Sashe 11
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Shiga tsakanine Shugabata, ya kamara ki farka daga dogon bachin da kika dade kina yi, mutuwar Haleema ishara ne a gareki musamman dan ta da aka cire a mace, kece kadai mace data dace ta zama matar Zain a yanzu ke ce kadai kika dace ki haifa masa yayan da zasu milki garin nan a watan wata rana Shugabata komai a hannunki yake, Hajiya Yalwa tana son ki fiye da kowa, haka ma Mai Martaba to amman mi tasa Zain ya tsaneki? Bayan kuma a can baya yafi kowa kaunarki?”
Fuskar mamaki da tunani tai.
“Na dade ina neman wannan dalilin”
“Daga ranar da kika bi shi zuwa gidan yar uwarsa, ya soma canja miki ko ba haka ba? Daga ranar ya kamata ki gane ba a banza ya barki ba, yanzu ma idan kika yi sake zai sake tsallakeki ya fada kan wata”
A fusace Hameeda ta mike tsaye tana nuna mata kofar fita.
“Abida fita ki bar min dakina...!”
“Allah ya huci zuciyarki”
Ta tashi da sauri jikinta har kyarma yake ta fice daga dakin kamar zata fadi. Kai Hameeda ta dafe yana busar da iskar bakinta.
FARHAT POV.
Bayan sun dawo cikin gida ne, Ya Bashir ya rufe Anty Rukaiya da fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ransa ya bace sosai akan abunda ya faru da Farhat.
“Ban taba ganin mahaukaciyar mace irinki ba, yarinyar nan amana aka bamu ita, bayan ta zo nan ta waye ta goge zaki turata kauye cikin dare? Akan wani dalili zaki turara gida? Da wani abun ya sameta me zaki fadawa mutane”
“Bata min rai tai, na tarar bata yai girki ba kuma yara suna jin yunwa dana mata magana sai ta ce min ba zata girka ba, nai mata fada ta mayar min, wannan dalilin ne yasa na koreta”
Daga shi har Farhat kallonta suke kallon mamaki, miyasa ta boye bata fada masa ba? Shine abunda ya tsaya a zuciyar Farhat, shi kuma yana mamakin wannan kankanen dalilin da yasa ta kori Farhat saboda shi.
“Yanzu saboda wannan kika tura yarinyar kauye cikin dare? Rukaiya ina hankalinki yake ciki ne? Yanxu da wani abun ya sameta wa za a zarga?”
“Kayi hakuri, an riga an rubuto haka shiyasa na aikata, amman ba zan sake ba insha-Allah. Ki yafe min Farhat kin ji?”
Ta karasa tana kallon Farhat fuskarta a raunane, idanuwanta narau narau. Farhat dai bata ce komai ba ta tashi ta nufi dakinta idonta cike da kwalla. Ya Bashir ma dakinsa ya nufa cikin mugun bacin rai, daman tun jiya yake tambayar Farhat tace masa tana gurin Anty Ummi wai zata taya ta kwana.
Rasa tai abunda ke mata dadi, tasan fadin ba shine alheri ba idan ma ta fada ta ya zata bullowa lamari, sai a yanzu ne take yi lamarin kallon da harara, ta kasa fayyace mai gaskiya tsakanin mijinta da kuma kanwarta, amman taya Ya Bashir xai nemi Farhat? Me kuma xai sa Farhat tai mata karya? Wata kila dan suna Uba daya, ko kuma dan bata sonta kamar yadda take gani, idan kuma Farhat gaskiya ta fada mata fa? Bata ga dalilin da zaisa taje waje ta yada labarin gidan mijinta ba idan ma har gaskiya ne, miyasa bata same ta da zance ba? Miyasa ita bata taba ganin alamun hakan ba? Kai ta girgiza ta mike tsaye tana jin kamar an dora mata wani abu saman kan, bata san da isa bedroom dinta ba har sai da tai karo da kofar dakin.
“Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un”
Shine abunda take ta maimaitawa har ta isa gaban madubi ta dauki wayarta, contacts ta shiga neman Number Nawwara, har ta kai ga wacce aka rubutawa Mrs Jibril Makama babu bata lokaci tai dialing. In few minute Nawwara ta dauka tare da sallama.
“Wa'alaikissalam, Nawwara good morning Nawwara”
“How are you Ma'am?”
“Ina lafiya, Mrs Jibril ina daya daga cikin masu bibiyar shafinki na Instagram da kuma facebook, sannan ina daya daga cikin members dinki na whatsapp”
“I'm glad to hear that, akwai wani taimako da zan iya miki?”
“Ina son ganinki inda hali”
“Gani na ba shi da wahala, sai dai ni ina Sokoto ne, ki fada min matsalarki wata kila zan iya hadaki da wacce zata miki maganin abun a kusa da ke”
A maimakon ta amsa ta, sai kawai ta kashe wayar fuskarta dauke da damuwa.
“Anya zan iya tona sirrin gidana? Taya zan bar wani ya san sirrina?”
Ta tambaye kanta ba dan ta san amsar ba, jin tashin motar Ya Bashir ya tabbatar mata da cewar ya fita. Da sauri ta fito falo sai ta samu yaranta sanye da uniform sun zauna saman kujera idonsu kan tv.
HAFSATU MANGA POV.
Sai bakwai da rabi Zain ya shigo asibitin, hankalinsa gaba daya yana gurin Hafsat, da ita ya kwana a ransa, hakan yasashi yin sammakon shigowa saboda ya dubata, kai tsaye Mr Zain rooms ya nufa, yana isa ya tura kofar dakin da take ciki. Yayi mamakin ganin gadon ba kowa ga robar jinin sai diga take kasa, sai dai hakan be hanashi karasawa cikin dakin ba, a zatonsa ko tana bandaki ne, dan yasan da fita tai daga asibitin gaba daya dole za a sanar da shi. Kunnensa ya kai jikin kofar toilet din, amman be ji motsin ruwa ba, hannu ya kai ya tura kofar bathroom din, sai yaga wayam babu kowa a cikin. Hakan yasa shi juyowa ya karaso gurin gadon yana dubawa, but still bata nan, har zai juya sai ya jiyo numsharin bachinta karkashin gadon. Dukawa yai ya leka.
Bachin take a takure, tasa dayan hannunta ta dafe dayan da har yanzu be daina zubar da jini ba. Ya dade yana kallon fuskarta kamin ya mika hannunsa ya janyota.
“Wayyo.... ”
Ta saka ihu.
“Shiiiiiiiiiiiiii”
Ya fada yana dora yatsansa saman lebensa. Kokarin komawa ta rika yi har sai da ya ture gadon can gafe ya iya fitowa da ita gaba daya.
“Jinina wayyo jinina”
Tsayawa yai yana kallonta ba dan yasan abunda zai ce mata ba.
“Bana so, ka kaini gida dan Allah, jinina suke diba”
“Sa miki ake yi”
Ya fada a hankali muryarsa kasakasa kamar mai tsoron magana. Bata saurareshi ba har yanzu kokarin kwatar kanta take daga rikon da yai mata, duka hannayenta biyu ya hada a hannunsa daya ya rike ya matse sosai har sai da taji zafi, a dole ta tsaya ta kalleshi har natsuwa ta shiga jikinta.
Sai a yanzu take gene shi tabbas tasan shi, shine na gidan da ta gudo.
“Kai ne wannan yaron ko?”
Ta fada cikin muryar shagwaba tana kokarin yin kuka. Be amsa ta ba sai kawai ya sassauta rikon da yai mata. Ya tashi tsaye ya dorata saman gadon zaune, ta sauko tana kallon cikin idonsa, ya sake dorata ta sake saukowa.
“Ni ba zan kwanta ba jinina suke sha ka kaini gida dan Allah”
“Hadari kikai shiyasa aka kawo ki nan ake miki karin jini”
“Kai ka kade ni ko?”
Kai ya girgiza mata alamar a a.
“Kai ne na sani, ka biyo bayana ya bi ta wata hanyar ka kade ni kaso na mutu ko?”
Ya tsaya kallon dikin dake kanta da gefen idonta ba tare da yasan abunda zai fada mata ba. Ita kallonsa take da kyau irin kallin nan da ke nuna ba bana Allah da Annabi ba ne.
“Kai da kanenka ka zo?”
Be amsata ba, itama bata tsaya jiran ya amsa ta din ba ta cigaba.
“Gashi nan kusa da kai, ku biyu ne masu kama”
Kyakkyawan murmushi ne ya bayyana a fuskarsa wanda ya karawa fuskarsa kyau da annuri.
“Jiri ne yake dibanki hau gado ki kwanta”
Ta lake kafada.
“Ni ba zan kwanta ba, dakin ma juyawa yake”
Ta kai zaune tana rumtse ido tare da dafe kai, sai ta fashe da kuka.
“Dan Allah ka kaini gida, bana son nan”
“Kina son allura?”
Tayi saurin bude ido.
“Aa wayuo ni Allah, Dan Allah ka kaini gidan Sarki, a garinmu idan mutum ya bata gidan sarki ake kai shi”
Ta fada tana wani abu da ido, sai lumshe suke mata, bakinta kuma a tabe kamar mai shirin yin kuka.
Kallonta kawai yake fuskarsa da murmushi, haka kawai yake jin tana burgeshi, daga kukanta har dariyarta burgeshi suke. Ganin yana murmushin yasa ita ma tai dariya ta rausayar kai.
“Dakin nan zai fado mana fa”
Hannunsa ya mika mata, ta rika ta tako kusa da shi sai ya risina daidai ita ya dora kanta a kafadarsa.
“Rumtse idonki”
Ta rufe idon kamar yadda ya bukata. Yana kokarin tashi tsaye Ibrahim ya turo kofar dakin ya shigo.
“Har ka shigo?”
“Ee wannan yarinyar na zo dubawa”
Ya amsa bayan ya tashi tsayen. Ido daya Hafsat ta bude ta kalli Ibrahim din, sannan ta rufe.
“Miyasa nake ganin mutane biyu biyu?”
Ta tambaya kadan kadan dar kar Ibrahim din yaji. Murmushi ya sake yi a karo na biyu yana kallon Ibrahim.
“Wacece wai? Magana take ko?”
Zain ya kada masa kai.
“Ina ka samo wannan yarinyar ne?”
“Daga sama ta fado”
“Wallahi ba daga sama na fado ba ina da iyaye, amman duk sun mutu, an kashe kowa garinmu a kauyen kufawa nake, gayu suka je suka kashe kowa da kowa sai an kalilan suka tsira, nima wani mutum ne ya kawo nan garin, na boya bayan gidansu wannan yaron shine ya ganne da naje gidansu na saci abinci, har aka yi ruwa ya jika ni sai kuma ya dawo da safe shi da matarsa suka je dani gidansa sai suka ce zasu kaini gurin yan sanda ni kuma nai kuka sai wannan yaron ya cewa matarsa kar a kai ni a bari sai gobe, sai suka fita, ni kuma na dinga kuka sai wata yarinya mai kamada roba ta fito, nace ta bude min kofa tana bude min na fito, mai gadin ya tare ni nace masa yarinyar ce ta aikeni na dauko kayana haka nai sai na gudu ina tafiya sai wannan yaron yazo da wata motar da gudu ya kade ni....”
Ta karasa tana kuka, tun da ta fara maganar bata tsaya ba, sai da ta kai aya, duk maganar da take bata bude ido ba, hannayenta kawai take motsawa.