← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 93

Sashe 27

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta daga masa kai. Sai ya bude gefensa ya fita ya shiga cikin Jafatu din. Tana zaune cikin motar tana jiransa ta hango wani magidanci sanye da narkakkiyar shadda ya fito daga Jafatu din makkale da waya a kunnensa hannunsa daya kuma rike da wasu papers, daya daga cikin papers din ne ta fadi, ganin hakan yasa Hafsatu manga fita da sauri ta nufi inda paper take duk kuwa da irin tazarar dake tsakani ta dauko ta falfalo da gudu ta kawo inda yake yana kokarin shiga mota ta mika masa.
Kallonta ya tsaya yi sai ya katse wayar da yake da sauri ya karbi takardar bakinsa a sake kamar mai mamaki. Hannunta da Zain ya rika ne ya dawo da shi cikin hayyacinsa. Sai ya kalli Zain da sauri.

“Yar ka ce?”

Zain ya daga masa kai.

“Allah sarki yarinya mai hankali”

Mutumen ya fada yana shafa kanta, hannunsa yasa aljihu ya debo kudin da shi kansa be san ko nawa bane ya mika mata

“Miye sunanki?”

“Mama”

Zain ya amsa masa a takaice, sai yaja hannun Hafsatu manga ba tare daya bari ta karbi kudin ba ya nufi gurin motarsa da ita. Da kallo mutumen ya bita har Zain ya sakata mota ya tada suka kama hanya.

“Idan na sake barinki cikin mota kika fita sai na zaneki”

Ya fada yana kallonta. Ita kuma sai ta bata fuska kamar zata fasa kuka. Hannayenta ya kalla

“Ina abun hannunki?”

Ta duba hannun, ita ma sai a yanzu ta tuna data bar shi kam mirror Doc Hafsat da tai mata wanka dazu da safe.

“Yana gidansu Doc?”

A nan ma kan ta gyada. Sai ya dauke kai ya cigaba da tukinsa har suka isa gidansu Anty Ummi, sannan ya fita daga motar ya zagayo ya bude mota ya fito da ita. Tana ganin gidan Anty Ummi sai ta bata fuska tana hawaye. Be kulata ba har suka shiga cikin falon hannunta na cikin nashi.
Da kallo Anty Ummi ta bisu har ya zauna ita ma ta zauna kusa da shi tana hawaye.

“Still...?”

Ta fada. Kallonta yai.

“Where else zan kaita bayan nan?”

“Ba zamanta a nan ne matsala ba Zain, abunda zai biyo baya nake gudu”

“Babu abunda zai biyo baya, just trust me”

Ajiyar zuciya ta sauke.

“Ina fatar hakan”

Ledar ya bude ya dauko mata chocolate ya mika mata.

“Please Aunt a mana one plate you know i can't speak louder”

“One plate?”

Ya daga kafadunsa.

“Zan yi feeding dinta ne”

Har zata ce wani abu sai kuma ta tashi ta nufi kitchen ta zubo masa abincin. Da kansa ya rika feeding din Hafsatu manga har ta koshi sannan ya cinye ragowar. Anty Ummi na zaune tana kallon ikon Allah.

“You change Zain, kamar dai ba kai ba”

“Akwai wani sabo a tare da ni?”

“Babu, fada min dazu da kuka je gurin Farhat ya akayi?”

Tabe baki yai yana jin sauraren yadda sunanta ke masa daci a makoshi.

“Anty kin rage min girma da daraja da nake tare da ita, kin sa naje zance da yarinyar da tafi ko wace yarinya lalace a rashin kunya a duniyar nan”

“Wani abun tai maka ne?”

“No bata mon komai ba, amman dai kamar ita ma bata so”

“Kar wannan ya dameka, ka tabbatar dai ka sanarwa mai martaba”

Ya maida dubansa gurin Hafsatu manga data soma angaje bachin tana kwanto masa. Tasowa Anty Ummi tai tana kokarin rika hannunta.

“Zo dakin zu Amal ki kwanta”

Fisge hannunta tai ta rike na Zain. Haka ta wuni kusa da shi ko ina bata matsawa, dawoawar su Amal daga Islamiya ne yasa ta dan soma sakewa har ta sauko kasa ta zauna kusa da su tana kallon story book din da suke karantawa. Sai dare Zain ya baro gidan Anty Ummi a lokacin Hafsatu manga ta yi bachi kusan ma shi yai mata addu'a tare da Amal kasancewar gado daya suka kwanta.

GIMBIYA HAMEEDA POV.

“Farincikin ki ya fiye min komai a duniyar nan, zan miki duk wani abu da kike so Hameeda matukar ina raye.”

“Kai nake so”

“Gani ai kin samu ba zan taba barinki ba, tunda ni yayanki ne”

Hoton da suka dauka tare take kallo tana shafawa hawaye na sauka daga idonta, kunnuwanta da Memory na taro mata wasu abubuwan daga rayuwarsu ta baya ita da Zain.

“Ban san miyasa zuciyata ta kasa hakuri da kai ba! Ban san halin da zan shiga ba idan ka maye gurbin yar uwata da wata mace wacce ba ni ba, ina son ka Zain shin ko baka ganine?”

Ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.

“Miyasa har yanzu na kasa daina kuka? Mi yasa zuciyata take wahalarda ni? Babu farinciki da kwanciyar hankali a matar da zaka aura Zain, kuma wallahi sai ka gane shayi ruwa ne”

Ta share hawayenta sannan ta maida hoton cikin album ta maida cikin durowa ta tashi ta fita.

Share your opinions.
[2/26, 10:39 AM] Ayusher P: *HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

2⃣1⃣

Be jin zai yi breakfast a gida yau, hakan yasa shi shiryawa da wuri ya fito part dinsa ba tare da jiran an kawo masa abun karin ba. Part din Dada Yalwa ya fara zuwa domin mata barka da kwana, sameta tsaye jikin kofa rumgume da hannayenta a baya fuskarta ba yabo ba fallasa. Tsayawa yai yana kallonta.

“Dada lafiya dai?”

Bata ce masa komai ba ta juyo ta dawo cikin falon ta zauna, shi ma zaman yai a kujerar dake facing dinta.

“Dada ko dai ni na bata miki rai ne? Indai akan maganar aurena ne na janye ki saki ranki dan Allah”

Wani dogon numfashi taja ta sauke.

“Muhammad ni kamar mahaifiyarka nake, nasan da ace Hafsat ce a raye zata goya maka baya saboda abinda kake so ne, amman na kasa samu natsuwa da yarinyar nan da zaka auro, sai nake jin kamar babu alheri a auren nan da zaka yi”

“Indai har dan na rashin natsuwa ne, kar hakan ya dame ki akwai alheri a ciki, sai dai idan har baki son auren zan iya fasawa”

“Allah ya sanya alheri sai ka samu Mai Martaba ku yi maganar, amman ina son ka sani nan gaba kadan zan gabatar maka da wata bukatar, ko da wasa bana son ka musa min a kan haka”

Yayi shiru yana kallonta kamar yadda itama take kallonsa irin kallon dake nuna babu wasa a kalamanta.

“Zan miki duk abunda kike so”

Kishingida tai jikin cushion din.

“Ba zamu kashe kudi akan yar takala ba, ba za ayi dinner ko kamu a aurenta ba dauren aure ne kawai dole, saboda bana son duniya ta san waka aura har sai nan gaba, a sirrance za ayi auren dan bana son kowa yaji, auren nan ma a cikin fadar nan za ayi”

Kai ya girgiza.

“Haba Dada sai kace wanda zai auri karuwa?”

“Idan dokokin basu maka ba, zaka iya fasa auren”

Kansa ya shafa yana sauke ajiyar zuciya.

“Shikenan as long as ba zaku wulakantata ba”

“Wannan ya rage nata, tashi kaje Mai Martaba na nemanka”

Tashi yai tsaye ya fice daga falon, Dada na binsa da kallon jin haushi.
Sai ya bar part din Dada sannan ya kama part din Mai Martaba jikinsa a sanyaye yasan by this time Mai Martaba be isa fitowa falonsa na uku ba, wato falon daya ganawa da iyalansa kamar su Yaya da sauran wasu masu muhimmanci, babu tantama yasan Dada ta fada masa wata kila ma ransa ne ya bace.

A falon na biyu ya samu Mai Martaba zaune shi kadai kamar daman shi yake jira, cikin ladabi yai sallama amman Mai Martaba be ko kalli inda yake ba balle ya amsa masa, guri ya samu nesa da shi ya zauna a kasa yana mika masa gaisuwa. A take Mai Martaba ya daga masa hannu.

“Sanin kanka ne, Masarautar Rishim masarauta ce mai daraja da girma, a ko da yaushe ina fada muku kar kuyi abunda zai zubar da kima da darajar nasarautar nan.
A yau ina son na fada maka wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaka saka mahaifiyata ta nema maka alfarma mai girma irin wannan, ba zan iya musa mata ba”

Har ya bude baki zai yi magana sai Mai Martaba ya sake daga masa hannu a karo na biyu.

“Fada min wacece ita”

Ya tambaya cikin Izzar dake nuna bacin ransa a fili. Wani daukewar wuta Zain yai na wani dan lokaci a rayuwarsa ya tsani bacin ran mahaifinsa domin yana ganin shi kadai ya rage masa a duniya, ko ba komai uba yana da muhimmanci a rayuwa babu ta yadda zai yi farinciki idan Mai Martaba baya yinsa, can kasa kasa ya tsinkayo muryarsa tana fitowa daga bakinsa.

“Yar talakawa ce kuma a anka take zaune, amman tayi karatun boko da addini, gidansu mutane ne masu tarbiya...”

Mai Martaba yayi shiru na dan wani lokaci kamin ya ce

“Ba kai zaka fada mana tarbiyarta da rashinta ba, mu zamu binciko hakan da kanmu, ka taba zuwa kauye?”

“Sau daya”

Ya amsa da sauri.

“Kar kafarka ta sake taka kauyen nan, zamu saka sarkin Anka ya nema maka aurenta a sirrance, idan sun baka za a daura auren a nan fada, zata so nasarautar nan a matsayin kuyangar da sarkin anka ya baka, kar wani daga wajen familyn nan yaji maganar auren nan, ba zamu dauki kuskure daga gareta ba karta kuskura ta aikata wani wawanci a cikin masarautar nan”

“Duk yadda kake so haka za'ayi Mai Martaba”

Ya fada cikin tsantsar ladabi da biyayya. Da hannu Mai Martaba yai masa alama daya tashi ya bashi guri, haka ya tashi jiki ba gwari zuciya ba dadi.

Yana fitowa harabar gidan fadawa suka rika gaisheshi amman ko daga kai be yi ya kallesu ba balle har ya amsa musu, ba motar daya saba shiga ya shiga ba, wata ya shiga daban wacce take daya daga cikin motocinsa, yana fita daga masarautar kiran Ibrahim ya shigo wayarsa, a nan yake labarta masa komai abunda ya faru. Kamar yadda ya saba goya masa baya da shawarwari yau ma haka ne.
Chapter 27 · 0% Book details