← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 93

Sashe 74

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Tambaya ta tana da fa'ida ya mai shari'a, dole ne za mu san wani irin zama take tsakaninta da mijinta, Wacece Farhat su waye kawayenta ya hallayarta take, dole ne zamu so mu so mu sani domin musan komai akanta abunda ne da zai taimake mu akan shari'ar nan”

“Korafi be karbu ba, Barr Husaina zaki iya cigaba”

“Na gode ya mai shari'a”

Ta juya gurin Zain.

“Shin auren soyayya kuka yi da ita”

“Auren kiyayya kike tsammanin zamu yi?”

“Tambayace kawai Malam Yarima ka amsa mana”

“Auren soyayya muka yi”

“Ya zamantakewar aurenku yake?”

“Akwai kyakkyawar mu'alama kuma muna kaunar junanmu”

“Shin ko zaka iya fadawa kotu kadan daga cikin halayen Farhat”

“Macece Mai Hakuri da biyayya ga bin umarnin na gaba da ita ko da hakan be mata dadi ba”

“Kotu zata so taji dalilin zaman karamar yarinya kamar Hafsatu manga a gidanka, bayan kuma akwai kyakkyawar alaka a tsakaninka da matarka, shin mai aiki ce ko kuma kanwarka ce”

“Ita ma matata ce ita ma, masarautar Damagaram ta bani ita a matsayin kuyanga, a wani lokaci fa na ziyarce masarautar”

“Akwai kishi da kiyayya a tsakaninsu ko? Kasancewar miji daya suke aure”

“Babu, zaman wuni da kwana ne kawai Hafsat tai a gidan ta ya kishi zai iya shiga tsakaninsu”

“Kishi zai iya shiga zuciyar mace cikin minti daya Zain, wata kila baka bawa Farhat kulawa yadda ya dace shiyasa baka fahimci kishi yana tare da ita ba ko babu, ko da yake ka fada mana tana da hakuri ko? Wata kila shiyasa ta danne zuciyarta ta kasa nuna ko da na minti daya ne a gabansa, shin ko akwai kyakkyawar alaka tsakanin Farhat da Hafsat na dan zaman da tai a gidan na wuni daya da rabi?”

“Akwai”

“Shin a lokacin da ka samu labarin cewar Hafsat ta dabawa Farhat wuka ya kaji”

“Nayi mamaki domin na san fada be taba shiga tsakaninsu ba, kuma Hafsat ko cinnaka ba zata iya kashewa ba balle rai”

“Na gode zaka iya komawa mazauninka”

Ta fada tana murmushi. Sai ta nufi gurin da teburinta yake ta bude jakarta ta dauko wata farar leda mai wuka a ciki ta daga ta sama.

“Ya mai shari'a wannan ita ce wukar da da Hafsat ta dabawa Margayiya Farhat ta kasheta, an samu sawon hannun Hafsat a jikin wukar, a bayanin da Abida ta bayar ta nuna cewa Hafsat ta kashe ta ne a lokacin da suke su kadai a cikin falon kuma tai kokarin guduwa, kyakkyawar fahimta dake tsakaninsu zai iya zama a gaban idon Zain ne kawai a bayan idonsa kuma wata kila suna samun rashin fahimtar juna, ba abun mamaki ba ne dan karamar yarinya kamar Hafsat ta dabawa babbar mace kamar Farhat wuka ba, domin ba sabon abu ne ba, kuma zai iyayuwa daman can Hafsat bata shigo gidan da kyakkyawar niya ba, domin a bincike da nai ya nuna cewar Hafsat tashi kauye ce kuma yarinya ce wacce ta tashi cikin maza da mata da basu san darajar kansu ba, hasalima har yanzu ba a san waye mahaifiyar Hafsat ba, a duk zaman da tai a kauye ta zauna ne a hannun wata mace wacce take baiwai ga sarkim kufawa, Hafsat zata iya kashe Farhat idan har tana ganin ta takura mata, ta hanyar fada da zata mata ko kuma ta sakata wani aikin da wannan nake rokon kotu mai adalci data yankewa Hafsat hukuncin abunda ta aikata, domin ya zama darasi a gareta, kuma izna ga yan baya na gode”

Ya mikawa muhti wukar muhti ya mikawa alkali, sannan ta koma ta zauna. Bayan Alkali ya karbi wukar ya duba ya yi rubutu ya dago ya kalli Barrister Hassana ya ce

“Ko Lauya mai kare wacce ake kara tana da wani abu da zata fada”

“Ina da shi ya mai shari'a”

Ta fita daga inda take ta nufi gurin da Hafsat ta ke.

“Ki kwantar da hankali wannan kotu ce mai adalci, ina son ki bude baki ki amsawa kotu wannan tambayar, shi ke kika kashe Farhat?”

Sai kasa dago kai ta kalli Hassana balle har ta ce wani abu.

“Ya mai girma Mai shari'a, wannan kukan da Hafsat take yi kadai ya isa ya karantar da duk wani mai hankali cewar ba ita tai kisan kan nan ba, a tunani na mai hankali da hangen nesa zai yi mamaki ace Hafsat yar shekara tara zuwa goma ta dauki wuka da hannunta ta dabawa babbar mace kamar Farhat mai shekara ashiri da shida a duniya, a iya binciken da nai ya nuna cewar wani tsabani ko rashin jutuwa be taba shiga takanin Farhat da Hafsat ba, a bayanin da Zain ya bayar a gaban kotu ya fada ma kotu cewar zaman da Hafsat tai a gidan na wuni daya da rabi ne, shin taya wani rashin jituwa zai iya shiga tsakanin Farhat da Hafsat da har zai kai ga yin kisa? Barrister Husaina bata fadi karya ba, gaskiya ne Hafsat bata tashi gaban iyayenta ba, amman kuma bata tashi gurin mutane masu gurbatacciyar tarbiya ba, a kaddara ma ta tashi a cikinsu a karancin shekarunta anya za ta iya daukar wuka ta tabawa wani kamar Farhat wacce ta taba ganin ganin wuni daya da rabi kawai?”

“Objection my lord, Barrister Hassana tana kokarin wasa da hankalin kotu ne kawai, domin ga zahiri ya nuna an ga sawun hannunta a jikin wukar”

“Ganin tambarin yatsun be isa ya bada shaidar cewar ita ta kashe Farhat ba, ta wuni a gidan na tsawon kwana daya da rana ba abun mamaki ba ne dan an ga tambarin yatsunta a jikin wukar ba”

“Korafi be karbu ba, za ki iya cigaba”

“Na gode ya mai shari'a, ina bukatar kotu ta kora Abida Zakari domin amsa mana wasu tambayoyin”

“Kotu na bukatar ganin Abida Zakaria gabanta”

A karo na biyu Abida ta taso ta sake dawowa gurin data tsaya dazun ta sake tsayawa.

“Shim ko zaki fadawa kotu abunda ya kai ki part din Zain?”

“Gimbiya Hameeda ce ta kirani a waya tace Farhat tana son gani naje yanzu yanzun nan”

“Da kika je a wane hali kika samu Hafsat da Farhat?”

Ta sake maimaita abunda ta fada dazun, sai Barrister Hassana ta ce

“Shin kin ga wukar ne a hannun Hafsat?”

“Aa wukar tana jikin Farhat ne ita kuma Hafsat ta zo jikin kofa tana kokarin guduwa”

“Shi kadai kike gani?”

“Ee”

“Shin daman idan Farhat zata kiraki tana kiran Hameeda ne ta ce ta fada miki”

“Aa hasali ma bata taba kirana ba”

“Shin miyasa ta kiraki a wannan karon?”

“Nima ban sani ba”

“Na gama ya mai shari'a”

“Zaki iya zuwa ki zauna”

Mai shari'a ya fada. Bayan ta koma ta zauna. Barrister Hassana ta nufi gurin zamanta ta dauko abu a lada gorar rubutu ne a ciki da kulli magani.

“Ya Mai girma Mai Shari'a, an samu wannan ne a kusa da gawar Farhat, rubutu ne da kullin magani shi taya rubutun ya shiga gidan? Waya kawo shi? Shin Hafsat tayi girman da zata iya bibiyar malamai har ta shigo da rubutu a gidan? Wani abun mamaki har yanzu babu wanda ya san inda wayar Farhat take, bata gurin mijinta haka zalika bata wani guri a cikin gidan, kuma mijinta ya tabbatar min da cewar ya siya mata waya to amman ina wayar take?”

“Objection my lord, zai iya yiyuwa Hafsat ta dauke wayar ne ta boye wani gurin”

Hasaana ta juyo ta kalleta.

“Haba Barrister Husaina, karki yaudari kanki mana, taya karamar yarinya kamar Hafsat zata shigo cikin gidan da rubutu da soketa da wuka kuma ta dauke wayarta? Shekara tara kadai ba goma sha takwas ba”

“Korafi be karbu ba, Barrister Hassana zaki iya cigana”

“Na gode ya mai shari'a, Ina rokon kotu data kira min Zain a gabanta domin ya amsa mana wasu tambayoyin”

“Kotu na bukatar ganin Zain a gabanta”

Ba bata lokaci Zain ya taso ta zo ya tsaya.

“Ka fadawa kotu cewar matarka mai hakuri ce, kenan bata taba samun sabani da kowa ba?”

“Bata taba fada da kowa ba, sai dai akwai takum saka a tsakaninta da wata yar'uwata Hameeda”

“Takun saka kamar yaya? Basa jituwa ne suna yawan fada ne?”

“Akwai dai rashin jituwa a tsakaninsu”

“Miya kawa rashin jutuwar a tsakaninsu”

“Saboda Kakata Hameeda take son na aura, saboda Hameeda tana so na, ni kuma Farhat na ke so, wani lokacin ta kan shigo sashen har su samu rashin jituwa”

“Kenan akwai kiyayya mai tsanani tsakaninsu? Haka ne?”

“Haka ne”

“Na gode, iya kacin tambayoyina kenan a gareshi ya mai shari'a”

“Zain zai iya komawa ya zauna”

Alkalin ya fada. Sai Barrister Hassana ta sake requesting. Cewar alkali ya kira mata Ibrahim domin amsa mata tambayoyi.

“Ibrahim kotuna na bukatar ka gabatar mata da kanta”

“Sunana Ibrahim Abdullahi kwararren likitan ina aiki da Zainuddeen Special Hospital”

“Mashallah, shi kai ne wanda ya tarbi Farhat kuma ya cire mata wukar da ke jikinta ko?”

“Ee ni ne”

“Shin ya ka samu gawar Farhat?”

“Ko da aka iso da ita tana da sauran numfashi, sai dai kamin mu gama mata aikin rai yai halinsa”

“Shin ya ka samu sukar da wukar tai mata?”

“An daba mata ita ne daga saman cikinta sai kuma tai kasa, hakan yasa har wasu daga cikin hanjinta suka fashe, mun yi iya kokarin mu na ceton ranta amman Allah be nufa ba”

“Shin karamin yarinya kamar Hafsat zata iya daba ma Farhat wukar har tai mata rauni haka?”

“Zata iya idan tsawonta ya kai mita talatin zuwa talatin da bakwai”

“Idan kuma be kai ba fa?”

“Ba zata iya taba mata wuka kamar hakan ba, domin alamu sun nuna duk wanda ya taba mata wuka to ya saba ne ko kuma ya gwari ne akan abu”

“Kai ne kai gwajin wukar da aka daba mata ko? Har ka samu safurin Hannun Hafsat”

“Ee amman ba safurin hannunta kawai na samu ba, na samu samfarin hannun wasu mutanen biyu, sai dai na Hafsat ne ya fito saboda mun dauki tambarin yatsunta”

“Kenan akwai tambarin yatsun wasu bayan nata”

“Ee akwai”

Barrister Hassana ta kalli Alkali ta ce.
Chapter 74 · 0% Book details