← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 93

Sashe 55

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Around takwas ya koma dakin dauke da cup din tea, saman mirror ya aje cup din ya kai hannu ya yaye zanen data rufa da shi, hannunsa ya dora saman kanta yaji yayi zafi sosai. Juya yai ya fita yaje ya dauko mata magani this time zauna nai bakin gadon sannan yasa duka hannayensa ya tallafota, cikin bachin ta bude idon tana ganin shi ne ta buge masa hannu.

“Ka kyale ni mana”

“Magani zaki sha da tea”

“Bana so ba zan sha ba”

Kallonta ya tsaya yi, nan da idonta ya kawo hawaye gashi kwayar idon ta kumbura.

“Kanki na ciwo”

“Babu ruwanka, ka kyale mana”

Yaja zanen ta sake lullubewa. Be san abunda zai sake ce mata ba, akwai abunda ya sani a yanzu be kyauta mata ba, yasan ba wannan lokacin ya kamata ya zo mata ba kuma a wannan yanayin ba, impact shi be ma taba sakawa ransa irin wannan abun zai faru tsakaninsa da ita. Hannu ya sake kaiwa ya yaye zanen. Sai ta fashe masa da kuka.

“Ka kyaleni mana”

“Da kin sha tea zan kyaleki i promise”

“Ba zan sha ba”

Ji yai kamar ya kyale but he can't yana jin kamar be kamata ya barta bata ci komai ba bayan abunda yai mata, and he feel her tears dake ta sauka a idonta, tana masa wani irin kallona na tsana.

“Me kike son ki ci?”

“Ban sani ba, ka fita ka bar min dakina”

“Zan fita idan kika sha, and stop crying”

Ji yake kamar ya zalumce ta, and what is more shameful ya sameta ba a yadda yake zarginta, ba zai iya nuna mata ba amman tabbas yaji kunyar zargin da yai mata. Ta sake unkurin komawa ta kwanta sai ya rikota ya janyota ta matso kusa da shi ya mika dayan hannunsa ya dauko tea ya kafa mata a baki.
Amaimakon ta sha tea sai ta dago kanta sama ta kalleshi hawaye na mata zuba.

“Zain baka jin komai idan kana zalumtar mutum? Miyasa baka da tausayi?”

“Just drink, ko na dura miki you know me well”

Ya maida kanta bakinta ya saitu da kofin,a hankali yake bata tana kurbawa har ta shanye, sannan ya tashi ya sauka kasa ya dauko ruwa ya dawo ya mika mata tare da maganin.
Ta kalleshi

“Ba zan sha ba, ka kyale ni mana”

“Dan Allah ki sha, bana son rigima da ke a yanzu”

Bata amsa ba duk da ya hada ta da Allah, sai taja mayafin rufar ta lullube ta barshi nan tsaye rike da maganin. Juyawa yai ya fita da maganin dan har ga Allah baya son rigima da ita a yanzu, he know what he did tana da bukatar hutu a yanzu. A dinning ya aje maganin sannan ya fice daga part dinsa ya nufi part din Dada, as usual da safe Dada bata zama falo dan haka ya wuce dakinta direct, baya jin sallamar haka nan ta tura kofar dakin ya shiga, sai ya sameta zaune saman gado Hameeda na kwance saman cinyarta ita da Dada duk fuskokinsu na dauke da hawaye.

“Tun jiya nake ta kiranka baka dauka ba kuma ba ka zo ba”

Dada ta fada tana share hawayenta.

Zauna yai saman kujerar dake dakin sannan ya amsa mata.

“Ina office, kuma muna tiyata ko da kika kirani, na dawo gida late shiyasa ban shigo ba”

“Hameeda ta fada min kana nemanta jiya”

Ya kalli Hameeda ba tare da yace da Dada komai ba.

“Wai kamin ta karasa inda zaku hadu ta hadu da wani mutum a hanya yana taronta ko da ta tsaya sai ya shaka mata wani abu, bata sake sanin inda take ba sai kusan magariba, ta ganta a ciki wani gida dake unguwar shine ta kira Fauziya da Ikram suka je suka taho da ita, motarta ma sai da aka aika direba ya dauko mata”

Gaban Zain ya fadi, jin an ambaci Fauziya da Ikram, hakan na nufin sun ganshi kenan ko kuma wani plan din ne daban. Ganin yayi shiru be ce komai ba ya bawa Dada Yalwa damar cigaba tana kuka.

“Fyade aka mata Zain kuma tace bata san ko wanene ba, ni Wallahi ba dan tace ayi shiru a rufa maganar ba da sai nasa an binciko ko wanene a kasar nan an wulankanta shi”

Hameeda da idanuwanta suka gama kumbura saboda kuka ta dago kanta ta kalli Dada.

“Dan Allah dan girman Allah ku rike min sirrina Dada, daga ke sai Ikram da Fauziya kawai kuka san wannan sai kuma Yarima, idan wannan maganar ta fita martabar masarautar nan zata fadi kuma za a yi ta kallona da abun ne, wata kila ma babu wanda zai aureni”

Ta kara fashewa da kuka kamar yadda Dada ma take kukan. Har yanzu Zain be ce komai ba, he was busy thinking of something. Miyasa tai haka? Miyasa bata fada cewa shi ne ba? Ko dai komai be faru tsakaninsu ba? Shin Ikram da Fauziya sun ganshi Naked ko kuma aa?

“Dada ba ni guri zan yi magana da ita”

Sai a lokacin ta dago ta kalleshi suna hada ido tai sauri dauke nata idon ta daga daga jikin Dada, sai Dada ta tashi ta fice daga dakin tana share hawayenta. Kallonta yai da kyau kamin ya ce wani abu ta riga shi magana.

“Na san abunda zaka tambaye Zain, matsalar Anty Ummi ce kawai a gabanka sai taka, to ba karya Abida ta fada maka ba, ni na shirya komai, iyayen karya kama Anty Ummi da siyar da yarinyar da aka yi ga masarautar Damagaram duk ni ce, na yi hakan ne saboda kai Zain, saboda ka kasa fahimtar komai, and wannan lokacin ba wasa nake ba, idan har ban samu cikar burina ba sai na watsa hotunan a cikin masarautar nan, sai na zubar da kimarka da kimar yayan da zaka haifa nan gaba, kuma kai duniya zata zaga saboda fyade kai min, Fauziya da Ikram zasu shaideni domin sun kararda ni Naked a falonka.... Na kirani mahaukaciya ko kuma duk sunan da kake ganin ya dace da ni, amman kai kaja komai....”

Ta karasa hawaye masu zafi na sauko mata, OMG she exposed it, he just can't believe daga bakinta wadannan kalaman ke fito, ta bashi amsar tambayar da ba ita zai tambayeta ba, amman ita tafi komai muhimmanci a gareshi a yanzu.
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660*

40

Ta dauka Abida ta Fadawa Zain komai shiyasa ta fallasa wannan sirrin har da fadin tasa an siyar da Hafsat a masarautar Damagaram, ta fada masa abunda yake son ji.
Kallonta kawai Zain ke yi zuciyarsa na raya masa bata da hankali, taya zata yi duk wannan sannan kuma ta fito kai tsaye ta fada masa kudirinta.
Shaye-shayen daya taba ganin tana yi ne ya fado masa a rai, hakan na nufin kwakwalta ta juye kenan ko kuma tana shirin juyewa.

“Abida bata fada min komai ba, kuma ba abunda zan tambayeki kika ban amsa ba”

“Ta fada maka komai Zain na sani, me zaka tambaya? Yadda za ayi yarinyar ta dawo? Ko kuma kana son ka tambaya na haukace ko ina cikin hayyacina?
Ba haukacewa nai ba Zain, ina cikin hayyacina to be frank, kayan mayen daka tarar a dakina ba sha nake ba, na yi kamar ina shan ne a tunani zaka tausaya min ka so ni”

Ta kai hannu ta share hawayen idonta, zuciyarta na mata mugun zafi.

“Baki ji kunyar abunda kika yi ba? Me yake damun ki ne Hameeda ke wace irin shu'umar macece? Ke baki san rashi ba, baki san kiyayya ba? Kin dade baki yada wadannan hotunan ba, baki cika yar iskaba tun da baki fito kai tsaye kin fadawa duniya abun ba”

Ya fada a tsawace zuciyarsa na mugun bugawa, yana mai jin kamar ya janyota da karfi ta buga kanta da gini. Murmushi tai irin murmishi nan da yafi kuka ciwo wasu hawayen bakinciki na fito daga idonta.

“Na tambaye ka wani abu Zain? Lokacin daka rasa Haleema ya ka ji? Abunda kake ji a duk lokacin da ka tuna da ita shi nake ji idan na tuna da kai, kasan ba zaka aure ni ba miyasa ka saka na fara son ka tun farko? Ka tsalleke ni ka auri Yayata, ta mutu sai kaje ka dauko wata, na san kiyayya Zain saboda ka nuna min ita a fili, na kuma san rashin saboda na rasa yar uwata Babana, mamata sai kuma kai, bani da wani abu daya rage min a duniyar nan da zan yi alfahari da shi, ka yi min zalumci mafi girma a duniyar nan Zain, ka sana na dasa sonka a inda ba muhallinsa ba, na yi ta masa ban ruwa, a maimakon ya fito yai yado sai sayyunsa suka koma min ciki suna son su haukarta da ni, na bautu Zain na bautu da son ka, amman ladan sakamakona kiyayya ce, mi kake son nai ne Zain? Fada min mi zan yi ka dawo ka so ni kamar da?”

“Ko a da ba son soyayya nake nuna miki ba, son yan'uwanta ne, wai ni kadai ne namiji a duniya ne? Ba akwai wasu mazan masu son ki ba? Ki auresu mana”

Ya fada a tsawace yana zaburo mata. Hannu tasa ta dafe zuciyarta ta hade wani abu mai da ci.

“Kai kadai ne Namiji a duniyar nan Zain, haka Hameeda take gani, idan na kalli idon wani namijin fuskarka nake gani, duk yadda nai kokarin dasa son wani a zuciyata sai na kasa saboda kai kadai nake so, kaji tsoron zuwan wata rana Zain wata rana da Allah zai jarrabeka kamar yadda ya jarrabeni, ba ni na sawa kaina son ka ba, jarrabawata ce ta zo a haka, miyasa ka kasa ganewa? Kaji tsoron addu'ar wanda aka zalumta...”
Chapter 55 · 0% Book details