya ne, baka tunanin plan ne?”

“I don't think so, Hameeda ta bani gudumawa Ibrahim, tana bukatar taimako na a yanzu be kamata na kyaleta cikin wannan halin ba”

“Ban zan hana ka ba, amman kayi taka tsantsan, mai son abunka ya fika dabara. Ina Mama?”

“Tana Lafiya”

Sai ya kashe wayar. Ya faka motarsa a harabar gidan Anty Ummi. Yana shiga tana shirin office, yau kam farinciki shimfide a fuskarta.

“Yanzu nake shirin kiranka”

“Gani na zo, amman ban karya ba”

“Baka da matsala ga abinci nan a dinning, idan ka gama ka shiga dakina ka kara turare direba zai kaika Anka, abunda za aka bata yana bayan motar”

‘Really...? ’

Ya fada a ransa, a fili kuma sai ya ce

“Okay”

Ya zauna saman kujera, yana hade yawun bakinsa. Sai da ta dauki jakarta ta kai bakin kofa sannan ta kira shi.

“Zain...”

Juyowa yai ya kalleta.
Chapter 25 · 0% Book details