← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 93

Sashe 38

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Da ita kadaice ai da sauki, wani abun na aikata abunda hankalina ya kasa kwanciya a shi”

Ya dago ya kalleta da kyau.

“Minene?”

“Kasan yarinyar kauye nan da Zain ya kawo a gidan nan, na bata ita a kaita garinsu yau, kuma har yanzu mutumen be kirani ba, idan na kira kuma bata shiga”

“Miyasa kika maida ita?”

“Bata jutuwa da Amal, bana son nai mata abunda zai sa ranta ya bace saboda marainiyace, amman a duk lokacin da nai mata fada sai tai ta kuka wanda hakan yana daya daga cikin abunda yake sa Zain yake kallon ina musgunawa yarinyar, kuma Zain yana son yarinyar nan sosai ina tsoron abunda zai faru saboda karamar yarinya ce, beside bamu san daga ina take ba, yarinyar bata da yanayi da kauye, kawai dai akwai kauyanci ne a tare da ita, idan wani abu ya faru Abban Amal kasan ni zuri'ar Mai Martaba zasu dorawa laifi, amman shi Zain ya kasa ganewa”

“Wa kika bawa ita ya kai ne? Ina kika samu mutumen kin sanshi ne?”

“Ban sanshi ba, amman kawata ta sanshi Hajiya Juwairriya ce ta hada ni dashi, tace dan kauyen ne yana kawo musu sako daga kauye shi direba, shi ma ya bani labarin cewar komai ya koma daidai a garin”

“Amman baki da hankali Aminatu, taya zaki hadata da mutumen da baki tabbatar da gaskiyarsa ba? Ita kanta Juwairriya ai ba wani dogon sani tai masa ba, yanzu idan wani abu ya samu yarinyar mutane fa? Mai zaki ce?”

“Dan Allah ka tayani nemansa.”

Ta fada idonta na cika da kwalla.

“Babu ruwana a ciki, da kika tashi yanke hukuncinki kin nemi shawarata ne? Ko kin fada min abunda zaki yi sai bayan ki aiwatar ta kwabe miki zaki dawo neman dauki a gurina”

Tashi tai ta fice daga dakin da zimmar komawa part dinta ta kira kawarta Hajiya Juwairriya.
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 28

Har garin Allah ya waye Zain be rutsa ba ya nemi dalilin rashin bachi ya rasa, bacin rai ne ko kuma tunanin halin da Hafsatu manga take ciki? Bashi tabbacin dalilin rashin bachinsa amman yana da tabbacin a duk inda Hafsatu manga take a yanzu tana cikin wani hali domin jikinsa ya bashi haka.
Kiran sallah farko ya sauka daga kan gadon ya shiga bathroom yai alwala ya fito rike da tawul yana goge ruwan fuskarsa, kofar fita ya nufa bayan ya jefar da tawul din saman gadonsa. Yana bude kofar ya ci karo da Farhat kwance a gurin ta dunkule cikin bedsheet tana sharar bachi, tsalaketa yai ya sauka downstairs.

Motsin fitarsa ne ya tasheta daga bachin da take, kiran Sallah da take ji ne ya tabbatar mata da asuba ta yi, sai tai saurin leka dakinsa daga baya nan sannan ta tattara bedsheet din da filo ta koma dakinta, tana shiga tai alwala raka'atayil fajir ta fara yi sannan ta tai sallah asuba. Har ta gama addu'o inta ta fito ta shiga kitchen be dawo ba. Ruwa zafi ta fara dorawa sannan ta koma dakin, inda ta dauko acan zanen gadon ta sake budewa ta dauko wani ta shimfida, sannan ta gyara komai a muhallinsa, babu datti a dakin amman hakan be hanata sharewa ba ta goge ta saka air freshener, bayan ta rufe dakin ta dawo downstairs tana gyara. Daman can gyaran gida baya damunta ta saba da yinsa a gidan Anty Rukaiya, girki ne kawai zai wahalar da ita. Ko da goma tai ta gama komai cikin har da abun karyawa, bayan ta gama jerawa ta nufi dakinta tai wanka sai ta shirya cikin farar shadda, bayan ta gama ta sauko ta dauki breakfast din Zain ta shiga dakinsa ta aje, tna kokarin juyowa taji shigowarsa.

“Breakfast na kawo maka”

Ta fada tun kamin ya tambayi dalilin shigowarta dakin.

“Karki sake shigo min daki”

“Insha-Allah”

Ta fada tana hade wani abu mai daci daya tsaya mata a makoshi, juyawa tai ta fita shi kuma ya shiga bathroom, zaune yai cikin bathtub bayan ya tube kayan jikinsa ya kunna shower ruwan yana sauka saman kansa, rayuwarsa ta baya ce ta dawo masa lokacin da suke tare da Haleema.

_Wata rana zata zo Zain, ranar da zamu rayu ni da kai da wata mace a cikin gidan nan, ko kuma kai a rayu da ita a lokacin da bana raye, amman ina kishin wannan ranar Zain ina kishin macen da zata dafa maka abinci ka ci, ina kishin macen da zata tsaya daidai nan a zuciyarka_

Ta fada tana nuna saitin kirjinsa yayinda take zaune saman jikinsa yana rumgume da ita. Hannunta ya rika ya sumbance shi sannan yaja hancinta.

_Babu zuwan wannan ranar Hamie babu kowa a duniyar mu sai mu kadai_

Ta dauke hannunsa daga saman fuskarta ta dora saman tsohon cikinta.

_Very soon zaka zama uba kai ma, kamar dai mai martaba, amman Zain kai min wani alkawari mana? Zaka sakawa yar da na haifa sunana, idan kuma Namiji ne a saka masa sunan Mai Martaba_

_I will_

“I will”

Ya furta yana lumshe ido, tare da busar da iskan dake cikin bakinsa, a Kasale yai wanka ya fito daure da tawul, a baki gado ya zauna zuciyarsa na raya masa abubuwan mabanbanta. Ya dade a zaune kamin ya tashi ya shirya cikin kananan kaya sannan ya feshe jikinsa da turare. Downstairs ya sauko ya nufi kitchen ya hada tea da kansa, hakan nan kawai yaji yana marmarin indomie he remember last indomie da suka ci tare da Hafsatu manga, da kansa ya dafa ya zuba a plate ya dawo falo har ya zauna zai ci sai kuma yaji ba zai iya ci ba, sai kawai ya dauki tea ya sha.
Bayan ya gama ya tashi ya nufi kofar fita, yana bude kofar ya samu sarkin dogarai tsaye kamar daman can jiran fitowarsa yake. Sarkin dogarai na gani Yarima ya risina kasa ya gaisheshi.

“Allah ya taimakeka, na sa an bincika an tabbatar da yarinyar nan bata je ba, sun ce ba a kawo wata yarinya daga birnin zuwa cikin kauye ba, Sarkin garin ma baya cikin garin wazirinsa ne ke rikon gari”

“Na gode”

Zain ya juyo ya dawo cikin falon, a kokarin da yake na ya danne zuciyarsa ne ya kira Anty Ummi amma sai ya kasa, dan haka ya kira abokinsa Ibrahim.

“Please ka tambaya min Anty Ummi ina ta kai yarinyar nan an bincika bata cikin garin”

“No Look Ibrahim ni ba zan iya kira Anty Ummi na fada mata haka ba, be kamata wannan yarinyar ta shiga tsakaninka da yar'uwarka ba abun....”

Be gama fadin abunda zai fada a Zain ya kashe wayarsa. Zaunawa yai saman kujera ya dafe kansa ya runtse ido.

*** *** ***

Tun da suka barin garin gusau take bachi har suka shiga garin Kaduna, hayaniyar motoci dake layin go slow ne ya tasheta, mutumen na ganin ta farka ya sake mika mata lemun daya bata dazu ta sha, sai ta karba wannan karon bata sha ba sai ta rike tana ta kallon titi kamar tai kuka.

“Sha”

Ya katsa mata tsawa, sai ta lake kafada ta ki ta sha ta kasa masa kuka.

“Duk baki sha shi ba sai nai miki dukan tsiya”

A dole ta kafa baki ta sha tana kuka, nan da nan bachi yai gaba da ita. Bata sake farkawa ba har sai da ya farkar da ita da kansa. Cikin magagin bachi ta bude idonta sai yasa hannunsa ya daukota ya dora saman kafadarsa, wani dogon guri ya bi da ita ya dade yana tafiyar sannan ya iso wani babban gida mai cike da mutane, da alama manyan mutanen sun sanshi sai gaisheshi suke har ya isa wani babban falo. Saman kujera ya zaunar da ita ta dauko ruwa ya bata, kadan ta sha sai idanuwanta suka wartsake.

“Ba nan ne gidan mu ba”

Ta fada tana karewa falon kallo, be kula ta ba sai wata kofar yake kallo kamar mai jiran fitowar wani, ya kusan minti latatin a gurin sannan wata dattijor mace ta fito daga kofar da yake kallo tana sanye da doguwar rigar atamfa hannunta rike da waya, idanuwanta kuma sanye da farin gilashi.

Sai da ta zauna saman cushion sannan ta kalli mutumen.

“Rayyanu”

“Na'am Hajiya ina wuni?”

“Lafiya kalau, har ka zo da yarinyar”

“Ee gata nan, ke gaishe ta”

Ya fadawa Hafsatu manga, sai ta lake kafada

“Ni ba nan aka ce a kawo ni ba”

Hajiyar ta maida dubanta gurin Hafsatu manga, sai kuma ta soma taba katuwar wayar dake hannunta.

“Ina fatar dai iyayenta sun san inda za a kawo ta?”

“Ee da amincewar su aka kawota nan, sai dai sun ce mata ba nan za a kawota ba shiyasa kika ji tana fadin haka”

“Yayi kyau, ta balaga kuwa?”

“Aa bana jin haka Hajiya kin ga dan jikinta yadda yake ai, bana jin ta balaga”

“To kasan ni bana son yaran kanana kamar wannan, saboda suna da wuyar sha'ani kuma ba ma aikasu ko ina aiki sai sun balaga sai an koya musu komai dan bana son a rika zuwa ana min complain, dan haka ka fadawa idan sun aminta sai musa Isa yai mata allura anjima”

“Iyayenta basa da matsala Hajiya, na fada musu komai kuma sun aminta”

“To ba matsala zan yi ma Isa waya sai ya zo yai mata allura, kaita ciki Siyama ta bata abinci”

“Wallahi ni ba za a min allura ba wayyo Allah na”

Shine kawai abunda Hafsatu manga take fada tana kuka iya karfinta, Hajiyar ko dagowa ba tai ta kalleta ba har ya shige da ita wani dakin.

HAMEEDA POV.

Tana tsaye jikin window tana tsinkar Sarkin dogarai tsayin da yai a kofar falon Zain da kuma fitowar da Zain yai suka yi magana. Tana ganin ya fito Zain ya koma ciki sai tai sauri juyowa ta baro jikin window ta dauki wayarta ta danna kira.

“Hello Isma'il”

“Gimbiya kina lafiya”

“Lafiya kalau ya aiki?”

“Ban ji ka ba har yanzu”

“Yau nake da niyar kiranki, maganar ba zata yiyu ta waya ba ya kamata mu hadu gaskiya”

“To ka zo gida anjima da dare”

“Okay Allah ya kaimu”

“Amin”

Ta sauke wayar.
Chapter 38 · 0% Book details