← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 93

Sashe 28

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kai ka kawo bukatar da ka san zata batawa kowa a gidanku rai, to miye abun damuwa dan mai martaba ya saka maka wadannan dokokin? Indai har kana son aurenta dole kai hakuri ka zura musu ido”

“Amman kasan ni ba zan yarda su wulakanta min mata ba ko? Ko bana son ta idan na aureta hakokinta suna kaina kuma tana karkashin kulawata ba zan yarda ko maganar banza su fada mata ba”

“Ni ma ban ce ka yarda a wulakantata ba, amman ka shirya fuskantar kalubale ta ko wane bangare, kai kana ganin ma Farhat din da iyayenta zasu yarda yarsu tazo gidan a matsayin kuyanga?”

“Dole su aminta mana, a kowa talaka yaji yarsa zata shiga masarautar Rishim a matsayin baiwa ma zai yarda balle kuyanga, beside bana jin Mai Martaba zai nuna musu haka a fali nafi tunanin a cikin masarautar yake nufi ba da iyayenta ba”

“In dai har haka ne, be tsaurara ba kamar Dada ba, ni na dauka ma ba zai amince ba shi da Dada, ganin Hameeda a gafe”

“Hameeda yanzu ba ta nawa take ba, and ta bani goyon baya dari bisa dari, kusan ma ita ta cilasta Dada amincewa da kudirina, Ibrahim ta canja fa trust me”

“Ba zan iya yarda da ita ba, amman zan iya yarda da kai ba zaka yi nasan ba zaka bata damar cin galaba akanka ba ko matarka”

“Bari nai tunani daya mana, karka sa na raba hankalina biyu Hameeda ta canja wannan nake kokarin sakawa a zuciyata, so that na samu damar jinyar bangare daya”

“Yayi kyau ina maka fatar alheri ango”

Tsaki yaja ya kashe wayar. Kana ya danna horn Malam Adamu mai gadin Anty Ummi ya bude masa gate din. A dade a cikin motar bayan ya faka motarsa sannan ya fito ya nufi babbar kofar falonta.
Hafsatu manga ya samu tsaye gaban Plasma remote a hannunta sai matsawa take ba dan tasan abunda take dannawar ba.

“Mama”

Ba shiri ta saki remote din ta juyo a firgice dan bata san da shigowarsa ba sai yanzu. Murmushi ya sakar mata ita ta mayar masa tare da fadin

“Zat...”

Yana kokarin zama sai ya fasa, mamaki karara a fuskarsa gurin da take tsaye ya nufa ya dafata.

“Me kika ce Mama? Sake cewa naji”

“Zat...”

Ta fada tana saka hannu a baki.

“Wow what a surprise, how how... ”

“How...?”

Anty Ummi ta amsa masa yayinda take fitowa daga wani bangare na falon wanda zai sadaka da tsakar gidanta dake can ciki.

“Yes Anty magana tai fa, kuma tunda aka mata gyaran halshe bata magana”

Anty Ummi tayi dariya.

“Gashi nan dai tana magana, kuma tunda safe muke firarmu da ita”

“Ya akayi kika sakata tai magana?”

“Kai ba doctor bane miyasa baka saka ta tayi magana ba?”

“I can't force her”

“So you mean i force her?”

“No i mean kinsan tana tsoronki”

Dinning Anty Ummi ta nufa tana fadin

“Ba wani tsoro, kawai dai baka san yadda zaka yi controlling dinta bane, ba maganar ce ta dauke ba tana tsoron magana ne saboda tana ganin kamar halshenta be gama warkewa ba, secondly tana son dadi so idan kai mata alkawarin zaka bata abu zata maka abunda kake so, na mata alkawarin indai zata cire tsoro tai magana zan rika bata ice cream da chocolate a kullum and i warning her idan batayi magana ba zan yi reporting dinta to police, amman idan tai magana zan siya mata kaya kuma zan kaita gurin Mamanta, shine kawai”

Zaunawa yai kasa carpet din ya dauketa ya dora a saman cinyarsa cike da jindadi.

“Cutest ni kike kin yi ma magana ko?”

Sai tai dariya tasa hannayenta ta rufe idonta, shima dariyar yai zuciyarsa cike da jindadi ya shafa kanta ya sumbanci goshinta.

“Zain miye haka?”

Anty Ummi ta katsa masa tsawa.

“Karamar yarinya ce, wannan da amin auren auri ai sai na haifeta”

Ya fada yana ci gaba da shafa kanta ba tare daya kula da abunda yai ba.

“Ko karamar yarinya ce bana do karka sake, a Muslim dubuwar da ta kai shekara tara ta isa balaga, kuma wannan yarinyar zata kai haka ko ma tafi so abunda kake yi ba shi da kyau”

Kallon mamaki yai mata yana murmushi.

“Ke da kike cewa yarinya bata balaga sai ta kai 18”

Bata amsa masa ba, ta nufi hanyar kitchen cikin yanayin dake nuna bacin ranta. Bayan ta shige ya maido kallonsa gurin Hafsatu wacce ke ta kallonsa tun dazu ganin abunda ya mata wanda bata san sunansa, gira daya ya daga mata alamar why, sai ta sauka saman kafafunsa ta nufi kitchen sai waigensa take tana wani yatsina fuska.

Tashi yai ya nufi dinning ya hada ma kansa breakfast, yana cikin karyawa ne Anty Ummi ta fito daga kitchen din ita kadai.

“Ina Mama?”

“Ina ruwanka da ita”

“Like serious?”

“Zain bana son shakuwar dake shiga tsakaninku da ita ne”

“Why..?”

Bata amsa shi ba, taja kujerar dinning din ta zauna.

“Fada min ya kuka yi da Mai Martaba?”

Be boye mata komai ba from a to z, bata jidadin yadda Mai Martaba da dada suka yi ba, amman bata da wani abun yi bayan amincewa kamar yadda kanen nata ya amince.

“Zan je har can na fada mata ta sanar iyayenta so that su sani, kaga da an mata magana sai ta amince”

Uffan be sake cewa ba, sai ya tashi tsaye yana kurba tea.

“Na wuce office”

“Allah ya tsare”

“Amin”

Ya amsa yana kallon Hafsatu manga data leko a kofar kitchen, hannu ya daga mata sai itama tai masa bye-bye da hannunta mai kumfa da alama wani abu take wankewa. Har ya juyo kamar zai cewa Anty Ummi wani abu sai kuma ya juya yayi ficewarsa.

*** *** ***

Tunda ya fita be dawo gidan ba sai washe gari, kasancewar jiya yayi dare so daga gurin aikin sai ya wuce gidansa.

Tun daga yanayin fuskarsa Momy ta san akwai abunda yake faruwa, da kallo ta bishi har ya zauna saman kujera yana kallon Doc Hafsat dake sanya Hijab.

“Momy ina kwana?”

“Lafiya kalau, ya Zainab”

“Tana lafiya, Momy na transfer to Kaduna”

Duk kallonsa suka yi cikin rashin jindadi.

“Yaushe?”

“Jiya”

Ya fada yana wara ido.

“Ina yarinyar nan take?”

“Ya dauketa tun jiya”

“Saboda me kika bashi ita?”

Ya tambaya a tsawace.

“Ina da dalilin riketa ne na hana masa ita?”

“Yes ai bashi da alaka da ita, sato yarinyar nan yai fa”

Momy tayi saurin rufe bakinta.

“Dan Allah Auwal ka rufa mana asiri, wani irin satowa kuma? Idan ma satota yai ina ruwanka Auwal?”

“Haba Momy wane irin ina ruwana kuma? Ai aikina ne kula da lafiyar al'umma da dukiyoyinsu, dan haka dole ne na bincike shi”

“Taya zaka tunkari babban mutum kamarsa kace zaka bincikesa?”

“Ni ba ruwana da milkinsu ko mukaminsa ko sarautar gidansu, aikine ya biyo ta kansu idan ta kama ma har cikin masarautar zan shiga na bincika”

“Dan Allah dan girman Allah Auwal ka rufa mana asiri, dan Allah ka Kyaleshi”

Momy ta fada tana hade hannayenta alamar roko, Hafsat ma ta bata fuska kamar ta fasa kuka sam bata ji dadin abunda Yayanta yake magana a kai ba. Sai a lokacin ma ta tuna da abun hannunta da Doc ya aiko mata da sakon ta taho da shi ta kawo masa office.

“Ina tunanin ma ya mayar da ita gurin iyayenta”

“Inji uban wa? Ke ma da ke aka hada kai aka sato yar mutane you will be involved”

Ya fada a tsawace, sannan ya mike tsaye ya fice daga falon cikin bacin rai.

[3/4, 3:36 PM] Mrs Zainab Jega: *HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

2⃣2⃣

Within a week Mai Martaba yasa aka yi komai kamar yadda ya fada, a sirarance aka daura auren bayan iyayen Farhat sun yarda da a daura a can saboda ta nace akan ita tana son Zain sai dai ba a fada musu cewar zata shiga fadar a matsayin kuyanga ba, wannan tsakanin Mai Martaba ne da iyalansa.

Da farko sun nuna kin yarda sai dai jin wanda zai aureta ne ya suka bada goyon baya har ma suna murna. Ranar jumma'a aka saka za a daura auren kuma ranar aka yi walima domin sarkin anka ya aiko a fada musu za a wuce da amarya. A garin Anka aka yi walimar babu wani wakilin ango ko yan uwansa a gurin walimar duk kuwa da kasancewar ba a fadi ko waye ango ba, yan'uwansu na nesa ma babu wanda ya san da maganar aure.
Daga ranar da aka tsayarda maganar sai kukan Farhat ya koma sabo, na daya mahaifiyarta bata farinciki da auren, ita kanta tasan makiyinta zata aura wanda aka cilasta masa aurenta, bata da wani zabi face na yarda da yadda kaddararta tazo mata, sai dai ta kudirta a ranta cewar ba zatayi zaman aure mai tsawo da Zain ba, ita burinta ta tsallake wannan siradin.
Ranar aka yi walimar a ranar mahaifiyarta bata yi wunin biki ba abunda aka san ko wace uwa na yi idan za a aurarda yarta, a ranar Farhat ta sha kuka marar misaltuwa duk wanda yaga irin kukan da take ya san bata son auren ko kuma akwai wani abu daya faru.

Misali karfe hudu na yamma aka aiko da manyan motoci masu kyau daga masarautar Rishim domin daukar Amarya, a lokacin ne aka shiga da amarya dakin gwaggonta danyi mata huduba, bayan an fito da ita daga can aka kaita gidan kawonta, sannan aka sake dawowa da ita dakin mahaifiyarta.
Inna na ganinta ta kawar da kai kamar wacce bata son kallonta, hakan be hana Farhat karasa inda take zaune ba ta kama kafafunta.

“Allah kadai yasan dalilin daya sa na amince da auren fiye da auren Ya Bashir, na san Ya Bashir dan uwana ne kuma mijin yaya, amman ba zan iya aurenta, ki yafe Inna dan Allah karki fushi da ni, ban sani ba wata kila ajalina na aura, akwai yiyuwar auren ya zame min silar samun aljanna ko wuta, ni kadai na san abunda nake ji Inna, dan Allah karki yi fushi da ni”

Kallonta Inna tai tana tabe baki.
Chapter 28 · 0% Book details