← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 93

Sashe 15

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Idan kai zaka iya cin amanarta ni ba zan iya cin amanar yar'uwata ba, Anty Rukaiya ta yi min komai a rayuwa be kamata na yi mata haka ba...”

Kamin ta karasa ya shiga kokuwar cire mata Hijab.

“Kin ga ina miki da lalama shiyasa kike min wannan abun ko? Ko dan kin ce naji bana son miki da karfi sai kin amince ne kike min wannan iskanci....”

Wasa wasa wanki hula ya kusa kaisu rana, kokari yake yaga ya kai ga jikinta ita kuma ta kasa masa ihu saboda kar mai gadi yaji, tasan ba rufin asirinta bane da kuma na Anty Rukaiya, wani bangare na zuciyarta kuma yana son sakata ta amince.

Jin hakan yasa Anty Rukaiya saurin bude kofar bathroom din ta fito fuskarta da hawaye shabe shabe kamar yadda ta Farhat take, zuciyarta kuma cike da kunci.
Daga Ya Bashir har Farhat mutuwar tsaye suka yi dan basu san tana ciki ba, ba ma kamar Bashir da gumi ya soma keto masa duk da sanyin ac dake dakin. Jinginawa tai da gurin ta sulale kasa ta zauna tana kallon mijinta ido cikin ido.
Jikinsa rawa yake har cikin antarsa ya kasa furta komai agareta kuma ya kasa dauke idonsa daga garin kallonta, kamar an tsikareta sai ta tashi da sauri ta bar jakarta a gurin ta nufi kofar fita ta bude da keys din dake makale jikin kofar ta fita, saurin fitowa yai shima he was just thinking of zata zuba musu wani abun ne ko kuma ta dauko wuka ta daba masa ko ta kullesu a dakin. Sai kawai yaga ta nufi kofar fita ta fice, a nan tunaninsa ya fara sauyawa zuciyarsa na raya masa ko zata tara musu mutane ne.
Da sauri ya dauki keys dinsa dake kan freezer ya fita, motarsa ya shiga mai gadi ya bude masa ya fita amman ko kurar Rukaiya be gani ba, hakan yasa shi nufar cikin garin dan baya son kara ganinta yanzu.

Tana fita tai sa'ar samun Napep sai kawai ta shige tace ya kaita Jibril Bala (JB) Secretaria gurin da take aiki, har suka isa hawaye ke mata zuba, sai da ta isa sai ta rasa kudin baya mai napep din sai da ta karba hannun daya daga cikin securities din da suke gadin gate din sannan ta taka da kafa ta karasa part din da office dinta yake.
Duk yadda tai kokarin boye hawayenta sai haka ya gagara har ta isa office dinta hawaye zuba suke mata, kowa sai mamaki yake masu tambayar tafiya sun fi wadanda suka yi shiru yawa.
Office dinta ta shiga ta zauna dip kamar an jefota, kawarta ce Samira ce ta shigo office din da sauri tana kallon yanayinta da kuma fuskarta.

“Na san yau kin gani ko kinji abunda yafi karfin idanuwanki, amman ya kamata kiyi controlling kanki saboda kar kowa ya san sirrinki, keep yourself clam, and clean your tears do not let anyone know your secret, wannan sirrinki ne ke kadai, please stop crying”

Ta karasa tana sa hannu ta share mata hawayenta. Anty Rukaiya ta dago kai ta kalleta.

“I can't work right now, i don't know what to do”

“Ki koma gida yanzu idan kuma ba zaki iya zama gidanki ba kije gidana, lemme handle the documents, just go and rest”

Ta saka hannu ta kwashe duka takadardun da suke gabanta, ita kuma ta mike tsaye tana jin zuciyarta ta mata mugun nauyi har bata iya numfashi, saurin rike kujearsa tai saboda kokarin faduwa da take.

“Samira i can't breathe”

Ta fada tana wani irin shidewa.

“Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un”

Samira tayi saurin sakin documents din ta riketa da sauri.

“Ina inhaler ki?”

Bata iya amsawa balle har ta fada mata ta baro jakarta gida.

“Please help us...”

Samira ta fada tana fashewa da kuka saboda mawuyacin halin data ga kawarta tana ciki...

_________________________________

What do you expect next?

Anya Zain iya kyale Hafsat kamar yadda Anty Ummi ta bukata?

Da gaske Hafsatu manga yar gudun Hijira ce ko kuma turota aka yi?

Me zai faru da Anty Rukaiya?

Ya Farhat zata kasance?

One word for Ya Bashir

One word for Anty Ummi.

One word for Hameeda.

What will happen next?

#Share
#Comment
#Vote

*HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

1⃣3⃣

Tun da Anty Rukaiya da Ya Bashir suka fice Farhat take wani irin kuka, kukan data rasa dalilinsa, farincikin Anty Rukaiya taga gaskiya ko kuma bakinciki data kasance ita silar kuncin da zai tabbata a ran Anty Rukaiya? Da gumi da majina duka ta hada a gurin da take zaune, gashi bata da karfi ko na kwayar zarra, tana son ta tashi amman data unkura sai ta kasa, tun daga nan ta tabbatar da raunin daga zuciyarta yake, hakan yasa ta kara fashewa da kuka.
Hankalinta ya tashi sosai lokacin da taji tsayarwa mota a harabar gidan, da fari tayi tunanin ko Anty Rukaiya ce ko kuma Ya Bashir, amman yanayin shigowa falon da kuma muryar da taji ya tabbatar mata da ba daya daga cikinsu ba ne. Iya kokarin da take na ta tashi ta fita daga dakin ne amman sai ta kasa, har Samira ta shigo dakin hankalinta tashe hawaye shabe shabe a fuskarta.

“Farhat Farhat kira mana Bashir kirashi yanzu ki ce Rukaiya tana asibiti.... ”

Kamar an sako mata karfi haka taji, sai ta zabura ta tashi tsaye jikinta da zuciyarta na mugun rawa kamar yadda bakinta yake karkarwa kamar mai jin sanyi.

“Me.... Me.... Me.... ”

Sai ta kasa tambaya. Samira ta matso kusa da ita ta rika hannunta.

“Kin san inda Bashir yake yanxu? Kina da number sa?”

Kai kawai ta iya daga mata, sai Samira ta mika mata wayarta, Farhat ta karba ta saka mata number, cikin sauri Samira ta karba ta danna kira, cikin kankanen lokaci aka dauka.

“Hello Bashir Samira ce kawar Rukaiya kazo asibitin Yarima yanzu nan muka kai Rukaiya asmanta ya tashi..”

“Sorry kin yi wrong number wannan Auwal ne”

Cikin sauri Samira ta katse kiran jin abunda mai number yace mata, sai ta girgiza kafadar Farhat.

“Ke number Bashir zaki bani ta Bashir”

Sai da ta girgiza kusan sau uku sannan ta sake kai hannu ta karbi wayar ta saka mata number Bashir kasancewar tana da number shi a kanta. Bugu daya ya dauka sai Samira tai masa bayani sannan ta kama hannunta suka fice daga dakin, gurin shiga motar ma Samira ce ta sakata sannan ta zagaya ta shiga maxaunin direba ta tashi motar suka dauki hanyar asibitin Yariman Bakura dake Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Har suka isa Farhat bata fahimci inda suka dosa ba, ita dai kallon motoci da titin kawai take, bayan Samira tayi parking ta zagayo ta budewa Farhat ta fito da ita, bata iya banbance inda take balle har ta fahimci hanyar da Samira take bi tare da ita.
Ko da suka isa Ya Bashir har ya isa gurin, Samira ce ta gane shi domin hankalin Farhat gaba daya baya jikinta balle ta iya gane shi din ne, sam bata iya gane fuskar mutane ma, ita dai taga mutum tsaye namiji ne mace ne wannan kam sai mai natsuwa ne zai banbance.

Likitocin uku ne tsaye kan Anty Rukaiya maza biyu mace daya, dukansu kwararune kuma manyan likitoci, kokarinsu na neman numfashinta ne, gata a raye amman ta kasa breath hawaye sai zuba yake a idonta, duk wani taimako daya kamata likitocin su bata suna kanyi amman numfashinta ya tsaya cak! Likitan mace ta kalli kwayar idonta, bakin ya bace bat sai farin shima kuma kamar ba daidai take kallo da shi ba, jikinta ya yi mugun sanyi sai wani gurnanin majina take dake cikin kirjinta irin kakarin nan na mutuwa. Ciwo take ji sosai a kirjinta, kowa bawa yana son duniya da burinta yake barinta, sosai Anty Rukaiya take jin kamar ta fisgo wani daga cikin likitocin su taimaka mata ta tsaya, a yau zata tafi ta bar Yayanta da mahaifiyarta, a yau zata bar duniyarta da mijinta, a yau zata yi bankwana da abokai da yan'uwanta, a yau ta sha ruwanta na karshe ta ci abincin karshe, duk wani abun data mallaka a duniya a yau ba nata ba ne, sai wanda ta aje ma kanta na gobe kiyama, a yau zata dandani dacin mutuwa, kamar yadda ko wane bawa yake dandantarsa a duk lokacin da mutuwarsa ta gabata, a yau zata kwana cikin kabarinta, ta tafi gidanta na gaskiya kenan babu zance dawowa, katifa da gadonta da motarta ta gidanta da duk wani abu data mallaka a yau ba nata bane, ji take kamar a kara mata wani lokacin, tana jin inama za a bata damar fadin ko da kalma daya ce amman ba dama, tana kallo duniya zata barta, a yau ko ta shirya ko bata shirya ba dole ne ta sauka a masaukinta na gaskiya, domin ta cinma wa'adinta.

Wani irin kakari take na fitar rai, irin kakarin nan da bashi da jin balle kallo, irin kakarin nan da idanuwanka suka soma bankwana da duniya, goshinta ya cika da zuba fatar jikinta ta canja sai sheki take tayi fari sosai saman da farin da take da shi, tayi tsawo. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke na fitar rai, sai idanuwanta suka kafe. Cikin sauri likitan ya kai hannunsa ya taba sauran ma suka shiga dubata amman ina mai kira yayi kira, mai rai ya karbi abunsa.
Hannu likitan yasa ya shafe mata idonta, sannan suka warware zanen dake saman gadon suka rufe jikinta da shi.
Chapter 15 · 0% Book details