← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 93

Sashe 79

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawa yai gurim mutane da suka zo da ita a nan suka tsaya suna masa bayanin inda suka sameta a kauyen kalgo, sun kira numbar da aka bayar basu samu ba, sai ta Mai maigadinsa shi ya fada musu inda gidan yake har suka iso, sai kuma sukai rashin sa'a baya gari, daya daga cikinsu dan sanda nw wanda ya rakosu tun daga garin kalgo har zuwa Kaduna, anan suka bashi labarin sun sha wahala kamin su zo da ita, dan ihu take musu har suka iso, Allah yasa ma motar gidace dan motar dayansu ce wanda ya kasance direbane mai zuwa gari gari. Tarba mai kyau Alhaji Habib yai musu ya aiki daya daga cikin masu aikin gidansa suka sawo musu abinci mai kyau a hotel. Ita kuma aka nufi main house da ita, amman a part dinsa, Hafsat manga na rike da hannunta, tana taka kafarta a kofar falonsa da zimmar shiga sai ta rafke ta fadi a gurin jikinta sai karkarwa yake kamar mai jin sanye idanuwanta kuma na rufewa tana dantsar baki. Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, shi Alhaji Habib ke ta furtawa shi da Sulaiman da kuma Jabiru (Direbansa) Hafsatu manga kuma ta shiga girgiza ta tana kuka. Sai a lokacin yan'uwanta suka fado masa sam ya manta ma da wayarsa dayar a kashe take sai yanzu, da sauri ya nufi motar da suka shigo ya dauki wayar ya kunna ya kirasu ya sanar musu. Ko minti goma aha biyar ba a yi ba sai gasu sun iso ciki har da mahaifiyarta. Kowannensu kuka yake ganin irin halin da take ciki, kanwarta ta dauke Hafsatu manga dake kuka ta rumgume kamar ta cinyeta. Alhaji Habib da hankalinsa ke a tashe ya ce

“Ina ganin kamar akai ta asibiti kawai zai fi”

“Aa ai ba ciwon asibiti bane, ko an kaita wani abun daban zasu mata, kara ma ai mata rubutu kuma ayi mata addu'a, wata kila abun ne yake kokarin karewa”

Cewar Hajiya Shafa wato gwaggonta.

“Nima dai haka na gani Allah ya saka miki Rufaida”

Cewar Mahaifiyarta, sai Hajiya Shafa ta ce

“Ku kaita ciki, ni zan koma nasa a rubuta mata bismillah dubu na kawo mata, ko minene zai bar jikinta kuma zata samu lafiya da yardar Allah”

Tana gama fadar hakan ta nufi kofar fita a lokacin ana kiran sallah isha'i, Bata dawo gidan ba sai goma da rabi na dare, har lokacin suna zaune tare da ita suna ta mata fifita, Hafsatu manga kuma na jikin Farida tana bachi, sai faman sauke ajiyar zuciya take, Daker suka dago kanta suka dora mata rubutun sauran suka shafa mata a kai da fuska, a take ta fara kwana kamar wacce ta shekara goma ba tai bachi ba, har yadda take jan numfashin tana saukewa ana ji.

*** *** ***

Kamar kullum yau ma ta samu mahaifiyarta babu wani sauki, ciwon kan da take tana nan da shi, ga wani abu da take da ido da kuma baki kamar mai magana da wani, Hawayen da Hassana ta zubar yau yafi ko wane hawaye da ta saba zubarwa domin a yau ta fi kowa tausayin halin da mhaifiyarta take ciki, bata bukatar a sake tunatar da ita, amman tasan karshen maihaifiyarta ya zo tunda Hafsatu manga ta tako gidan, abinda bata sani ba har Rufaida ma tana can gidan ba Hafsatu manga kadai ba. Misalin tara da tabi Hussaina ta shigo dakin tare da mijinta da kuma yarinyar ta daya. A lokacin Hassana na zaune saman gadon da Hajiya Safiya take kwance.

“Me kike a nan?”

Dagowa Hassana tai ta kalleta tana hawaye sai ta kasa ce mata komai.

“Naga ai burinki ya cika ai ko? Za ayi zama na karshe zaman da za a wanke Hafsat a yankewa Hameeda hukuncin kisa, kin yi winning na yi losing, ba shikenan ba? Ina ganin be kamata ki zauna a nan ki tsareta har sai kin ga mutuwarta ko haukanta ba, da ace Mama tana cikin koshi lafiya a yanzu da zata fada miki a duniyar bata da makiyi irinki, kuma sai ta fi kowa tsanarki”

“Husaina kin kasa fahimta”

Ta fada cikin kuka.

“In fahimta? In fahimce cewar Kina son wata bare fiye da mahaifiyarki, ko kuma kina son kashe mahaifiyarki da hannunki, wace uwace kamar tawa zata raini ya kamar ke ta bata tarbiya da kulawa amman ta girma ta tsaya defending wata a kotu saboda ita tai nasara mahaifiyar kuma ta kwanta ciwo? ”

“Babu, hakika babu yar da ta kai kamar ni wacce ke son Mahaifiyarta ta samu rahamar Allah da gafararsa, Hussaina kin san irin azabar da aka tanadawar mace da ta mutu mijinta na fushi da ita? Duniya tana mata mummunar shaida? Kuma ta cutarta kishiryarta da yar kishiryar saboda wani bukatu nata ka kanta? Kin san Zafin wutar Allah da azabarsa anya kin yadda Allah baya yafe laifin wani kan wani? Abunda ya faru da Mama darasi ne a garemu da kowa, idan amman Allah be kamata duniya ba zai kamata ranar da babu mai iya daga ido ya kalleta balle har ya nema mata yafiya, ita kadai ta san halim da take ciki a yanzu, ita kadai ta san abunda take ji saboda abunda ta aikata, da ace tana cikin hankalinta a yanzu, da yafiyar Rufaida da Hafsat zata nema, kuma Allah ba zai yafe mata ba har sai idan su suka yafe mata”

Hussaina ta durgushe a gurin ta fashe da kuka.

“Bana son wani abu ya samu Mama, bana son ta tafi ta barmu, miyasa kika aikata Mama? Wayyo Allah Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, na shiga uku ni Husaina ban jidadin ganin wannan bakar ranar ba... ”

Kuka take sosai tana fadin haka, mijinta na yarta na lallasarta, Hassana ma kuka take daga can inda take zaune.

*** *** ***

*Washe gari...*

A hankali take takowa hannayenta sanye da handcuffs, jikinta kuma sanye da kayan tufafin an gidan yari, fuskarta ba yabo ba fallasa, sai dai kana ganin idonta kasan ta sha kuka. Yar gandireba na bayan har suka iso harabar da ake ganawa da mutane, hango Anty Ummi da Zain yasa ta tsaya kamar ba zata zo ba, sai kuma ta tako a hankali ta karaso kusa da su, sai yar gandireban ta saka makulli ta bude mata handcuff din.

“Minti goma sha biyar”

Ta fada mata sannan ta juya ta koma can ciki inda ta fito. Tsaye tai tana kallon daidaikun mutane dake gurin dan bata son sauke idonta gurin Anty Ummi ko Zain, ganin hakan yasa Anty Ummi ta ce

“Zauna Hameeda”

“Na zauna kiji dadin kallona ko? Na san kin zo ne ki fada min kinji dadin abunda ya faru”

Anty Ummi tayi murmushi irin murmushin da ke bayyana damuwar da ke cikin ranta.

“Kin rasa abubuwa da yawa Hameeda, Mahaifinki, mahaifiyarki, yayarki, da kuma Zain, me zai sa nai farinciki da abunda ya sameki? Kin yi abunda ya dace da kika fadi gaskiya amman tun jiya kukan kama ki na kai, tsakanin ke da Farhat ban san waya fi wani rashin dacen rayuwa ba, ita ma ta tashi kamar ke, ba uba, sai uwa kawai, ta zauna a hannun yyarta irin zaman da bata jidadinsa ba, ta auri Zain ta hadu da kalubale daga gareki, har kika kasheta, tsakanin ke da ita sai na rasa wa zan tausayawa”

Hameeda ta fashe da kuka tana jin rashin kyautawa a abunda ta aikata, zaunawa tai yana fadin.

“Na san Dada da Mai Martaba ba za su taba yafe min ba”

“Har yanzu Dada bata san abunda ya faru ba, shiyasa na zo nan zan baki ku gaisa, na fada mata cewar kin tafi Kaduna gurin Yayan Mahifiyarki har zuwa lokacin da za a gama shari'ar, ga wayar ki nan dazun na karbeta gurin Ikram dan makullin dakinki yana hannunta”

Zain ya mika mata wayar, sai ta karba ta kunna ta cire password ta kira numbar Dada, ringing biyu ta dauka.

“Assalamu Alaikum Hameeda”

“Na'am Dada kina lafiya?”

“Lafiya kalau, Zain ya fada min wai kin tafi kaduna gurin Alhaji Aminu har a gama case din da gaske ne”

“Ee Dada ki kwantar da hankalinki ina nan lafiya kalau sai idan an gama case din zan dawo”

“Na yi ta kiran wayarki ban samu ba”

“Ee inda na ke ba network kowa sai yace min yana kirana bata shiga,amman ni idan na kira ina samu ai”

“Amman dai zaki zo ki ganni ko?”

Ta kalli Zain sai ya gyada mata kai alamar ee.

“Ee zan zo idan an kwana biyu, Dada ina son ki sosai, ina kewarki ki kula da kanki dan Allah”

“Inshallah nima na yi kewarki Hameeda, dama kin yi zaman ki a nan zan fi jidadi”

Dada ta fada cikin kukan. Sai Hameeda ma ta amsa cikin kukan.

“Na fi son nan Dada, sai anjima”

Tana sauke wayar Zain ya mika mata hannu ta bashi wayar, sai ya kashe ya mike tsaye, itama ta mike tsaye tana kiran sunansa.

“Zain I'm pregnant, ina son na fada maka tuntuni amman ban samu dama ba, ina ganin ya kamata na fada maka a yanzu...”

Ta fada kai tsaye, ba shiri ya juyo ya kalleta, Anty Ummi ma ta mike tsaye tana kallon Zain...

*** *** ***

Tun da aka dora mata rubutun ta sha take ta aikin bachi har garin Allah ya waye, bata farka ba ko matsawa ba tai ba daga inda take, sai guraren karfe goma sha daya na safe sannan ta fara motsawa a lokacin har sun fara yanke shawarar kai ta asibiti dan sun fara tsorata, daman Hajiya Shafa ce take tausarsu itama izuwa yanzu ta fara tsorata da lamarin. Babu kalar addu'ar da ba a mata ba, har mai ruqya an kira da safen nan yai mata amman shiru.

Kafafunta ta fara motsawa sannan ta tashi zaune dafe da kai tana ta maimaita.

“Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un”

Kan take ji kamar zai fashe mata, tana jin hayaniyar da suke kamar a mafarki, dan can kasa kasa take jin muryaoyinsu, daker ta bude idonta shima saboda kiran sunanta da Alhaji Habib ke ta yi ne dan ya karara ta bude idonta he just can't believe ita ce din.
Tana budewa sai ta ga komai na juya mata tai saurin maidawa ta rufe.
Chapter 79 · 0% Book details