← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 93

Sashe 77

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wannan wayar Farhat ce, na tabbatar akwai abunda na ke fada a ciki, na dauke wayar amman Allah be bani ikon jefarwa ba. Na san kowa zai yi mamakin abunda na fada, amman na gaji da rayuwar da na ke ciki shiyasa na fadi gaskiya, na cutar mutane da yawa, kuma saboda son Zain ne son da be amfanin min komai ba, duk kokarin da nai ban taba cin nasaraba, mafarkina be taba tabbatuwa ba, na yi damar zuwana a duniya yau, na yi nadamar sanin Zain a rayuwata, na bata sunan masarautar Rishim, na cutar da Yar'uwata, Farhat da Hafsat, ba ni da sa'a a rayuwata, da nasan haka rayuwata zata kasance da ban zauna da ku ba, na san Mai Martaba zai ji haushi na, Dada ma ba zata yafe min ba, ko ba dade ko ba jima nasan asirina zai tonu kuma Allah ba zai barni ba shiyasa na fadi gaskiya ta yadda za a yanke min hukunci daidai da abunda na aikata...”

Ta fashe da wani iri kuka mai ban tausayi da sosa zuciya. Barrister Hassana ta nufi laptop dinta ta kunna ta bude wayar ta cire memory card din dake cikin wayar ta saka a laptop dinta ta nemo video ta bude video ta mikawa muhti muhtin ya mikawa Alkali ya kalla da kansa, sannan ya miko mata laptop din.

“Ya mai shari'a, bisa ga amsa laifinta da Hameeda tai ba tare da batawa kotu lokaci ba, da kuma tabbacin abunda ta aikata a cikin daukar da margayiya Farhat tai wanda ya zame mana shaida, da kuma samunta da wayar da akai a gurinta, na ke rokon wannan kotu mai adalci da ta bada belin Hafsat kuma ta yankewa Hameeda hukuncin dai dai da laifin da ta aikata, ina rokon wannan kotun ta sa a kama Fauziya da Abida domin dukansu sun kashe rai kuma suna kokarin sake kashe wani ran ne, domin barin irin wadannan mutanen su cigaba da zama cikin mutane ba shi da wani amfani kuma barazana ce ga wasu rayukan, na gode ya mai shari'a, na gode ya mai shari'a”

Ta dan risina masa tana hawaye, sannan ta zauna tana kallon Husaina wacce ita ma hawayen take daga inda take zaune. Sai da Alkalin yai rubutu sannan ya dago ya kalli Husaina.

“Ko lauya mai kara na da wani abun da zata fada?”

“Babu ya mai shari'a”

Ta fada cikin muryar kuka. Sai ke maida kansa yai gurin takardun dake gabansa yana rubutu, dukansu abu daya suke yi ma kuka wato mahaifiyarsu, kowa yayi mamakin ganin Husaina tana hawayen a cikin kotu, ba yau aka fara shiga shari'a daya yai nasara daya kuma ya fadi ba, amman ganin dukansu suna hawaye shine abunda ya bawa kowa mamaki, meanwhile Anty Ummi hawaye take, duk wanda ke da alaka da Hameeda baya farinciki da abunda ya faru, Alhaji Habib da yan'uwansa sai yan'uwan Rufaida sune kawai suke farinciki. Ta bangaren Zain he feel Empty, ba farinciki kuma ba akasin hakan.

A natse Alkalin ya dago ya ce.

“Kotu zata dage wannan karar har zuwa shida ga watan bakwai, kuma ta aminta da bada belin Hafsat, kotu ta bada izinin kama Hameeda a kaita gidan kaso har zuwa lokacin da za a sake zama na uku kuma na zama na karshe, sannan kotu na umartar Dpo Auwal ya kama Fauziya da Abida ya gabatar da su a gaban kotu a ranar shida ga watan bakwai, kuma kotu ta bada umarnin a bincike kwakwalwar Hameeda domin tabbatar da lafiyarta kamin ranar shida ga watan bakwai”

Yana gama fadar hakam sai ga police din dake tsaye jikin kofa sun zo da sauri mace ta tashi Hameeda tsaye aka saka mata handcuff, baka jin komai a kotun sai sautin kukanta. Yar gandireba dake bayan Hafsatu manga ta ja gefe tana fadin.

“Jeka gurin mahaifinki”

Sai ta daga kai ta kalleta sannan ta maida kanta kasa ta fara takawa a hankali kanta a kasa har yanzu kuka take, Alhaji Habib na hango ta fito ya taso fa sauri ya nufo inda Hafsatu manga take, ita kuma ta nufi inda Zain yake, tasowa Zain ya dosota cike da zafin nama har ya riga mahaifinta isa inda take ya dauketa ya rumgume, sai ta kara fashewa da kuka. Fitowa yai da ita daga cikin kotu zuwa harabar gurin inda motocinsu suke.

“Shiii ya isa ai na fada miki za a fitar da ke daga nan, kin ga yanzu ba zaki sake komawa can ba”

“Zat ina mamata?”

“Nima ban sani ba, amman tana nan zuwa ita ta aiko wadannan mutane kanenta ne, kuma ga babanki can”

Ya karasa tare da sauke ta kasa, tana kallon Alhaji Habib ta sake kallon Zain tana kokarin shigewa jikinsa

“Ni ba babana ba ne”

“Babanki ne mana, baki ga kunyi kama ba? Kuma yana tare da yan'uwan mamarki ita ce ta turo su”

“Da gaske ita ce ta turosu? To ina su Inna Ladi”

“Ban sani ba, idan ta zo zata fada miki, Mama ashe kina iya magana ko kika ki magana a kotu”

“Tsoron Alkalin na ke ji”

Yan'uwan Rufaida na isowa suka dauketa suna shafa kanta kamar zasu cinyeta kowane fuskarsa dauke da murmushi wasu kuma na hawaye, karba karba suka rika yi da ita suna jin kamar mahaifiyarta ce.

Ibrahim ne ya karaso inda Zain yake tsaye yana kallon motar yan prison wacce aka saka Hameeda a ciki wacce aka zo da Hafsatu manga da ita sai a aka wuce da Hameeda aka wuce da ita ciki.
Anty Ummi ce ta fito rike da kafadar Husaina wacce ke ta rusa kuka ta nufi gurin motarta ta saka ta sannan ta zagayo mazaunin direaba ta shiga tai ma motar key taja ta suka bar kotun. Sai barrister Hassana wacce ta fito rike da rigarta a hannu ,dayab hannunta kuma rike da madaidaiciyar jaka mai dauke da laptop da kuma wasu takardun a cikin. Gurin da Alhaji Habib yake tsaye ta nufo amman ta tsaya nesa da su tana kallonsu fuskarta dauke da murmushi Idanuwanta na zubar da kwalla. Alhaji Habib na hangota sai ya doso inda take cike da kaunarta.

“Na gode sosai Hassana, karatunki ya yi min amfani Allah yai miki albarka”

Tasa hannu ta share hawayen.

“Amin Baba, nima ina rokon wata alfarma”

“Name whatever you want zan miki shi”

“Dan Allah ka yafewa Mama, na maka alkawarin zamu yi nasara, kuma nasan zama na karshe Alkali zai wanke ta ne kuma ya yankewa Hameeda hukuncin laifin da ta aikata”

“Ai na yafe mata, na fada miki na fadawa yan'uwanta na yafe mata”

“Ba irin wacan yafiyar Baba, tun da ta kamu da rashin lafiyar nan baka taka je ka dubata ba, saboda kana fushi da ita ko kace ka yafe mata hakam ba zai wadatar ba har sai kaje ka ganta, Baba ko ba dan tana matar ka ba, ni da Husaina muna tsakani ko dan ya kamata ka mutunta Mama, bana farinciki da abunda ta aikata, amman dukan dan'adam ajizine kowa be wuce fadawa cikin wannan halin ba, kuma ina tunanin a yanzu ma goge laifinta”

“Kin goge Hassana, kuma yau yau din nan zan koma kaduna ba sai gobe ba, zan je na dubata indai hakan ne abunda kike bukata”

“Na gode Baba”

Ya gyada mata kai, sai ta juyar da fuskarta gurin su Zain tana kallonsu shi da Ibrahim.

Su Hajiya Zarah da Maryam na isowa da labarin abunda ya faru gaba daya sai da masarautar ta girgiza, daman wasu sisters din Zain sun dawo da kuka. Babu wanda yaji dadin abunda ya faru musamman Mai Martaba wanda shine uba a gurinta a yanzu, yadda za a sanar da Dada Yalwa ne kowa ke tunanin, be shirya rabuwa da mahaifiyarsa a yanzu ba, sai dai yasan fada mata zai iya sanadiyar mutuwarta ko kuma faruwar wani abun saboda so da shakuwar da ke tsakaninsu da Hameeda.

“Babu wanda zai fadawa Hajiya abunda ya faru, kuma zan karbe wayarta gudun kar wani ya kirata daga waje da sunan jaje ya fada mata”

“Amman Mai Martaba baka tunanin zata tambayi Hameeda? Zata son jin halin da take ciki”

Cewar Hajiya Hadiza cike da damuwa.

“Za'a fada mata wani abun ne na dabam amman ba wannan ba, ko kuma a fada mata cewar ta ki ta bada shaidar ne a kotu shiyasa alkalin yasa a ka tsare ta”

Hajiya Maryam ta ce

“Sai dai zata dame ka da bukatar akayi wani abun a sakota, kasan yadda take jin Hameeda idan bata ganta a gidan nan ba, hankalinta ba zai taba kwanciya ba”

“Damuwata da zata yi zai fi sauki fiye da a fada mata gaskiya”

Ikram ta kalli Mai Martaba tana hawaye ta ce

“Na san zama na gaba alkalin zai yanke mata hukuncin kisa ne, kuma ya wanke Hafsat, dan Allah ka yi wani abu Mai Martaba Wallahi son Ya Zain ne yaja mata shiga wannan halin, ko abunda ta aikata a kwanakin baya har ta kirani a waya ni da kawarta muka tararda ita sai ta fada mana wai Ya Zain ya mata fyade ban yarda ba, amman ban tona mata asiri ba saboda na san dukan abunda take saboda so take yi, tana kokarin aikata abunda zai sa Zain ya so ta ne”

“Amman dukan abunda zai sa Zain ya so ta, be cancanci ta kashe yyarta ba, har ta kai ga Farhat, idan har aka barta ta cigana da zama a nan mu kanmu rayuwarmu tana cikin hadari, kuma ba zata taba barin Zain ba, bayan haka mutane da yawa sun sa ido akan shari'ar sai kuma aji Mai Martaba ya saka baki a ciki ko yayi wani unkurin? Sam hakan be dace ba a ganina”

Cewar Hajiya Hadiza. Ikram ta kalleta tana kuka.

“Tare muka tashi da Hameeda Hajiya, kin fi kowa sanin halinta ba haka yake ba, kuma ki misalta da ni ko Sapna idan dayan mu haka ta faru da shi ya zaki ji? Bata da uwa ba uba a yanzu bata da kowa sai Mai Martaba sai mu, ba a fili Mai Martaba zai dauki matakin ba, a sirrinsa zai yi, a biya diya ko kuma ayi wani abun a fito da ita dan Allah kar abari kotu ta kasheta”
Chapter 77 · 0% Book details